Rashin sha’awar iyali da dalilansu (2)



Rashin sha’awar iyali da dalilansu (2)


Daga BILKISU YUSUF ALI

Ci gaba daga makon da ya gabata

A makon da ya gabata muna magana kan abubuwan da ke hana sha’awar maigida ga iyalinsa alhalin a farkon auren ba haka ba ne. Maza da mata kan ɗora laifin ga abokin zama da hujja me rauni ta zargi da hasaahe maras tabbas ko kuma tunanin wata jinya ta musamman. A makon jiya mun tsaya kan abin da ya shafi maza inda yau za mu ɗora da ɓangaren mata.

Mata su ma suna fuskantar irin wannan matsalar wanda kafin a yi tunanin wata larura ya kamata a fara tabbatar da ba ɗaya daga cikin wa]annan dalilan.

Soyayya don Allah:

Duk lokacin da mace ta auri namiji, amma ba don tana sonsa ba sawa’un ko dai auren dole ko kuma don wani abu da ta hanga ta aure shi don shi, to da matsala. Don kuwa sha’awa ko gamsuwa yayin aure yana tafiya kafaɗa da kafaɗa ne da soyayya. Don haka in har abin da ake nema ba a samu ba na abin duniya ko wani muƙami zuciya za ta kasance da damuwar da za ta rusa duk wani jin dadi na zamantakewar aure. Haka idan aure ne na dole shi ma zai zama ba wani doki ko mararin juna yayin da aka haɗu. Haka idan ma abin da ake nema na abin duniyar ya samu nan ma ƙin ne zai biyo baya, don a lokacin buƙatar shi ne kowa ya kama gabansa da ma buƙatar maje hajji sallah. Ga irin wannan matsalar duk magani ko dabaru ba za su yi aiki ba, saboda sakon farko da ke zuwa ƙwaƙwalwa soyaya ne.

Zafin kishi:

Mata da ke da zafin kishi ba sa lura kishin nan matsala ce da ke hana su dukkan wata walwala bi hasali ma sukan dora larurar ga abokiyar zama ko abokan zama da tunanin ita ta yi asiri ta hana sha’awar ko ta yi auri mijin ya daina son ta ko ranar girkinta ba zai shigo da wuri ba ko idan ya kusance ta ba ta da ni’ima da dai sauran ƙorafe-ƙorafen da mata kan yi musamman waɗanda ke da abokan zama, wanda da dama matsalar ba haka ta ke ba. Abin da mace ta sa ma zuciyarta na kishi da raahin kwanciyar hankali shi ne yake dawo mata har ya shafi zamantakewar aurenta. Idan har zuciya babu nutsuwa babu abin da za a samu na sha’awa. Kullum mace na ganin bakin mijinta da laifinsa ƙwaƙwalwa da zuciya ba za su bar wani sukunin jin daɗi ba.

Zargi:

Duk lokacin da zargi ya ratsa tsakanin miji da mata ko dai mijin na zargin matar da wasu laifuka na cin amana ko zalunci ko ita matar na zargin sa da cin amana ko zalunci to kuwa da wuya a samu abin da ake buƙata na zamantakewar aure. Mace kan hana kan ta sukunin lallai mijinta yana da wata mu’amala da wata ko wasu a waje, don haka za ta shiga fargaba da kishi wata har da ƙyama wanda in har ta dasa hakan a zuciyarta. Kuma ta bari mijin ya san da hakan to daga ita har mijin sun bar jin da]in mu’amalar aure da juna kenan, don kowa na jin haushin kowa.

Ƙazanta:

Kowacce mace tana buƙatar tsafta ba wai ita kadai ce ake so kullum a sa ta yi ta tsafta ba.Don haka ƙazamin namiji kan hana matarsa sha’awar sa da gamsuwa da shi yayin kusantar juna. Don haka ƙazanta kan damu da mata su kasa gamsuwa da abokin zama.

Fargaba da rashin kwanciyar hankali
Zaman aure zama ne na lumana da fahimtar juna da kwanciyar idan har namiji zai zama mafaɗaci da rigimar ba gaira ba dalili da fuskar shanu da firgita abokiyar zama ba yadda za ta samu nutsuwar sha’awarsa ko ni’ima ko gamsuwa.

Cin abinci mai kyau:

Duk wani magani da za a ce mace ta sha, don samun ni’ima ko gamsar da abokin zama bayan abinci ne mai kyau da gina jiki. Idan har mace ba ta da ci ma mai kyau ba yadda za a yi ta gamsar da mijinta haka ita ma ba za ta gamsu ba ba ma za ta samu sha’awar ba. Don haka kafin mace ta fara tunanin shaye-shayen magani yana da kyau ta fara kulawa da abin da ta ke ci son shi ne magani na farko.

Cushen magunguna:

Cushe-cushen magunguna kuma marasa inganci da tsafta shi ma yana haifar da rashin sha’awa musamman yawan amfani da sabulai barkatai waɗanda aka yi su da sinadarai wanda ba ma asan waɗanne iri ba ne. Idan har mace za ta ke irin wannan kimshe-kimshen, to a ƙarshe kuwa za ta yi abin da ake kira “garin neman gira an raaa ido”, don kuwa irin wannan kan haifar da ɗaukewar ni’ima da ma ɗaukewar sha’awar gabaki ɗaya.

Shekaru:

Akwai shekaru da idan mace ta kai, wannan shekarun sha’awarta kan ragu. Haka yanayin yadda za ta gamsar da abokin zamanta shi ma ba zai kasance kamar yadda za ta yi a lokacin da take da ƙananan shekaru ba.

Gabatar da wasanni kafin kwanciyar aure:

Sau da dama matsalar da mata kan fuskanta ta rashin samun ni’ima ko sha’awa karancin wasanni ne da akan gabatar kafin a kusanci juna, wanda wannan yana taimakawa kwarai wajen gamsuwar iyali.

Idan har mace tana ɗauke da wasu ko ɗaya gada cikin wa]annan abin da aka lissafa to zai yi wahala a samu gamsuwa ko sha’awa yayin kusantar juna.

Post a Comment

0 Comments