AMFANIN SANA_MAKIY WAJEN KARA LAFIYA.



AMFANIN SANA_MAKIY WAJEN KARA LAFIYA. 

Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce

 "Da za a samu abinda zai yi maganin mutuwa to da Sana(makiy) ce"

قال رسول الله صلى الله عليه وسلم
لوكان في شيء شفاء من الموت لكان في السنا.

Manzon Allah صلى الله عليه وسلم 
ya ce "Da za a samu wani abu wanda maganin mutuwa yake a cikinsa to da acikin Sana(makiy) za a samu"

   Likitoci Larabawa su ne suka fara amfani da Sana Makiy a matsayin magani tun shekaru dari tara bayan aiko Annabi Isa عليه السلام.

   Haka ma mutanen Europe sun dade suna amfani da ita ta fuskar magani.

   Ga wasu daga cikin Amfanin Sana_Makiy ga lafiyar al'uma. 

1-Gyran fata. Mai, wanda yake jikin ganyen Sana Makiy yana dauke da sinadaran da ke gyara fata da kuma maganin cututtukanta. Kamar kuraje da Makero da dai sauransu. Tana kuma maganin ciwo ko qonewa.
Sai a hada garin Sana Makiy da garin Habbatussauda da Farar wuta, a kwa6a da Man kadanya a dinga shafawa.

2-Kara hasken Hakora. Goge hakori da ciyawar Sana Makiy na kara masa haske da sheqi. Ana kuma iya zuba garin Sana Makiy a cikin totuwar Ayaba a hada da ganyen Na'ana'a a goge hakora don kara musu haske da sheqi.

3-Kara yawan gashi da sa shi baqi da kuma hana shi karyewa.
Ana iya kwa6a Sana Makiy a cikin Man Kwakwa domin kara yawan gashi da kyawunsa.

4-Rage qiba da te6a. Shan rabin cokali na garin Sana Makiya a kullum yana saurin rage kiba da tumbi.

5-Sana Makiy tana maganin wasu-wasi wanda ya takurawa mutum. Ana hada ta da Na'ana'a da Ray'han, a dafa a zuba zuma ana sha kullum cokali daya.

6-Tana fitar da guba da mutum ya ci ko ya sha a cikinsa.

7- Tana taimakawa wajen yin bayan gida ga wanda ya kasa ko yake ba shi wahala.

8- Sana Makiy tana maganin Basir sosai da sosai.

9-Tana Maganin karancin jini a jikin mutum.

10-Tana tsaftace hanyoyin fitsari kuma tana taimakawa wajen yin sa cikin sauqi.

11-Tana karfafa zuciya kuma tana taimaka mata wajen yin aiki.

12- Tana Maganin Aljanu idan an hada ta da zuma ana sha.

13- Tana maganin ciwon suga. A hada Sana Makiy da 6awon kwakwa a jiqa a ruwa. Sai a dinga sha.

14- Yawan mantuwa. Sai a yi shayi da Sana Makiy da garin Ray'han a zuba zuma.

15- Ciwon ciki. A gauraya Sana Makiy da garin Rawaya, ya zamto yawansu duka daya ne.
Sai a jiqa a dinga sha.

16- Shan garin SanaMakiy yana maganin Tsutsar ciki.

17- Tana maganin Majina.

17-Tana maganin Farfadiya.

18- Sana Makiy na maganin Ciwon jiki idan ana sha da ruwan dumi.

AMMA A KULA.

Duk da amfani da SanaMakiy take da shi, yin amfani da ita ba bisa ka'ida ba yana iya cutar da mutum.

1- Mai ciki kasa da wata hudu kada ta sha Sana Makiy.

2- Kada a baiwa yaro dan kasa da shekara shida.

3- Shan Sana Makiy da yawa zai sa mutum gudawa.

4- Idan mutum ya fara shan SanaMakiy fitsarinsa yana canja kala amma daga baya yana dawowa daidai.

5- Kada mutum ya yawaita amfani da SanaMakiy kowane lokaci.

Idan kuna bukatar sanin amfanin wani magani ko wani abinci ko yadda ake sarrafa wani magani sai ku rubuta a wajen comment, insha Allah za mu kawo muku. 

Daga shafin Bashir Halilu. 

Post a Comment

0 Comments