MUTUMIN DAKE FAMA DA CIWON KODA.
Da zai samu
1. SHAMMAR (FENNEL SEED)
2. YANSUN (ANISE SEED)
3. SI'ITIR (THYME)
Guda ukun nan sannan nune, babu wani abu baƙo wanda idan akaje gurin masu magani ko masu sayar da spices baza'a same shiba.
Ana haɗasu da qaro, sai a niƙa qaron yayi gari.
Ana iya hadasu ma duka a nike su.
Idan aka nike su, yadda za'a dinga amfani dasu shine, za'a iya dinga zuba su a cikin ruwan shayi ko kuma a siyo ruwan roba babba, sai a ɗebi table spoon guda biyu a zuba.
Masu tsakuwar koda idan sukayi wannan da yardar Allah yakan narkar da tsakuwar.
Kuma yazama cewa an samu lafiya a cikin jiki kuma a kuɓuta daga cutarwa na shi wannan tsakuwar dake cikin kodar.
Allah ya bawa duk wasu marasa lafiya lafiya.
✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam
0 Comments