🍉 Amfanin kankana wajen inganta lafiyar jima'i. 🍉


🍉 Amfanin kankana wajen inganta lafiyar jima'i. 🍉

Mutane da yawa suna mamakin irin amfanin da jar kankana keda shi ga maza.

Maza da dama suna yin amfani da magunguna kala daban-daban don ganin sun magance matsalolin raunin mazakuta.

Abinda baku sani ba shine, kankana na iya zama madadin wasu nau’o’in magunguna da ake amfani da su wajen magance matsalar raunin al'aura, kamar su Viagra, musamman a lokutan da aka hana ka amfani da magungunan, kamar ga masu fama da ciwon zuciya, ko ciwon kirji.

Kankana tana iya samar da sinadarin citrulline ta hanya ta dabi'a, wanda yana daya daga cikin sinadiran amino acid dake inganta lafiyar mazakuta, wanda a fakaice yake taimakawa maza a yayin jima'i da kuma kara inganta musu al'amuran da suka shafi jima'i.

Domin samun fa'idar kankana wajen jima'i, ana shawartar maza da su sha ruwan kankana da aka fitar (watermelon juice) zallar sa ba surki domin samun adadi mai yawa na sinadarin citrulline, domin mafi yawan kankana na kunshe da ruwa, sannan kuma jiki yana iya mayar da amino acid citrulline zuwa amino acid arginine, wanda yake sauyawa izuwa nitric oxide, wanda ke taimakawa wajen fadada hanyoyin jini, wanda ke inganta gudanar Jini ya kai har zuwa ga al'aurar namiji. 

ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA. 

✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam

Post a Comment

0 Comments