Muhimman Shawarwari 20 Ga Mai Aure Da Mai Neman Aure:👇🏿



Muhimman Shawarwari 20 Ga Mai Aure Da Mai Neman Aure:👇🏿

1. Idan kai tsoho ne, kar ka auri matashiya, saboda ba za ka Iya biya mata buƙatar sha'awa ba, dalilin haka za ta ƙosa da kai, kuma ƙarshenta ta shiga neman wasu mazan kuma ba yadda ka iya, sai dai ka zamo mara kishi (dayyus), ka yi asarar mutuncinka, rayuwarka ta yi ƙunci, lahirarka ta lalace. Sannan za ka rayu cikin cutuwa, saboda za ka fuskanci gatsali da maganganun banza daga gare ta, da mu'amala mara daɗi.

ولا تنكحن إن كنت شيخا فتية
تعش في ضرار العيش أو ترض بالردي

2. Kar ka auri wadda ta fi ka matsayi da ɗaukaka, idan ka aura za ka samu ƙuncin zama tare da ita, saboda za ta dinga maka alfahari, kuma ba za ta damu da kai ba saboda ƙasƙancinka, da tawayarka a idonta, kai za ka zamo kana rayuwa ƙarƙashin dokokinta, ba ita ba. 

ولا تنكحن من نسم فوقك رتبة
تكن أبدا في حكمها في تنكد

3. Kada kwaɗayin dukiyar mace da abin hannunta ya sa kana talaka ka je ka auro mai kuɗi, lallai idan ka auro mai kuɗi alhalin kana talaka za ka ƙasƙanta saboda rashin fifikonka a kanta, da kasa biya mata buƙatu da za ka yi, da buƙatuwarka ga dukiyarta, gwargwadon gajartan hanunka (wajen mata hidima), gwargwadon tsawon harshenta (wajen jefa maka maganganun rashin kyautawa), kuma gwargwadon yadda za ta buwaye ka, ta raina ka, ta ɗamfaru da ƴan'uwanta ta watsar da kai, za ka ƙasƙanta a gabanta irin ƙasƙantar da manemi yake yi a gaban wanda ake nema wajensa, ga tsawon lokaci (da za ku rayu) da yawan gori, sai lamari ya cakuɗe maka, ka ƙare a damuwa.

ولا ترغبن في مالها وأثاثها
إذا كنت ذا فقر تُذَلُّ وتضهدِ

4. Kar ka yarda ka yi aure ka zauna a gidan matarka, musamman tare da danginta, saboda za ka ji maganganu mara sa daɗi daga wajensu, na daga aibatawa da zagi da gori da cutarwa, saboda izzarta da ƙasƙancinka, da wadatarta da talaucinka, da ɗamfaruwarta da danginta a yayin da kai kuma kake bare, za ta dinga maka girman kai da nuna falala/fifiko, a yayin da kai kuma kake kwantar da kai kana ƙasƙanta. To duk wanda wannan ya zama halinsa, makomarsa a aure ta zama haka, babu alheri a cikin rayuwarsa kuma ba shi ba jin daɗi. 

ولا تسكنن في دارها عند أهلها
تُسَمَّع إذا أنواع من متعدد
فلا خير فيمن كان في فضل عرسه
يروح على هون إليها ويغتدي

5. Idan matarka ta yi sadaka ko ta kyautar da ɗan abin da bai kai ya kawo ba daga cikin abin da ka kawo, kar ka mata inkarin hakan kana mai nuna rowa da kwaɗayi da son abinka, abin da ya dace da kai a irin wannan halin shi ne ka kau da kai ka zamo mai kyauta da karamci, idan ka yi haka za ka samu lada, kuma za ka samu daɗin zama da ƙarin ƙauna tsakaninka da iyalinka, Annabi (SAW) ya ce: "Idan mace ta ciyar daga dukiyar mijinta ba tare da ɓarna ba, tana da ladar ciyarwarta, mijinta yana da ladar nemowa, mai ajiya ma yana da ladansa, ba tare da wani ya tauye ladan wani ba daga cikinsu". (Bukhari:1359, Muslim: 1024).

ولا تنكرن بَذْلَ اليسير تَنَكُّدًا 
وسامح تنل أجرا وحسن التودد

6. Kada ka zama mai binciken ƙwaƙwaf a kan komai, saboda ƙoƙarin tona komai ƙeƙe da ƙeƙe yana daga cikin ɗabi'un marowata da masu son kai. Sannan ka rintsa idonka ka basar daga kasawar matarka idan ba a kan abin da yake na zargi ba a shari'ance, saboda dagewa wajen kallon aibi shi ma aibi ne, shi ya sa abin da ya fi shi ne kawar da kai, wani mai hikima yana cewa: "Mutum mai hankali shi ne mai hikima mai kawar da kai".

