Domin magance wasu matsalolin lafiyar da yawa waɗanda wasu lokutan suke da wahalar warkewa da magunguna.


Domin magance wasu matsalolin lafiyar da yawa waɗanda wasu lokutan suke da wahalar warkewa da magunguna.

Hadin zuma da Girfa wato cinnamon na daya daga cikin hadin magani mai banmamaki da ake amfani dashi don warkar da cututtuka da dama da matsalolin lafiya.

Zuma tana da wadatar vitamin (A, B1, B2, B3 ,B5, B6, B8, B9, C, D da kuma K).

Sannan kuma tana dauke da ma'adanai masu yawa irin su (iron, copper, Sodium, potassium, zinc, calcium da phosphorus).

Bugu da ƙari tana dauke da protein, carbohydrates, antibiotics na dabi'a, antioxidant, sannan kuma tana bada kariya daga afkuwar wasu cututtukan da dawa.

Cinnamon tana taimakawa wajen karfafa garkuwar jiki, tana aiki a matsayin anti-inflammatory, antioxidant, antibacterial da kuma antifungal, tana bada kariya daga cututtukan zuciya da jijiyoyin jini, Girfa tana aiki don magance gajiya da damuwa, tana inganta lafiyar ƙwaƙwalwa sannan kuma tana daidaita tsarin narkewar abinci, tana yakar cholesterol da ciwon sukari wato diebetes. 

Wasu daga cikin cututtukan da hadin girfa da zuma ke warkarwa da yadda za'ayi amfani dasu.

Cututtukan zuciya:

Ana hada zuma cokali biyu da garin Girfa cokali guda, wannan hadin yana kara inganta zagayawar jini da bada kariya daga toshewar hanyoyin jini.

Maganin cutar arthritis:

A cikin kofi mai dauke da ruwan dumi, ana zuba zuma cokali biyu da cokali daya na garin Girfa. A gauraya shi da kyau sannan a sha wannan hadin sau biyu a rana, safe da yamma.

Kawar da cututtukan Infections:

Domin kawar da cututtuka da kwayoyin cutar bacteria ke yadawa, a hada cokali guda na zuma da teaspoon na garin girfa a ruwan dumi a sha bayan cin kowanne abinci.

Domin magance cholesterol:

Ana zuba cokali guda na Girfa a cikin kofin shayi, sannan kuna iya kara masa zaki da zuma kadan

Magance Radadi;

Ana hada babban cokali na zuma da babban cokali na garin girfa don kawar da ciwon hakori, ciwon ciki, zafin al'ada dama duka sauran radadin da za'a iya samu a cikin jiki.
 
Karfafa garkuwar jiki:

Ana hada garin girfa cokali guda da zuma, ana shan wannan hadin kullum domin karfafa garkuwar jiki.

ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA. 

✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam

Post a Comment

0 Comments