MAGANIN SHANYEWAR BARIN JIKI (PARALYSIS)
Ga wanda yake fama da mutuwar 6arin jiki ko shanyewar jiki gaba daya, sai a jarraba daya daga cikin wadannan hanyoyi
1) Mara lafiyar ya yawaita shan nonon Rakumi kuma a narka 6argon Saniya arika sanya masa acikin abincinsa yana ci da shi kuma ana shafa masa adukkan gabobin da suka shanye din.
Wannan fa'idar tana da muhimmanci hatta ga kananan yara wadanda wani 'bangaren jikinsu ya shanye, ko kuma jikinsu babu karfi.
2) Asamu kwanduwar kwan Tantabara (Wato yellow din cikin ruwan kwan), a hada da ruwan albasa, da tafarnuwa, a gauraya, arika shan cokali biyu safe da dare. Amma idan karamin yaro ne arika bashi cokali daya tak.
Kuma arika shafa man Jimina ajikin kafa ko hannun da yake ciwon.
Masu fama da shanyewar gabobi, ko kuma rashin karfin jiki in sha Allahu zasu samu waraka.
3) A samu 'bargon kafar rakumi (wato na wajen kwaurinsa) a narkar da shi sannan a gauraya shi da Man habbatus Sauda mai kyau, a rika shafa wa mara lafiyar a jikin kafadunsa da kuma kashin bayansa, da kuma gabobin da suke ciwon. In sha Allahu Za'a ga abun mamaki wajen samun waraka da izinin Allah.
4) A rika dafa tafarnuwa, ana baiwa mara lafiyar ruwanta yana sha tare da zuma kuma ana ba shi man tafarnuwa wanda aka hada da bargon saniya. Amma idan za'a narkar da 'bargon ba soya shi za'ayi ba, a rana za a sanya shi har sai ya narke da kansa. Wannan faida tana da kyau sosai.
Daga cibiyar Daga shafin Bashir Halilu.
0 Comments