Amfanin Za'afaran (saffron) guda 5 masu ban mamaki.
Za'afaran na daya daga cikin sinadaran girki (spices) mafi tsada a duniya saboda yana da wahalar girbi sannan kuma yana da buƙatar aiki mai yawa wajen samar dashi.
Za'afaran yana ƙunshe da Nutritional properties masu yawa da chemicals waɗanda ke bawa jiki kariya daga cututtuka.
Menene amfanin Za'afaran ta fannin lafiya?
■ Yana Inganta Garkuwar Jiki:
Ko da yake kuna iya tunanin cewa ana amfani da Za'afaran ne kadai kawai don kara dandano a cikin nau'o'in abinci daban-daban.
A wani bangaren kuma yana ƙunshe da muhimmin sinadirai, irin su ascorbic acid. Shi wannan acid din yana da amfani ga lafiyar ku, saboda yana ƙarfafa immune system na samar da white blood cell wanda ke taimakawa jiki wajen bashi damar samar da kariya daga cututtuka.
Bugu da ƙari, yana kara yawan samar da collagen, wanda ke taimakawa wajen warkar da rauni, girman tsoka, gyara jijiyoyin jini, da samar da tissues.
■ Yana bada kariya ga lafiyar zuciya:
Yana da kyau mutum yasan hanyar da zaibi don inganta lafiyar zuciyar sa da hanyoyin jini, amma akwai hanya mai sauƙi don yin haka, wato ta hanyar ƙara yawan adadin potassium. Potassium din da ake samu a cikin za'afaran yana aiki a matsayin vasodilator, wanda ke rage pressure a hanyoyin jini da arteries yadda ya kamata, kuma yana rage hadari faruwar bugun zuciya da atherosclerosis da stroke.
■ Yana magance damuwa:
Za'afaran yana kawar da damuwa sannan kuma yana inganta yanayi ga waɗanda ke amfani dashi akai-akai.
Za'afaran yana ƙunshe da adadi mai yawa na active compounds waɗanda ke saka endocrin system kai tsaye sakin hormone na farin ciki wanda akafi sani da serotonin.
■ Yana kara inganta ƙarfin kashi:
Wasu daga cikin minerals da organic Compounds da ake samu a cikin za'afaran suna da alaka mai kyau da absorption din nutrients musamman ma calcium.
Bugu da kari, saboda za'afaran yana iya samar da adadi mai yawa na calcium ga jiki, structure din kashi yana inganta, wanda hakan ke bada kariya daga rashin karfin kashi wato Osteoporosis.
■Yana bada kariya daga ciwon daji:
Za'afaran yana ƙunshe da adadin kaso mai yawa na antioxidant waɗanda ke aiki don kawar da free radicals waɗanda ke haifar da lalacewar kwayoyin halitta (cell damage) da kuma ciwon kansa.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.
✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam
0 Comments