🌸 GYARAN FUSKA & LAUSHIN FATA (By: Sirrin Rike Miji) 🌸



🌸 GYARAN FUSKA & LAUSHIN FATA (By: Sirrin Rike Miji) 🌸

Domin samun fata mai laushi, sumul, da haske kamar kwai.


✅ 1. MAGANIN KURAJE DA LAUSHIN FUSKA

Abubuwan hadawa:

🥚 Bawon lemon tsami

🥚 Bawon kwai

💧 Ruwa


Yadda ake hadawa:
Ki shanya bawon lemon tsami da na kwai su bushe, ki daka su sosai har su yi laushi. Ki kwaba da ruwa kadan, sannan ki shafa a fuskarki kafin wanka.


✅ 2. GYARAN FUSKA DA TUMATIR

Abubuwan hadawa:

🍅 Tumatir

🥛 Madara


Yadda ake amfani:
Ki markada tumatir, ki zuba madara, ki kwaba. Ki shafa a fuska, ki bar shi na minti 30, sannan ki wanke da ruwan dumi.


✅ 3. GYARAN FUSKA DA GARIN ALKAMA

Abubuwan hadawa:

🌾 Garin alkama

🍯 Zuma

🥛 Madara


Yadda ake amfani:
Ki hada su wuri guda, ki shafa a fuska kafin ki shiga wanka. Zai sa fata ta yi laushi sosai.


✅ 4. LAUSHIN FATA DA LEMON TSAMI

Abubuwan hadawa:

🍋 Lemon tsami

🍯 Zuma


Yadda ake amfani:
Kafin kwanciya barci, ki hada lemon da zuma ki shafa. Da safe, ki wanke da ruwan dumi. Zai haskaka fata kuma ya hana kuraje.


✅ 5. MAN SHAFAWA DOMIN LAUSHIN JIKI

Abubuwan hadawa:

🥥 Man kwakwa

🌰 Man kade

🌿 Man angurya

🌿 Man zaitun

🌰 Almond oil

🍼 Baby oil

🧴 Madarar turare

🍫 Cocoa butter


Yadda ake amfani:
A hada dukkan mayukan, a zuba a kwalba. Ki rika shafawa bayan wanka. Jikinki zai yi laushi, santsi da kamshi.


✅ 6. SABULUN WANKA NA MUSAMMAN

Hade-haden sabulun:

🧼 Sabulun zaitun

🧼 Tetmosol

🧼 Sabulun salo da gana

🧼 Sabulun karas

🧼 Sabulun cucumber

🌿 Kurkur (turmeric)


Yadda ake amfani:
Ki hadasu su yi sabulu guda. Ki rika amfani da shi duk wanka. Zai tsabtace jiki, ya magance kuraje, ya hana duhu.


✅ 7. HADIN MAGANIN KURAJE

Abubuwan hadawa:

🍯 Zuma

🌿 Ruwan khal

🌿 Man zaitun


Yadda ake amfani:
A dafa su kadan a wuta, a kara ruwa, a juya sosai. Ki wanke fuskarki da sabulu, ki goge da auduga mai jika da wannan hadin. Yana kawar da kuraje da dattin fuska.


✅ 8. STEAMING NA FUSKA (Tururin Gyara Fuska)

Hadin farko:

🥚 Kwai

🍯 Zuma

🥛 Nono


Yadda ake amfani:
A hada a shafa a fuska, sannan a turara da ruwan zafi. Yana kashe kuraje da bude pores.

Hadin biyu:

🥛 Kindirmo (nono)

🌿 Man zaitun

🍯 Zuma


Yadda ake amfani:
A hada, a shafa a fuska, sannan a sa ruwa mai zafi a kwano, ki kara fuska a kai, ki lullube fuskar na minti 10–15. Daga nan ki wanke da ruwan sanyi.



✅ 9. DOMIN HASKEN FATA

Hadi na 1:

🌳 Itacen sandal wood

🌿 Kurkur

🥛 Madara


Hadi na 2:

🌿 Kurkur

🥛 Madara

🥚 Kwaiduwar kwai


Yadda ake amfani:
Ki shafa kafin wanka safe da yamma. Yana sa fata ta haskaka kamar zinariya.


✅ 10. GYARAN FUSKA MAI TUMBUR

Abubuwan hadawa:

🌿 Ruwan kal (vinegar) – cokali 10

🌿 Man zaitun – cokali 2

🍯 Zuma – cokali 2

💧 Ruwa kadan


Yadda ake amfani:
A dora a wuta su dan yi zafi, ki kara ruwa kadan. Ki tsoma auduga ki rinka goge fuska bayan kin wanke da sabulu. Yana cire duhu da tabo, ya sanya fuska tayi fes.

📝 Dukkan hadin nan na karkashin: SIRRIN RIKE MIJI
Don Allah a kiyaye hakkin mallaka, kada a kwafa ba tare da izini ba.

Post a Comment

0 Comments