AMFANIN CARDAMOM GA MAZA.


AMFANIN CARDAMOM GA MAZA. 

Cardamom yana dauke da anti-inflammatory Properties da antioxidants wadanda suke taimaka masa wajen sa shi ya zamto mafita mai kyau ga wasu matsalolin kiwon lafiya na yau da kullum musamman ga maza.

Muhimman fa'idodin cardamom ga maza sun haɗa da:

■ KARA KARFIN SHA'AWAR JIMA'I 

Cardamom an san shi sosai wajen inganta lafiyar jima'i, kuma yana iya kara karfin sha'awar jima'i, musamman ma a cikin maza, kuma yana iya zama maganin da za'a yi amfani dashi na dabi'a madadin amfani da Viagra, kamar yadda aka gano cewa cardamom yana aiki a matsayin maganin dake kara karfi maza, wanda ke da tasiri sosai ga lafiya.

Haka nan kuma cin ya'yan cardamom ko shafa man cardamom a jikin al'aura Yana iya kara yawan kwaranyar jini da zagayawar sa, ta yadda zai bada dama wajen kara maka karfin sha'awa.

Haka kuma kasancewar shi cardamom yana ɗauke da protein Compounds masu yawa, kamar su arginine, su waɗannan sinadarai suna taimakawa wajen ƙara 
yawan kuzarin da ake buƙata a lokacin jima'i.

Sannan kuma, ya kamata a lura cewa damuwa tana ba da gudummawa sosai wajen rashin daidaituwar hormonal wato (hormonal imbalance), wanda hakan yana daya daga cikin muhimman abubuwan da ke haifar da raguwar sha'awar jima'i, kuma cardamom an san shi yana taimakawa wajen rage damuwa da kuma taimakawa wajen samun ingantacciyar nutsuwa, wanda hakan zai iya inganta al'amuran da suka shafi jima'i da kara yawan sha'awar jima'i.

■ MAGANCE RAUNIN AL'AURA 

Kafin gaban dan Adam ya tashi ya samu karfi ta hanyar dabi'a, tilas ne hanyoyin jinin da ke cikin al'aurar namiji su kasance sun bude ta yadda jini zai iya gudana a cikin su cikin sauri, wanda hakan kan taimakawa al'aura ta samu karfi. 

Rashin karfin mazakuta yana nufin cewa wadannan hanyoyin ba sa aiki yadda ya kamata ko kuma yadda ake bukata.

Wasu daga cikin tsirrai, irin su cardamom, suna taimakawa wajen magance raunin mazakuta ta hanyar dabi'a, ta hanyar daidaita fitar hormones din jikin namiji, tsarin jijiyoyin jini, da sarrafa pressure din jini.

Hakan yana faru ne sakamakon cewa shi cardamom yana dauke da antioxidants da kuma compound irin su cineole, wanda ke da tasiri wajen kara yawan sha'awar jima'i da kuma taimakawa wajen magance matsalar rashin karfin mazakuta.

Wasu daga cikin minerals, kamar iron da ake samu a cikin cardamom, suma suna taimakawa wajen kara yawan zagayawa jini zuwa ga al'aurar namiji, wanda hakan ke kara karfin mazakuta, kuma hakan na iya taimakawa matuka wajen inganta ayyukan jima'i.

■ INGANTA FERTILITY. 

Cin cardamom na taimakawa sosai wajen ƙara yawan samar da ruwan maniyyi mai inganci, ƙara haɓakarsu da harbawar su, wanda hakan zai iya taimakawa wajen inganta fertility. 

Hakan na faruwa ne sakamako cardamom yana da wadata a cikin magnesium, zinc, da compound irin su polyphenols.

Sannan kuma Cardamom yana ba da karin wasu gudummawar wasu fa'idodin masu yawa don inganta fertility a cikin maza da mata baki daya, wadanda suka hada da: 

● Samun ingantaccen ruwan maniyyi da kara yawan sa.

● Ƙarfafa zagayowar jini musamman a bangaren ƙashin ƙugu.

● Ƙara karfin sha'awar jima'i.

● Taimakawa wajen daidaita hormones.

● Ƙarfafa garkuwar jiki.

● Rage damuwa da kunci.

■ HANYOYIN DA AKE AMFANI DA CARDAMOM. 

Cardamom za a iya amfani da shi ta hanyoyi fiye da ɗaya don samun fa'idodin cardamom ga maza.

Tsiro ne mai amfani da yawa, domin ana iya amfani da shi ta hanyar ci kai tsaye don samun amfanin sa.
Hakanan za'a iya amfani dashi a matsayin sinadarin dandanon girki na dabi'a da ake ƙarawa a abinci da kayan shaye-shaye daban-daban.
Ana iya amfani da tsabar ya'yan sa, ko kuma busassun cardamom, ko a nika shi ayi amfani da garin sa.

Ana iya hada garin cardamom da abubuwan sha da muke sha na yau da kullum, kamar shayi, coffee, ko madara.

Hakanan kuma ana iya ƙara shi a nau'ika daban-daban na abinci na yau da kullun don samun fa'idodinsa.

Cardamom na daya daga cikin shahararrun tsirrai da ake amfani da su a gidajen dake fadin kasashen Larabawa, sun kasance suna amfani da shi wajen shirya girkin abinci da abubuwan sha daban-daban, domin yana da dandano na musamman da karfi wanda ke ba abinci da abin sha dandano na musamman.

Amma amfani da cardamom bai tsaya ga lafiyar maza kawai, haka nan kuma ana yin amfani dashi sosai domin yana da fa'idodi masu yawa na kiwon lafiya, kamar inganta lafiyar tsarin narkewa abinci, lafiyar hanta, lafiyar baki, daidaita hawan jini, bada kariya daga cutar daji, da sauran fa'idodi masu yawa.


ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA. 

✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam

Post a Comment

0 Comments