Yadda Zaki Nunawa Masoyinki Ke Fa Ta Dabance.


Yadda Zaki Nunawa Masoyinki Ke Fa Ta Dabance.

#Tsangayarmalamtonga
 
Wani lokacin dole sai kin nunawa masoyinki kefa ta dabance a wajensa. Dole ki nuna masa kina da wata baiwar da ba duk mace ke d shi ba.

Yana da kyau ki tabbatar masa da cewa samunki a rayuwarsa nasara ne a gareshi shi.

Ga wasu hanyoyin da zaki iya nunawa masoyinki ke ta dabance.

 
🎀 Ki tuna masa irin mazan daya kasa kamin ya samu soyayar ki. Wannan wani yanayi ne da yake sa namiji ya kara jin son matarsa.

🎀 Nunawa Mijinki irin yarda da amanna da kika masa. Ganin akasarin mata basu cika baiwa mazansu yarda ba. Amma ke gashi baki shakkar mijinki. 

🎀 Ki nuna masa yadda kike bashi damar yin harkokinsa ba tare da kin masa shinshigi ba.

🎀 Nuna masa ba ruwanki da abokan hukdarsa bare ki bibiyi lamuransa. 

🎀 Tabbatar masa da yadda baki riko dashi a zuciyarki. Ya san cewa a duk lokacinda kuka samu sabani da zaran kun fahimci juna kin manta da zancen.

🎀 Nuna masa yadda bakison ganin wani abu ya cutarsa da shi. Fahimtar dashi irin so da kaunar da kike masa tsakaninki da Allah .

#TsangayarMalam 

Ba kina fadawa masoyinki wadannan abubuwan domin bai sansu bane, sai dai kina tunatar dashi ne domin ya fahimci cikin jerin ni'imar da Allah Ya masa, har dake.

Post a Comment

0 Comments