AMFANIN AMBAR WAJEN KYAUTATA LAFIYA


AMFANIN AMBAR WAJEN KYAUTATA LAFIYA

Bayan amfanin da Ambar yake da shi wajen kiwon lafiya, haka ma yana
taimakawa wajen cututtukan jiki da na jinnu ko sihiri.

Ana iya hada Ambar da wasu magungunan kamar zuma, miski, habba, zaitun, za'afaran da dai sauransu, ayi amfani da shi don samun ingantacciyar lafiya

★ Yi amfani da Ambar kadan ka samu lafiya mai yawa da yaddar Allah.

★ Ana samun Anbar na gari, ana samun na ruwa, ana samun na turare, ana
samun kwa6a66e na shafawa, sannan da akwai original wanda ba a sarrafa ba. 

1-Yana sanya nishadi idan aka sha kilogram daya tare da zuma cokali daya. 

2- Yana kara karfin hakori idan ana goge hakora da man sa.

3-Yana maganin cututtukan kwakwalwa idan ana shan sa tare da Man zaitun da Habbatussauda'a.

4-Ga mai lalurar hauka sai adinga tofa ayoyin Ruq'yah a cikin Ambar a zuba a ruwa, a ba shi ya sha kuma a dinga yi masa hayaki da shi musamman a hada da miski wajen hayakin.

5- Ciwon kai bari guda sai a hada Ambar da jan miski da Man juda a kwaɓa, a dinga shafawa a kan kuma ana yin hayakin sa.

6-Ana amfani da Ambar wajen ɓata sihiri wanda mutum ya ci ko ya sha, ta hanyar shan ɗan kaɗan acikin man zaitun cokali ɗaya. 

7-Masu hawan jini su sha kadan a cikin ruwa.

8-Don gyaran fata da jin dadin jiki sai a diga Ambar kadan a cikin ruwan wanka ay wanka da shi.

9- Mai son yin bacci mai dadi shi ma sai ya zuba kadan a ruwan wankansa, yai wanka da shi. 

10- Ambar yana taimakawa kwakwalwa wajen samun hutu mai dadi.

11-Amfani da Ambar yana kara kyautata karfin zuciya.

12- Masu cutar Asthma su ma Ambar yana taimaka musu idan suna amfani da shi.

13- Amfani da Ambar yana kara kyautata gudanawar jini a jikin mutum.

14- Yana kuma kara karfin jima'i ga maza da mata.

15- Amfani da Ambar na saukaka narkewar abinci a cikin ciki.

16- Yana kara soyayya tsakanin miji da mata, idan dayan su yana amfani da shi.

17- Warkewar ciwo da kashe kwayoyin cuta, sai a zuba man Ambar a kan
ciwon bayan an wanke shi. To zai warke cikin sauki insha Allah.

★ Amma a kula.

★ Duk da amfanin Ambar kuma zai iya cutarwa .

1- Mata masu ciki su guji amfani da Ambar, musamman wajen sha a ciki.

2- Ambar din da ba a gauraya shi da wani abu ba kamar ruwa da makamantansu, to a guji shan sa kai tsaye.

3- Ba'a sa Ambar a cikin ido.

4- A guji ajjiye shi kusa da yara, saboda zai iya ɓarkar da gudawa idan aka sha.

Daga shafin Bashir Halilu.

Post a Comment

0 Comments