HANYOYIN RAGE ƘIBA DA TEƁA


HANYOYIN RAGE ƘIBA DA TEƁA

Masana sun bayyana cewa domin kyautata lafiyarka a yayin da ka manyanta, yana da matukar amfani a guji kiba, domin za ta iya haddasa cututtuka da daman gaske, wadanda suka hada ciwon suga, matsalolin zuciya, ciwon ƙafa (gout)
da sauransu.



Za ka iya kaucewa fadawa cikin jerin wadanda kiba ke saurin lalata musu rayuwa ta yin amfani da hanyoyi kamar haka:-

★ Ka tanadi lemun zaki da citta. A tafasa su minti hudu zuwa biya, a yi shayi ban da madara. A zuba MA’UL – KHAL ( Karanta cikakken bayani akan amfanin Ma'ul khal a cikin wannan shudin rubutun. bashirhalilu.my
wapblog.com/amfanin-maul-khal.xhtml )
cokali daya ko biyu, cikin kofin shayin a sha da ganyen shayi kamar Lipton da zuma ko suga.
Za a yi haka sau biyu a kullum.
Haka kuma za ka iya amfani da lemun tsami a madadin MA’UL-KHAL din.
.
★Bayan haka, mutum ya rika motsa jiki a kai a kai. Idan kana ganin cewa ba
ka da lokacin motsa jiki, to sai ka rika gudanar da wasu aikace aikacen
gida da kan ka.
Abin bukata dai, kada mutum ya yi tunanin cewa “Na fi
karfin in yi wanki alal misali, don ina da hali...” Yi tunanin ‘na fi son
lafiyata fiye da komai!’
.
.
★ Bayan wannan, za ka iya samun kwayar ‘ya’yan zogale a markada a hada da ruwan zafi a rika sha da safe da dare yana
maganin rage kiba ko tumbi.
.
.
★ A wani bangare kuma, idan mace na da
bukatar rage kiba, to abu mafi sauki da ya kamata ta yi a takaice shi ne
kamar haka: Abu na farko da za ta nema shi ne zogale, bayan an gyara
an wanke shi, sai a markada, sannan a tace ruwan, kana a rika sha safe
da kuma dare, ma’ana kullum sau biyu a rana.
Sai dai kar a manta
binciken ya bayyana cewa, akwai yiwuwar sanya gudawa, saboda an hau
turbar rage kiba ne. Muddin aka yi amfani da wannan dabara kamar
yadda aka bayyana, to mace za ta rage kiba sosai da sosai, har namijin.
.
Karanta cikakken bayani akan amfanin Zogale a cikin wannan shudin rubutun
bashirhalilu.mywapblog.com/amfanin-zogale-benefits-of-moringa-read.xhtml
.
.
★ Sannan kuma ga wanda yake da tumbi, sannan ya ke son rage shi, to sai ya sami
sassaken Gamji ya hada da ‘yar jar kanwa, sannan a tafasa a rika sha, in
Allah Ya yarda za a neme shi a rasa. Saboda shi maiko yake tsotsewa a
jikin dan Adam!
.
.
★ Ko kun San Cin Dafaffen Kwai Na Rage Kiba?
Kamar yadda binciken ya nuna, cin dafaffen kwai tare da kunduwarsa baki daya, ya na matukar rage kiba tare da sanya koshin lafiya.
Saboda haka, yasar da
kunduwar kwai ba dabara ba ce, idan aka yi la’akari da irin rawar da take
takawa wajen gina jiki da kuma kara ingantacciyar lafiya ga jikin bil-
Adama. Haka zalika, kai tsaye za a iya cewa, cin dafaffen kwai a
matsayin karin kumallon safe ga dan Adam, na yin tasiri ta yadda duk
wani abu da aka ci wadda ke sanya kiba, to ko kadan a wannan ranar ba
zai yi tasiri ba. Har ila yau a wani binciken da aka gudanar a kasar
Amurika, ya nuna cewa, wadanda ke amfani da dafaffen kwai a matsayi
karin kumallon safe ba za su taba zama daya da wadanda ba sa yi da shi
ba, ta fuskar rage kiba, tare da sanya kuzari da kuma yalwata lafiyar jiki
baki daya.
.
.
★ Haka kuma za ka iya samun Garin Sanamakiy ka rika dafa cokali guda kana sha
tare da Zuma.
.
.
★ Sannan ka rika shan Man Habbatussauda Cokali guda acikin ruwan dumi ko
shayi. Kullum kafin ka ci komai.
.
