AMFANIN ZUMA GA MASU FAMA DA GYAMBON CIKI (Stomach Ulcer).



AMFANIN ZUMA GA MASU FAMA DA GYAMBON CIKI (Stomach Ulcer).

Ruwan zuma yana ƙunshe da kaso mai yawa na rukunin element da antioxidants waɗanda ke taimakawa wajen kawar da ƙwayoyin cutar bacteria.

mafi shahara daga cikinsu sune:

■ Organic acid.
■ Protein. 
■ Amino acid.
■ Vitamins.
■ Enzymes.
■ Metals.
■ Antioxidants.

Ana ɗaukar polyphenols ɗaya daga cikin fitattun antioxidants da ake samu a cikin zuma, sannan kuma tana dauke da kaso mai yawa na wannan sinadarin. 

Polyphenols na iya taimakawa wajen hana ci gaban kwayoyin cutar Helicobacter pylori bacteria, wanda ake ganin suna daya daga cikin abubuwan da ke haifar da ciwon gyambon ciki, don haka za a iya magance shi da zuma.

YADDA AKE AMFANI DA ZUMA DON MAGANCE GYAMBON CIKI. 

Zaka iya shan cokali guda na zuma farar saƙa, Idan kuma baka son ka sha cokali daya na zuma kai tsaye, za ka iya zubawa a kofin guda na ruwa ko kuma wani abin sha mai dumi tare da zuma farar saka cokali daya a kullum.

Hakanan zaka iya magance gyambon ciki da zuma ta hanyar hada ta da wadannan tsirrai na dabi'a. 

■ Habbatus sauda: Maganin gyambon ciki za'a iya inganta shi da zuma da habbatus sauda, saboda suna da antibacterial properties kuma suna iya taimakawa wajen kawar da gyambon ciki.

■ Bawon ruman (pomegranates): Bawon ruman yana kunshe da sinadarin tannin da ke taka rawa wajen bada kariya daga ciwon gyambon ciki, saboda haka za'a iya hada zuma da bawon ruman don magance cutar gyambon ciki. 

■ Citta: Citta na iya zama daya daga cikin tsirrai masu amfani ga ulcer saboda tasirinta na magance matsalolin ciki, ciki har da ulcers.

Ana magance gyambon ciki da zuma da citta ta hanyar yin shayin citta a zuba cokali guda na zuma aciki

Citta bata saurin taimakawa wajen magance gyambon ciki da sauri, amma tana iya taimakawa wajen hana sake dawowar sa.

Baya ga maganin gyambon ciki da zuma, ana iya amfani da wasu tsirrai da ke taimakawa wajen rage bayyanar cututtukan musamman :

■ Tafarnuwa: Tafarnuwa na iya taimakawa wajen hana girma na Helicobacter pylori, don haka ana iya amfani da ita wajen magance gyambon ciki. 

■ Kurkum (Turmeric): Turmeric yana dauke da wani Compound wanda ake kira curcumin, wanda yake aiki a matsayin anti-inflammatory da antioxidant, kuma yana iya taimakawa wajen bada kari daga gyambon ciki dakuma saukaka alamomin ta.

■ Babunaj (Chamomile): Ana amfani da babunaj don sauƙaƙawa yanayin rashin lafiya da dawa, kamar cututtukan numfashi, kumburin hanji, da Infections. 

Hakanan kuma za'a iya amfani da ruwan babunaj don magance gyambon ciki saboda yana dauke da anti-ulcer properties. 

■ Green tea: Greean tea na iya taimakawa wajen warkar da gyambon ciki da kuma magance wasu matsalolin ciki kamar gudawa idan aka sha shi matsakaici, amma ana ba da shawarar kada a sha shi fiye da kima don kada ya ta'azzara matsalar.

Za a iya zuba masa zuma cokali daya maimakon sukari domin samun karin faida

Baya ga maganin gyambon ciki da zuma da tsirrai, za a iya amfani da abinci mai dauke da sinadarin probiotics, wadanda kwayoyin bacteria ne masu amfani da ke da muhimmanci ga lafiyar tsarin narkewar abinci.
Hakanan za su iya taimakawa wajen kawar da kwayoyin cutar Helicobacter pylori bacteria da ke haifar da gyambon ciki da kuma inganta warkarwa daga gare su. 

Ana samun probiotics a cikin rukuni na abinci kamar

■Garri
■Yogurt 
■Nonon Akuya
■Daddawa
■Aya
■Kunu
■Amala. Da sauransu.

ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA. 

✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam

Post a Comment

0 Comments