Blue Ball (Ciwon 'ya'yan Gwalaqe)


Blue Ball (Ciwon 'ya'yan Gwalaqe)

Maza dayawa suna fama da ciwon Gwalaqe ko kuma Gwailo guda daya. Mutum zai ji Gwailon sa yana masa radadi kamar wadda ya bugu. Dayawa mutane suna tsammanin cewar wata matsala ce, amma a zahirin gaskia ba matsala bace, asali ma lafiya ce ta kawo haka.

Ba san mutane zasu yi mamaki saboda na ce lafiya ce take kawo haka. Eh tabbas lafiya ce.

Dalili kuwa shine. Shi Gwailo aikin sa yana riqe ruwan Maniyi ne, ma'ana a cikin sa maniyi yake taruwa kafin lokacin Jima'i a yi inzali ya fito. Idan maniyi ya taru a cikin Gwalaqen ka yayi yawa, yana buqatar ya fito, kai kuma bakka da aure, kuma bakka da wata hanya da zaka fitar dashi, to a nan ne sai Gwalaqen ka ko Gwailon ka ya fara maka radadi, saboda yana da buqatar fitowa amma bai samu ba. Wannan ya nuna maka cewar kai lafiyayye ne kuma kana da sinadarin haihuwa ko baka taba yin aure ba zaka iya fahimtar cewar lafiyar ka lau. Amma fa ba kowa ne yake da wannan larurin ba. Wasu ciwon ciki yake saka su, wasu kuma ciwon Gwalaqe (wato blue Ball a turance).

Hanyoyin magance wannan larura suna da yawa. Akwai haramtattu hanyoyi da kuma halaltattu.
Haramtattu sun hada da Zina da kuma Istim'na'i (Masturbation), while halal tattu sun hada da yin aure, ko kuma haquri, dannan sai mutum zai nesanta kansa da cin wasu daga cikin abincin da suke qasa sha'awar mutum.

Abincin da mutum zaiyi nesa dasu idan bashi da aure sun hada da; Ayaba (Banana), Tafarnuwa da kuma kifi musammam kifin mu na Hausa, sannan sai Qwai (egg), sannan sai madara, amma madara bata kai sauran qara ruwan maniyi ba. Tabbas wadannan abubuwa da na ambata sun fi kowane nau'in abinci qara ruwan maniyi. Kayi Googling ka gani.

Sau dayawa maza suna fama da wannan laruri na Blue Ball, amma suna dauka cewar wata cuta ce. Eh to, suna da gaskia, saboda akwai cututtukan da suke sanyawa ana yin ciwon Gwalaqe, amma mafi yawanci ciwon da aka fi yi na lafiya ne.
Taya za a gane bambancin ciwon lafiya da kuma ciwon rashin lafiya?
Ciwon rashin lafiya, yawanci zaka ga Gwailon ka daya ya fi daya girma, sannan zaka ji sha'awar ka ta gushe. Shi kuma ciwon lafiya (Blue Ball), zaka ji shawa'ar ka ta yi yawa, sannan Gwailon ka suna nan girman su daya, sannan zaka ji idan kana matsa su kana jin dadi, kamar yadda mai targade yake matsa ciwon sa yana jin dadi, haka kaima zaka dinga jin dadi idan kana matsa su.

Wasu sukan sha lemon tsami ko kuma kanwa domin su sami sauqi.

Kanwa da lemon tsami, aikin su shine, suna tsinka ruwan maniyi ne kamara yadda Kunu yake tsinkewa idan yayi ruwa, daga nan sai mutum ya zubar da maniyin ta cikin fitsari, daga nan kuma sai balls dinsa su dawo empty banu maniyi a ciki, sai kuma bayan kwanaki idan kana cin abincin da zai qasa maniyi sai ya dawo.
Wasu suna gani kamar wai hakan zai iya bada matsala. A zahirin gaskia babu wata matsala da hakan yake haifarwa. Kawai ka zubar da maniyin ka ne, kuma abincin da kake ci ya sake kawo maka wasu. A rana daya ma zaka iya dawo da ruwan maniyin ka. Kawai ana yi ne donin a samu salama da kuma kashe gobara.
Kai kanka ai ya kamata ka tambayi kanka, shin in da suka bada matsala, meyasa ba'a daina shan lemon tsami da kuma kanwa ba kwata-kwata?
Allah dai yasa mu dace.
In akwai mai tambaya sai yai muna jinsa, kuma zamu bada amsa.
Sannan muna maraba da qarin bayani

✍️ Abdulhadi Abba Kyari



Ayi share

Post a Comment

0 Comments