Cinnamon yana ƙunshe da nau'ikan magunguna daban-daban waɗanda za su iya amfanar da waɗanda ke da rashin lafiya kamar su ciwon sukari da cututtukan zuciya.
Yana ƙunshe da Antioxidant da Anti-inflammatory Compounds
Amfanin cinnamon na kiwon lafiya, yana da alaƙa da yawa yawan sinadaran kariya na tsirrai, kamar su coumarin, cinnamic acid, eugenol, da cinnamaldehyde.
waɗannan abubuwan an san su suna da ƙarfi wajen anti-inflammatory, antioxidant, da anti-diabetic Properties.
Polyphenolic Properties da ake samu a cikin cinnamon, irin su cinnamaldehyde, na iya taimakawa wajen rage kumburi a cikin jiki ta hanyar tsarin daidaita sunadaran protein masu kawo kumburi.
Saboda yawan tasirin sa na sinadarin anti-inflammatory da antioxidant, cinnamon na iya amfanar waɗanda ke da cututtukan kumburi kamar rheumatoid arthritis.
Wani ƙaramin binciken da ya haɗar da mata 36 masu rheumatoid arthritis. An samu mahalarta waɗanda sukayi amfani da supplement na cinnamon gram 2 a kowace rana na tsawon makonni takwas sun sami raguwa mai yawa a cikin matakin alamun kumburi.
Cinnamon na iya amfanar lafiyar zuciya gaba ɗaya ta hanyar haɓaka hauhawar jini da zagayawar sa, da rage matakan kitsen jini, kamar LDL cholesterol.
Samun hawan jini da yawan matakin kitse a jini na iya ƙara haɗarin cututtukan zuciya, don haka shan supplement na cinnamon na iya taimakawa wajen rage haɗarin cututtukan zuciya.
Buncike ya nuna sinadaran da ake samu a cikin cinnamon, irin su cinnamaldehyde, suna da vasorelaxant Properties, ma'ana yana taimakawa jijiyoyin jini su huta. Wannan zai iya taimakawa wajen inganta hauhawar jini da zagayawar sa a cikin jiki.
Cinnamaldehyde kuma na iya hana sakin calcium, wanda shine minerals da ake buƙata don vasoconstriction, ko tsuke jijiyoyin jini.
A wani bincike na mutane 40 masu fama da hawan jini anyi amfani da 1500 milligrams (mg) na cinnamon a kowace rana har tsawon watanni uku .
ya haifar da raguwa mai yawa na wannan hawan jini.
Cinnamon na iya taimakawa waje rage ƙwayar cholesterol da fatty acid a cikin hanji, wanda zai iya taimakawa wajen rage matakin kitse na jini.
Haka kum cinnamon da alama yana rage yawan ƙwayar cholesterol a cikin jiki.
Cinnamon na iya zama mai amfani ga mutanen da ke da hawan sukari na jini, gami da masu ciwon sukari na 2 (type 2 diebetes).
Bincike ya nuna cinnamon na iya taimakawa wajen rage sukarin jini ta hanyar rage saurin sakin glucose a cikin jini.
Wani binciken da ya haɗa da mutane 40 ya nuna mahalarta waɗanda sukayi amfani da tsakanin gram uku zuwa shida na cinnamon kowace rana tsawon kwanaki 40 sun sami raguwar kaso mai yawa a cikin matakan sukari na jini.
Yadda ake amfani da Cinnamon
Ana iya amfani da cinnamon a matsayin spices a kayan abinci ko a matsayin supplement.
Hanya mai sauƙi don amfani da cinnamon ita ce amfani da ita a matsayin spices a cikin abinci.
Kamar abubuwan ciye-ciye, da abubuwan sha. Hakanan ana iya ƙara kirfa a cikin miya don ƙara mata ɗanɗano.
Adadin daya kamata ayi amfani dashi
Yawan adadin cinnamon da aka saba amfani dashi a cikin abinci gabaɗaya ana ɗaukar sa daidai.
Bincike ya nuna cewa amfani da cinnamon gram ɗaya zuwa biyu a kowace rana har zuwa watanni uku.
Yayin amfani da ita a ɓangare na abinci na yau da kullun, cinnamon yana da lafiya kuma baya da wani side effects.
Duk da haka, kamar yawancin spices da supplement, shan cinnamon adadi mai yawa na iya haifar da illa.
Cinnamon na dauke da sinadari mai yawa da ake kira coumarin, wanda zai iya zama mai guba ga hanta kuma yana haifar da hadarin lafiya idan aka sha shi akai-akai.
Supplement na cinnamon da ke ɗauke da cinnamon mai yawa na iya zama barazana ga lafiyar mutanen da ke da juna biyu ko masu shayarwa.
teaspoon daya na cinnamon na ƙunshe da 7mg zuwa 18mg na coumarin. Ka'idar sha na yau da kullun na coumarin shine 0.1mg na kowace kilogiram a kowace rana, wanda yayi daidai da 17mg ga mutum mai nauyin kilo 150.
Shan fiye da 50g na coumarin kullum zai iya haifar da hepatotoxicity, ko rauni ga hanta.
Idan ka sha cinnamon da yawa, za ka iya samun yawan gumi, yawan bugun numfashi, da bugun zuciya da sauri.
Ku Tuntubi likitanku nan da nan idan kun sami waɗannan alamun bayan shan supplement na cinnamon.
Side Effects na Cinnamon
shan cinnamon gami da supplement na cinnamon mai yawan gaske, na iya haifar da illoli kamar haka:
• Ciwon kai
• Ciwon zuciya
• Kumburi
• Rashin jin daɗin ciki
• Tashin zuciya
• Gudawa
Idan kuka fuskanci wani side effects, hadi da ɗaya ko fiye na alamun da aka jera a sama, bayan shan supplement na cinnamon a dakatar da amfani dashi, sannan kuma a tuntubi likita.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.
✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam
0 Comments