Amma idan ta aikata abin zargi a shari'a ne to wajibi a yi tanbaya da bincike, saboda ana kawar da kai ne a harkar rayuwa kawai ko wajen rashin cika wani ladabi cikin ladubban zamantakewa, amma cikin lamarin addini da kare mutunci, ba kyau a dinga ɗauke kai daga kuskure, musamman a kan wajibai.

ولا تسألن عما عهدت وغُضَّ عن 
عَوَارٍ اذا لم يذمم الشرع ترشد

7. Ka sani da kyau cewa mata kayan amana ne kuma tamkar kamammun yaƙi a hannunka, saboda haka ka yi riƙo da wasiyyar Annabi (SAW) da ya ce a riƙe su da alheri.

وكن حافظا أن النساء ودائع 
عَوَانٌ لدينا احفظ وصية مرشد

8. Kar ka yawaita suka da ƙorafi a kan matarka, idan ka yi haka za ka sa a dinga tuhumar ta (ka ɓata mata suna) saboda yawan inkarinka a gare ta, har mutane su yanke hukuncin ita mai munanan ɗabi'u ce. Sannan kar ka zama daga wani ya yi laifi cikin ƴaƴanka ko matanka ka hau shi da duka, lallai rashin duka ya fi tabbatar da ƙauna, ka yi koyi da Annabi (SAW) da Nana A'isha (R.A) take cewa: "Bai taɓa duka da hannunsa ba sai a wajen jihadi" (Bukhari:3367, Muslim: 1814).

ولا تكثر الانكار تُرْمَ بتهمة 
ولا ترفعن السوط عن كل معتد

9. Kar ka yi ƙoƙarin miƙar da karkatar matarka ka ce sai ta zama ɗari bisa ɗari, saboda misalinta wajen karkacewa kamar ƙashin haƙarƙari ne, saboda hadisin da ya zo cikin Bukhari:3153 da Muslim: 1090, Annabi (SAW) ya ce: "An halicci mace daga ƙashin haƙarƙari, kuma mafi karkacewar haƙarƙari shi ne na can samansa, idan ka ce za ka tsayar da shi za ka karya shi, idan ka bar shi kuma zai zauna a karkace.

ولا تطمعن في أن تقيم اعوجاجها
فما هي إلا مثل ضلع مردد

9. Kar ka yi ƙoƙarin miƙar da karkatar matarka ka ce sai ta zama ɗari bisa ɗari, saboda misalinta wajen karkacewa kamar ƙashin haƙarƙari ne, saboda hadisin da ya zo cikin Bukhari:3153 da Muslim: 1090, Annabi (SAW) ya ce: "An halicci mace daga ƙashin haƙarƙari, kuma mafi karkacewar haƙarƙari shi ne na can samansa, idan ka ce za ka tsayar da shi za ka karya shi, idan ka bar shi kuma zai zauna a karkace.

ولا تطمعن في أن تقيم اعوجاجها
فما هي إلا مثل ضلع مردد

10. Kar ka zauna ko kai kaɗai ko da iyalinka a gida/ɗakin da masu wucewa kan hanya za su dinga gano ku, saboda hakan zai iya haifar da tuhuma, a yi zaton kun yi hakan ne don ku dinga leƙa mutane, ko kuma wani yana iya ganin matarka dalilin hakan, kuma ƙarshe abu ya haifar da fitina. 

وسكنى الفتى في غرفة فوق سِكَّةٍ
تؤول إلى تهمى البريء المشدِّدِ

11. Ka kiyayi auren kyakkyawar mace daga gidan da ba su da kamun kai ko da kuwa ita mai kamun kan ce, saboda da da ƙyar ne ka ga halin gidansu bai rinjaye ta ba. 

وإياك يا هذا وروضة دمنة
سترجع عن قرب الى أصلها الردي

12. Kar ka yi aure idan kana fama da talauci in ba don larura ba, kamar tsoron faɗawa zina, idan ka samu kanka a wannan yanayin to ka nemi macen ƙwarai daga gidan talakawa, wadda ka san za ta dinga girmama kaɗan ɗin da kake ba ta, sannan kuma ka cike gurbin talauci naka da kyawawan ɗabi'u da sakin fuska da daɗin zama. Idan ba ka yi auren ba ka nemi kariya ta hanyar yawaita azumi, saboda wasiyyar Annabi (SAW).

