AMFANIN DADDAWA WAJEN ƘARAWA MUTANE LAFIYA.
Asalin Daddawa ana samar da ita ne daga ƙwallon ƴaƴan bishiyar ɗorawa, wand ake kira da Kalwa. Kalwa wani abu ne da ake sarrafawa domin samar da daddawa, wadda yawancin al'umomin Najeriya da yankin Afirka ta Yamma ke amfani da ita domin kara wa abinci ɗanɗano.
Kalwa ce babban abin da ake sarrafawa wajen yin daddawa. Ma'aikatan lafiya sun ce tana da amfani mai yawa ga rayuwar ɗan Adam.
A taƙaice, kalwa na ɗauke da sinadari mai tasiri ga jikin dan Adam, musamman a ɓangarorin da suka shafi jini.
Amfanin Daddawa.
1 - Daddawa tana taimakawa wajen al'amarin da ya shafi iyali.
Kalwa wadda ake amfani da ita wajen haɗa daddawa na kunshe da sinadarin zinc, wanda kamar yadda bincike ya nuna yana kara mizanin kwayoyin halittta na testosterone, wanda ya fi yawa a jikin maza.
Har wa yau, bincike ya nuna cewa tana da sinadarin mineral, wanda ke kara ingancin kuzari da inganta rayuwar jima'i.
Wani dalili na sa Daddawa cikin abinci shi ne tana bunkasa kwayoyin halitta waɗanda suke jikin mutum, saboda ta kunshi sinadarin zinc, wanda shi ma yake taimakawa wajen kare mutum daga kamuwa daga wasu cututtuka.
2 - Daddawa tna taimaka wa lafiyar idanu.
Kalwa ta kunshi sinadarin gina jiki na Vitamin A wanda kuma yake taimaka wa idanu da kuma hana kamuwa da cutar makanta.
Tana yin hakan ne ta hanyar samar wa wani bangare na ido da ake kira 'cornea' kwayoyin halitta na antiodidants waɗanda suke taimakawa wajen hana kamuwa da matsalolin da kan shafi idanu.
3 - Daddawa tana ƙara nagartar kasusuwa da lafiyar haƙora.
Kalwa har ila yau ta kunshi sinadarin calcium wanda shima yana taimakawa wajen samar da nagartattun kasusuwa, hakan ma yana taimakawa wajen lafiya da kuma ingancin hakora.
4 - Dadda na sauƙaƙa narkar da abinci da kuma amfaninsa.
Sinadaran Lipids wanda ke cikin jiki na taimakawa matuka wajen narkar da abinci kamar yadda ya kamata da kuma wasu abubuwan da ya kunsa.
Sinadaran lipids ana samun su cikin kalwa, ana kuma bukatarsu ne saboda daukar dawainiyar nau'in abinci mai wuyar narkewa, ya mayar da shi wanda zai iya narkewa, domin samar da sauran sinadarai da jiki ke buƙata na bitamins A, D, E, K daga cikin kanana da manyan hanji, har zuwa inda jini yake.
5 - Daddawa na samarwa mutum tsokar jiki mai lafiya.
Kalwa ta kunshi sinadarin abinci na 'protein', wanda yake aiki mai muhimmanci wajen gina ƙasusuwa, da tsokar naman jiki, da jijiya, da kuma jini.
Jikin mutum yana amfani da sinadari na protein ne saboda ya ginu da kuma yin wasu gyare-gyare na wasu kananan kwayoyin halitta na jikin mutum.
Sinadarin protein na amfani wajen samar da ƙwayoyin halitta na enzymes, wadanda ke cikin baki kuma suke taimakawa wajen daddatsa abinci ko kuma rage masa girma saboda ya samu narkewa domin yin aikin da ya kamata a jikin mutum.
6 - Daddawa na taimakawa wajen ciwon sikari da kuma daidaita cholesterol.
Bincike ya nuna ita Kalwa ta kunshi fibre wadda kuma ana iya narkar da ita, tana taimakawa wajen lura da yadda, mizanin sikari yake, da kuma rage yawan mizanin cholesterol. Don haka wadanda suke fama da cutar sikari, ya kamata su rika amfani da Daddawa a cikin abincin su.
7 - Rage hawan jini.
Haka nan, daddawa na taimaka wa wajen rage hauhawar jini da kuma rage haɗarin kamuwa da shanyewar ɓarin jiki, wato stroke a Turance.
8 - Maganin gudawa.
Masana harkar lafiya na cewa daddawa na ƙunshe da sinadarin tannins da ake samu a ganyayyaki da abinci da dama.
Duk abincin da ke ɗauke da sinadarin tannins mai yawa, akan umarci mai fama da gudawa ya ci domin rage yawan fitar ruwa a jikinsa.
9 - Tana gina ƙwaƙwalwar jarirai.
Amfani da daddawa na taimaka wa wajen hana zurarewar sinadaran folic acid da ke samar da neural tube, waɗanda su ne ke haɓaka ƙwaƙwalwar jariran da ba a haifa ba tukunna.
Wannan dalili ya sa masana harkokin lafiya ke son masu ciki su dinga amfani da ita daidai gwargwado.
SHAWARA.
★ Ya kamata a wajen baki, a goge shi da abun goge baki bayan an ci daddawa.
★ Haka ma ya kamata a wanke hannu da sabulu ko omo bayan an ci abinci da daddawa.
Daga shafin Bashir Halilu
0 Comments