MATSALAR WARIN BAKI


MATSALAR WARIN BAKI

Warin baki shi ne lokacin da mutum ya ke magana sai wari ko ɗoyi mara daɗi ya dinga fita daga bakinsa, wani ma ko bai yi magana ba numfashinsa ma kawai wari ya ke fitarwa. Wani idan yana da warin baki shi kansa yana jin warin, wani kuma ba ya ji, sai dai kawai ya ga in yana magana mutane suna toshe hanci ko kau da fuska. 

   Mutum na iya kamuwa da matsalar warin baki saboda dalilai da dama. Ga wasu daga ciki. 

1- Rashin tsaftar baki. 
    Rashin wanke baki yadda ya kamata na iya sa wa wasu ƙwayoyin cuta su dinga girma da yawaita acikin bakin mutum, waɗanda ke maida abincin da ya maƙale acikin baki ya koma mai wari ko ɗoyi. 

     2- Rashin sakace baki idan an ci abinci. 
       Musamman nama ko kifi da dai sauransu, ragowar abincin da ya maƙale acikin haƙora ba a sakace shi ba, yana ruɓewa ne a cikin haƙoran, ya dinga ɗoyi, wani sa'in ma yana yin tsutsotsi, wanda hakan ke haifar da warin baki da ciwon haƙora. 

     3- Bushewar baki. 
          Idan ya zama miyau na ɗaukewa a bakin mutum, zai zama bakinsa yana bushewa, wanda hakan ke sa wasu ƙwayoyin halitta a bakin mutum su dinga wari. 

   4- Shan taba. 
      Shan taba kan iya janyo warin baki saboda sinadarai masu ƙarfi da ke cikinta da kuma yadda ta ke ta'adi ga lafiyar bakin mutum. 

       5- Kogon haƙori, olsar baki da kuma rauni acikin baki. 
      Dukkan waɗannan suna iya kama abincin da mutum ya ci, su riƙeahi a jikinsu, har ya ruɓe acikin baki ya dinga wari. 

     6- Cututtukan baki. 
            Kamar cirewar haƙori, ruɓewar haƙori da kuma cututtukan dadashi, duk suna iya janyo warin baki. 

  7- Diabetes da wasu nau'ukan rashin lafiya na iya sa wa bakin mutum ya dinga wari. 

      8- Rashin cin abinci ko yin Azumi. 
        Idan mutum ya ɗau lokaci mai tswo bai ci abinci ba hakan na iya sa wa idan yay numfashi a dinga jin wari yana fita daga bakinsa saboda babu komai a cikinsa, sai abinda ya daɗe acikin hanji.

    9- Cin abinci mai ɗauke da acid da yawa. 
     Kamar Albasa, tafarnuwa, da dai sauransu. Waɗannan kan sa warin acid ɗin ya dinga tasowa idan mutum yana maga, suna fitowa ta bakinsa.

    Da akwai hanyoyi da dama da ake bi domin magance warin baki da kuma hnayoyin rigakafi. 


Post a Comment

0 Comments