FA’IDODI 12 NA GANYEN LEMUN TSAMI DA YADDA AKE AMFANI DA SU:
Ganyen lemun tsami sau da yawa ana barinsu a gefe saboda ‘ya’yan lemun kawai akafi amfani dasu amma suna dauke da muhimman fa’idodi da yawa wadanda za a iya amfani da su a girki, ko kuma fannin lafiya da kuma kula da gida.
1. Cike suke da Antioxidants
Fa’ida: Ganyen lemu na dauke da antioxidants masu yaki da free radicals da rage gajiya ta jiki (oxidative stress). Wannan na taimakawa wajen kare sel daga lalacewa da kuma hana cututtuka masu tsanani.
Yadda Ake Amfani da Su: a Dafa ganyen lemu a cikin ruwan zafi don yin shayi. Shan wannan shayin yana taimakawa lafiyar jiki gaba ɗaya.
2. Kadarorin Rage Harzuka (Anti-inflammatory)
Fa’ida: Ganyen lemu na da ikon rage kumburi a jiki, wanda zai iya saukaka alamomin cutar sankarau (arthritis) da wasu cututtukan kumburi.
Yadda Ake Amfani da Su: A rika shan shayin ganyen lemu akai-akai. Ka Kara zuma yana inganta dandano da amfanin lafiya.
3. Kwantar da Hankali da Rage Damuwa
Fa’ida: Kamshin ganyen lemu na kwantar da hankali da rage tashin hankali. Ana amfani da su sosai a aromatherapy.
Yadda Ake Amfani da Su: Saka ganye a cikin ruwan wanka mai dumi ko sanya su a jaka (sachet) a gefen gadon ka. Kamshinsu yana taimakawa samun natsuwa da barci mai kyau.
4. Taimakawa narkewar Abinci (Digestion)
Fa’ida: Ganyen lemu suna rage kumburin ciki da ciwon ciki, suna kuma taimakawa narkewar abinci.
Yadda Ake Amfani da Su:Kasha shayin ganyen lemu bayan cin abinci domin sauƙaƙa narkewar abinci.
5. Taimakawa Lafiyar Hanyar Numfashi
Fa’ida: Ganyen lemu na da sinadarai masu taimakawa wajen fitar da datti daga hanyar numfashi, suna amfani sosai wajen mura, tari, da matsalolin numfashi.
Yadda Ake Amfani da Su: Daura ganyen lemun a ruwan zafi, sannan ka shaka tururin ko kasha shayin domin saukaka tari da jin zafi a makogwaro.
6. Kara Karfin Garkuwar Jiki
Fa’ida: Ganyen lemu na dauke da vitamin C da sauran sinadarai da ke karfafa garkuwar jiki wajen yaki da cututtuka.
Yadda Ake Amfani da Su: A sha shayin ganyen lemu ko a kara su a miya da soups domin samun fa’idarsu.
7. Rage Ciwo
Fa’ida: Ganyen lemu na dauke da sinadarai masu rage radadi (pain relief) kamar ciwon kai da ciwon jiki.
Yadda Ake Amfani da Su: Daura ganyen a ruwan zafi, sannan ka bari su huce kadan, sannan a daura a inda ke ciwo domin samun sauki.
8. Inganta Lafiyar Fata
Fa’ida: Ganyen lemu na dauke da antioxidants da sinadarai masu kashe kwayoyin cuta, suna taimakawa wajen hana kuraje da kamuwa da cututtuka a fata.
Yadda Ake Amfani da Su: Shafa ruwan shayin ganyen lemu da ya huce a fata da auduga. Hakanan, za a iya amfani da shi a matsayin ruwan wanke fuska.
9. Kara Dandano A Abinci
Fa’ida: Ganyen lemu suna da kamshi da dandano mai sanyi wanda ke kara armashi ga girke-girke, musamman a girkin Mediterranean da Asiya.
Yadda Ake Amfani da Su: Sanya ganyen lemu a cikin nama da ake soya ko gasawa, miya, da soups. A cire su kafin a ci abinci.
10. Na’urar sanyaya daki (Natural Air Freshener)
Fa’ida: Kamshin ganyen lemu na fitar da kamshi mai kyau wanda ke sabunta iska a gida ba tare da sinadarai ba.
Yadda Ake Amfani da Su: Tafasa su a tukunya domin su fitar da kamshi ko a saka ganyen da aka busar a jaka a dora a cikin gida.
11. Rage Damuwa da Inganta Hankali
Fa’ida: Kamshin ganyen lemu na rage damuwa da kara fahimta da nutsuwa a kwakwalwa.
Yadda Ake Amfani da Su: A saka ganye kusa da wurin aiki ko a hada da potpourri. Ana iya shaƙar tururinsu domin samun nutsuwa
12. Maganin kwari(Insect Repellent)
Fa’ida: Ganyen lemu suna korar kwari kamar sauro ba tare da amfani da sinadarai ba.
Yadda Ake Amfani da Su: Shafa ganyen da suka bushe ko kuma danye a fata. Ko dafa su a ruwan zafi, a fesa ruwan da ya huce a wuraren da ake buƙata a gida.
Karin Shawarwari:
Shayin Ganyen Lemu: Ana iya shansa da dumi ko da sanyi; yana taimakawa wajen kwantar da hankali, narkewar abinci da garkuwar jiki.
Man Ganyen Lemu (Essential Oil): Wasu na fitar da mai daga ganyen don amfani da shi a diffuser ko kayan shafa.
Kawata Abinci: Ana amfani da ganyen lemu wajen kawata abinci da teburi.
Hanyoyin Kare Kai (Precautions):
Ku Guji Yawan Amfani dashi always : Kada a sha ko aci da yawa saboda wasu sinadarai na iya zama masu karfi a jiki.
Tantance Rashin Lafiya: Idan kana da rashin lafiyan citrus,to ka fara da kadan domin ganin ko kana da matsala.
Wanke ganyen lemun Da kyau: Kafin kayi amfani dasu , ka tabbatar da ka wanke su sosai musamman idan an shuka su da magungunan feshi.
Ganyen lemu suna da amfani da dama a girki, da kuma lafiya da gyaran gida. Tare da kamshi mai kyau, da dandano na musamman da fa’idodin lafiya, suna da matukar amfani ga duk wanda ke neman lafiyar halitta.
Daga naku @sadeeqone
0 Comments