Hanyoyi 10 Da Zaki Hana Mijinki Sha'awar Kara Aure:



Hanyoyi 10 Da Zaki Hana Mijinki Sha'awar Kara Aure:

#Tsangayarmalamtonga 

Ba duk maza suke da burin kara aure ba. Wasu mazan hakan yana zuwa musu kawai saboda babu yadda suka iya.

Daya daga cikin abubuwan dake sa wasu mazan kara aure bai wuce rashin iya mu'amalar zaman aure da wasu matan basu iya ba.

Ga wasu abubuwan da duk macen data dage da yiwa mijinta su, zai yi wuya ya daga kai ya ga wata mace da sunan soyayya bare ma yace zai kara aure.

 
1: Ki Girmama Mijinki.
2: Kirashi da suna mafi soyuwa a gareshi. 
3: Saurareshi cikin kauna da soyayya idan yana miki magana.
4: Ki Karfafa Masa Gwaiwa Aka Burukansa.
5: Ki Zama Kece Goya Masa Baya Ta Farko A Bayyane Aka Wani Burinsa Na Siyasa Ko Neman Wani Matsayi.
6: Ki Nuna Masa Gamsuwarki A Lokacinda Ya Miki Wani Gyaran Kuskurenki.
7: Ki Masa Gyara Cikin Mutuntawa Da Girmamawa.
8: Ki Kwarai Wajen Dafa Masa Irin Abincin Daya Yafi So.
9: Ki Guji Nuna Gajiyawarki Wajen Gamsar Dashi A Jima'ince.
10: Ki Mutunta Duk Wani Na Kusa Dashi.

#Tsangayarmalamtonga

Tabbas duk macen da zata daure da yiwa mijinta wadannan abubuwan, ko dole aka aura masa ita zata samu saukin zama dashi.

Post a Comment

0 Comments