Amfanin Shammar (Fennel seed)
Shammar yana da abubuwan gina jiki masu kariya ga lafiya kuma yana iya inganta lafiyar fata, ƙasusuwa, tsarin narkewar abinci, da sauran su.
A wani nazari da akayi akan Shammar ya nuna cewa Shammar yana ƙunshe da antioxidant, antimicrobial, antiviral, anti-fungal, da anti-inflammatory Compounds.
Ba abin mamaki ba ne ba, don saboda an dade ana amfani da Shammar a matsayin tsiro na magani don magance batutuwa masu yawa da suka shafi narkewar abinci, endocrin, haihuwa, da tsarin numfashi da kuma karin ruwan nono ga iyaye masu shayarwa.
Yana Magance Alamomin daukewar al'ada (Menopause)
Ga mutanen da ke cikin halin daukewar al'ada, amfanin shammar ga lafiyar su yana da alaƙa da man sa.
A shekarar 2019 Wata takarda ta yi bitar ingantattun tasirin mai na Shammar wajen kula da haila mai raɗaɗi, premenstrual syndrome,rashin ganin al'ada,daukewar al'ada (menopause),samar da ruwan nono, da polycystic ovarian syndrome.
Takardar ta yi nuni da wani bincike na matan da suka samu daukewar al’ada suka sha miligram 100 na man Shammar sau biyu a kullum na tsawon makonni takwas ya inganta lafiyar su.
Sun sami raguwar alamomi kamar zafin jiki, rashin barci, da gumin cikin dare.
Ki tuntuɓi likita don sanin ko za ki iya amfana daga man Shammar,da sanin yadda ake amfani da shi tare da saka idanu kan duk wani abu nashi mai yuwuwar halayen sakarashin lafiyan, ko wasu side effects.
Wannan yana da mahimmanci musamman idan kina da ciki ko kina ƙoƙarin ɗaukar ciki.
Yana Taimakawa wajen Sauƙaƙe Ciwon Haila
Shammar na iya kwantar da ciwon haila, wanda zai iya taimakawa idan ciwon yana hana ku zuwa makaranta ko aiki ko ayyukanku na yau da kullum.
Wannan na faruwa ne saboda Shammar na iya rage adadin prostaglandins a jikin ku. Prostaglandins wasu sinadarai ne da ke taimakawa tsokoki na mahaifar ku su bude don zubar da tissue da ke layi a cikin mahaifar ku wanda ake kira (endometrium). Mutanen da ke da prostaglandins da yawa suna iya fuskantar raɗaɗi mai yawa akan wanda nasu yake daidai.
Bugu da ƙari, Shammar yana da nitrites, wanda ke taimakawa kwararar jini. Saboda haka, nitrites na iya taimakawa wajen zubar da endometrium cikin sauƙi da sauri fiye da na dabi'a.
Yana Taimakawa wajen Sauƙaƙe Ciwo
Wani bincike na 2020 ya kalli tasirin Shammar akan mutanen da ke fama da osteoarthritis na gwiwa. An ba marasa lafiya sittin da shida da aka zabo capsule mai dauke dagarin Shammar a kowace rana har tsawon makonni biyu. Sun sami raguwa a cikin ciwo da rashin ƙarfi sa sosai.
Yana Inganta Lafiyar Kashi
Shammar kyakkyawan tushe ne na samun calcium, wanda ke bawa ƙasusuwan ku lafiya.
Calcium yana da mahimmanci wajen kara ƙarfin kashi. Rashin calcium na iya ƙara haɗarin haɓaka cutar osteoporosis da karyewar kashi.
Zai Iya Amfani wajen Narkewar Abinci
Ana amfani da tsabar ya'ya daga tsiro na Shammar a matsayin nau'in spices don kara dandanon abinci.
A bangaren magani, ana kuma yin amfani da 'ya'yan shammar don magance kumburi da iskar gas ta hanyar shayin da aka yi daga ƙaramin cokali na tsabar Shammar da ruwan zafi, a zuba na tsawon minti 20, kuma a sha rabin sa'a bayan cin abinci.
Wannan na yin aiki saboda Shammar da tsabar sa suna ba da fiber, wanda ke tallafawa narkewar abinci.