Insha Allahu Qibarka zata ragu. Amma ka hada da yawan Motsa jiki,
kuma ki rage cin Maiqo. Maimakon haka ka yawaita cin 'Ya'yan Itace
tare da ganyayyaki.
.
.
bashirhalilu.mywapblog.com
Ya`yan Itatatunwa dake Raye Kiba
.
.
Akwai ya`yan itatuwa guda uku dake rage kiba wanda zan fada, Ita dai
Kiba bata raguwa sai an rage ciye-ciye mussaman na abin da aka sarrafa
shi domin ya dadi ko kuma aka dafa shi da mai.
.
.
1. ALBASA
Da farko kafin ina ce komai bari in fara da cewa tarihi ya nuna Albasa na
daya daga cikin abin da yake sa mutane samun ingantacciyar lafiya, kuma
bincike ya nuna Albasa da Tafarnuwa nada kunshe da kayan mussanman
wanda ke kare garkuwar jikin mu masu karfi, wasu daga cikin cututtuka
da albasa ke karewa sun hada da ciwon zuciya, genbon ciki da kuma
yana raye girman ciwo kadan daga cikin aiyukan ta a jikin dan adam
kenan.
Ya rayuwa zata kasan ce ba Albasa ? cin albasa danya nada amfani idan
zaka iya ko cikin salka, ko cikin Kwain karin kumallon safe da kuma cikin
abincin rana ko dare.
Tafarnuwa nasa jini ya gudana da kuma raye kitse dake tare hanyuyin jini.
shekaru da shekaru tafarnuwa na daya daga cikin abubuwan dake kara
armashin abinci
.
Karanta cikakken bayani akan amfanin Tafarnuwa a cikin wannan shudin rubutun bashirhalilu.my
wapblog.com/amfanin-tafarnuwa-ga-mata.xhtml
.
Karanta cikakken bayani akan amfanin albasa a cikin wannan shudin rubutun
bashirhalilu.mywapblog.com/amfanin-albasa-2.xhtml
.
.
2. CITTA
Citta na daga cikin itattuwan dake kara kuzari a jikin dan adam, An jima
ana amfani da citta a kasar Sin( China)a matsayin magani da karin
armashi kin abinci
kadan daga cikin abubuwan da Citta ke kara shine:
Tana kara gudanar jini
Tana kara kwanatar da jijiyoyin jini
Tana kare jiki da cuttitika
Tana kare kuburin jiki
Tana rage cuttar hunhu, sayi, mura da sauran su.
Yanzu bari na koma kan itaciya ta uku dake da amfani da kona kitse a
jikin mu
wanda zaka ci ba far gaba wani abu ko haufi.
.
Karanta cikakken bayaninakan amfanin citta a cikin wannan shudin rubutun
bashirhalilu.mywapblog.com/amfanin-citta-wato-zanjabiyl.xhtml
.
.
3. AYABA
Ayaba mutane da yawa na son cin ayaba da kyada ko kuma bayan cin
abinci, Na sha ganin tambayoyi akan wai ayaba nasa kiba ? amma amsar
shine ba dan itaciyar dake sa kiba idan ka cishi kamar yarda aka fiddo shi
daga lambu balle har ma yasa kiba.
Ayaba na narkewa cikin mintina (45)sauran ya`itatuwa na narkewa cikin
mintina (15) wannan shine yasa kasa zaka ji wasu na cewa cikina ya cika
na ci ayaba amma bayan mintina 45 zasu ji kuma duk ya narke. Idan
mutum zai mai da ayaba da sauran ya`yan itatuwa abin karin kumallon sa
cikin sati daya zaiga chanji wajen kibar sa.... Ayaba na tattare da kayan
gina jiki wanda ba zai sa kiba..... amma samun amfanin ta shine a ci
ayaba kafin ka ci komai kuma idan zaka ci abinci da ita ta kan dauki
lokaci wajen narkewa.
.
.
4. KANKANA
Abu na hudu shine Kankana itaceya mai armashi wajen hada abin sha
mussaman ma ace kayan sayi kuma kankana bata kara kiba saboda
kashi 90% dinta ruwa ne kuma tan kunshe da kaya gina jiki da zasu kare
jiki daga cuttutuka.
.
.
Ga wanda yake bukatar magungunan rage kiba, zai iya samu acibiyatar Tarbiyyah Islamiyyah, muna da su hadaddu da sauran magungunan gyaran jiki dana cututtukan sihiri dana jinnu.
.
Daga shafin Bashir Halilu .

Post a Comment

0 Comments