Amfanin Bay leaf


Amfanin Bay leaf

■ Bay leaf yana magance matsalolin tsarin narkewar abinci:

Bay ganye yana taimakawa wajen kawar da kumburin ciki, Heartburn, acidity, Cushewarciki, sannan kuma yana daidaita motsin hanji.

Ana amfani dashi ta wannan tsarin ta hanyar shan shayin bay leaf mai zafi.

■ Yana saukar da sukarin jini:

Bay leaf antioxidant ne, yana bawa jiki dama don samar da sinadarin Insulin.

Ana amfani da shi a wannan tsarin ta hanyar cin shi a cikin abinci ko shan shayin bay leaf na tsawon wata guda.

■ Yana kawar da mummunan cholesterol da fitar da kitse daga jiki.

■ Yana da matukar amfani wajen magance mura da tari mai tsanani domin yana da wadataccen sinadarin vitamin C.

■ Ana tafasa ganyen ayi surace dashi domin kawar da majina da rage tari mai tsanani.

■ Yana ƙunshe da caffeic acid da quercetin, eugenol da Parthenolide, waɗanda sune abubuwan da suke hana samuwar ƙwayoyin cutar kansa a cikin jiki.

■ Yana kawar da larurar rashin barci da damuwa, idan aka sha shayin sa kafin barci, yana taimakawa wajen samar da nutsuwa da kwanciyar hankali da samun barci mai dadi.

■ Shan kofin dafaffen ganyen bay leaf sau biyu a kullum, yana narkar da tsakuwar koda.

ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA. 

✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam

Post a Comment

0 Comments