MAGANIN KARANCIN KWAYOYIN MANIYYI (LOW SPERM COUNT)
Low sperm count yana nufin cewa ruwan maniyyi da kake fitar da shi yayin inzali yana ƙunshe da mafi ƙaranci na maniyyi fiye da na al'ada.
Ana la'akari da cewa adadin fitar maniyyin ku yayi ƙasa da na al'ada idan kuna fitar da ƙasa da miliyan 25 na kwayoyi maniyyi (sperm cell).
Samun karancin adadin ruwan maniyyi yana rage damar maniyyi wajen kyankyasar kwan abokiyar tarayya don haifar da ciki.
SABUBBAN DAKE KAWO KARANCIN RUWAN MANIYYI
> Kamuwa da cutar infection
> Yawan sukari
> Damuwa
> Cin abinci mara kyau
> Shan kofi
>Yawan zafi ga ya'yan maraina
> Lalacewar chromosomes
> Amfani da kwayoyi
> Yawan shan barasa
MAGANI
Mutumin dake fama da wannan matsalar ana so ya samo;
> Ganyen Guava
> Karas
> Citta
> Bawon Kankana
> Zuma
Zaka hada karas, citta da bawon kankana ka markada su a gefe daban.
Sai ka tafasa ganyen Guava na tsawon minti 30, sai ka zuba ruwan a cikin markadadden karas, citta da bawon kankana, sai ka zuba rabin kwalbar zuma.
Ana sha rabin kofi sau biyu a kullum tsawon wata daya (kwana 30)
Yawan maniyyin ku zai ƙaru sosai da izinin Allah.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.
✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam
0 Comments