Zai Iya taimakawa wajen Inganta Lafiyar Fata
Shammar yana kunshe da bitamin C, wani maganin antioxidant wanda ke rage lalacewar kwayoyin halitta (cell) wanda free radicals suka haifar, wadanda abubuwa ne masu cutarwa da aka samu ta hanyar ultraviolet (UV).
Free radicals na iya ba da gudummawa ga kansar fata da bayyanar alamun tsufa kafin tsufa (premature ageing).
Zai Iya samar da Kariya Daga Cutuka Masu tsanani
Vitamin da kuma mineral compound da ake samu a Shammar na iya taimakawa wajen hana wasu cututtuka masu tsanani, kamar cututtuka na zuciya da jijiyoyin jini da kuma ciwon daji.
Alal misali, Shammar yana kunshe da fiber. Fiber shine sinadari ɗaya wanda zai iya rage haɗarin cututtukan zuciya.
Hakanan, anethole da aka samu a cikin Shammar na iya taimakawa don rage haɗarin haɓaka ko cigaban girman wasu cututtukan daji.
A cikin wani binciken da akayi a cikin shekarar 2021, masu binciken sun gano cewa anethole yana taimakawa wajen jawo apoptosis.
Apoptosis wani tsarin mutuwar kwayoyin halitta ne (cell death), muhimmin tsari ne don hana haɓaka da yaduwar ƙwayoyin cutar kansa.
Yana Kara Lafiyar Kwakwalwa
Wasu bincike sun nuna cewa Shammar yana taimakawa wajen hana wasu cututtuka kamar cutar Alzheimer.
A cikin wani bincike a 2017, masu binciken sunyi nazarin antioxidants da aka samo a cikin essential oils da kuma ruwan 'ya'yan itace na ganyayyaki hudu, ciki har da shammar.
Bayan tantance ganyen, masu binciken sun gano cewa za su iya taimakawa wajen rage yawan damuwa, wanda ke lalata kwayoyin halitta (cells).
Dangane da binciken da suka yi, masu binciken sun kammala da cewa Shammar yana cikin ganyen da za su taimaka wajen rage raguwar fahimta.
Yana Rage Hadarin Anemia
Iron yana daya daga cikin minerals da ake samu a cikin Shammar. Iron wani muhimmin sashi ne na haemoglobin, wanda shine protein da ke jigilar iskar oxygen daga huhu zuwa sassa daban-daban na jikin ku.
Mutanen da ke da ƙarancin iron na iya haifar da anemia, yanayin da zai iya haifar da rauni da gajiya, a tsakanin sauran alamun. Saboda kasantuwar iron , Shammar zai iya taimakawa wajen sake cike wasu iron a jikinku idan kuna da-ko kuna ƙoƙarin gujewa karancin sa.
Yana tallafawa Lafiyar Ido
Shammar yana kunshe da antioxidants masu yaki da cututtukan ido, kamar macular degeneration. Misali, a cikin binciken da aka buga a cikin 2013, vitamin C da ake samu a cikin shammar yana taimaka wa idanunku. Vitamin C shima ma yana taimakawa wajen sake samar da wasu antioxidants masu tallafawa lafiyar ido, kamar vitamin E.
Sinadarai da ake samu cikin Shammar
Bisa ga bincike na Ma'aikatar Aikin Gona ta Amurka, kofi ɗaya na ɗanyen Shammar yana da dauke da sinadirai masu zuwa:
• Calories: 27 calories
• Fat: 0.17g
• Sodium: 45.2mg
• Carbohydrates: 6.35g
• Fiber: 2.7g
• Protein: 1.08g
• Vitamin C: 10.4mg
Hadarin Shammar
Kamar kowane abinci, ya kamata ku ji daɗin shammar matsakaici. Amfani da Shammar da yawa na iya kaiku ku zuwa estragole, carcinogen da aka samu a cikin Shammar, kuma yana iya haɓaka girman ƙwayoyin cutar kansa.
Bugu da ƙari, Shammar na iya yin mummunan tasiri ga masu ciki da dan tayi mai tasowa (developing fetus).
Alal misali, a cikin binciken daya da akayi a cikin 2015, masu bincike sun gano cewa yin amfani da Shammar akai-akai a lokacin daukar ciki yana da alaƙa da lower gestational age.
Mutanen da ke fama da ciwon farfadiya ya kamata su guje wa man shammar tunda yana iya tayar da farfadiya ga wasu mutanen.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.
✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam
0 Comments