((مَنِ اسْتَطاعَ الباءَةَ فَلْيَتَزَوَّجْ، فإنَّه أغَضُّ لِلْبَصَرِ، وأَحْصَنُ لِلْفَرْجِ، ومَن لَمْ يَسْتَطِعْ فَعليه بالصَّوْمِ، فإنَّه له وِجاءٌ.)) البخاري (١٩٠٥) مسلم (١٤٠٠)

((وَلْيَسْتَعْفِفِ الَّذِينَ لَا يَجِدُونَ نِكَاحًا حَتَّى يُغْنِيَهُمُ اللَّهُ مِنْ فَضْلِهِ)) نور: ٣٣

ولا تنكحن في الفقر الا ضرروة 
وَلُذْ بوجاء الصوم تَهْدِ وتهتدي

13. Ka san cewa mata abokan wasanmu ne, da muke raha da su muke nutsuwa izuwa gare su, kuma ranmu yake daɗi idan muka gan su, saboda haka ka kyautata wajen nema ka samu mai kyawawan halaye, mai kyakkyawan asali, don ka samu cikar buri.

وكن عالما أن النسا لُقَبٌ لنا 
فَحَسِّنْ اذا مهما استطعت وجَوِّدِ

14. Ka san cewa mafi alherin mace ita ce wadda idan mijinta ya kalle ta yake farin ciki, ida ba ya nan ta tsare gidansa da mutuncinta, mai gajeren harshe, ba ta magana sai mai amfani, ba ta yawon gidajen mutane da kasuwanni, mai gajeren gani, ba ta sha'awar kowa sai mijinta, ya zo cikin sahihu Muslim:1467, Annabi (SAW) ya ce: "mafi girman jin daɗin duniya shi ne mace ta gari".

وخير النسا من سرت الزوج منظرا
ومن حفظته في مغيب ومشهد
قصيرة ألفاظ قصيرة بيتها 
قصيرة طرف العين عن كل أبعد

15,16,17,18. Ka nemi budurwa (mai ƙananan shekaru), ma'abociyar addini, ma'abociyar asali, mai son ka a matsayin mijinta, kuma mai haihuwa. Idan kana neman rabauta da ƴaƴa na gari, ka zaɓa musu uwa mai asali nagari, saboda idan mutum ya yi aure daga tushe mai kyau, ɗan zai zo yana kamanceceniya da jinin mahaifiyarsa a ɗabi'u da ayyuka. 

عليك بذات الدين تظفر بالمنى 
الودود الولود الأصل ذات التعبد
حسيبة أصل من كرام تفز إذًا 
بولد كرام والبَكَارةَ فاقصد

Ga wasiyyoyin Manzon Allah (SAW) da suka zo a kan haka:

١. ((تُنْكَحُ المَرْأَةُ لأرْبَعٍ: لِمالِها، ولِحَسَبِها، وجَمالِها، ولِدِينِها، فاظْفَرْ بذاتِ الدِّينِ، تَرِبَتْ يَداكَ)).
 البخاري (٥٠٩٠)، مسلم (١٤٦٦)

٢. ((تزوَّجو الولودَ الودودَ فإنِّي مُكاثرٌ بِكُمُ الأممَ يومَ القيامة)) أبو داود (٢٠٥٠)

٣. ((عليكُم بالأبكارِ فإنَّهنَّ أعذَبُ أفواهًا وأنتَقُ أرحامًا وأرضى باليَسيرِ)) ابن ماجه (١٥٢٠)


19. Ka wadatu da mace ɗaya idan ka samu kamewa da ita, saboda hakan zai fi maka sauƙin yin adalci da kuɓuta daga zalunci, idan kuma ka buƙaci ƙari kana da damar yin har huɗu, kar ka ƙara a kan haka, (saboda shi ne iyakar shari'a). 

وواحدة أدنى من العدل فاقتنع
وان شئت فابلغ أربعالا تُزَيِّدِ

20. Ka sani cewa duk wanda tsoron Allansa ya sa ya kame daga lalata da zuri'ar wasu, to shi ma za a kare masa nasa zuri'ar daga zina.

ومن عَفَّ تَقْوًى عن محارم غيره 
يَعَِّف اهْلُهُ حَقًّا وان يَزْنِ يُفْسِدِ


Asalin karatun yana cikin littafin تحفة الأحباب شرح نظم الآداب, shafi na 108-116: فصل في آداب النكاح. Allah ya sa mu dace.

@mallam bahaushe 

Post a Comment

0 Comments