AMFANIN MA'UL WARDI
ماء الورد
Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah, masu yin Ruq'yah da harhada magungunan musulunci.
Ma'ul Wardi ana samar da shi ne ta hanyar matse ruwan da ke cikin wasu furen itatuwa, kamar yadda sunansa ya nuna, "Ma'ul Wardi" wato "Ruwan Fure" da Hausa ko kuma "Rose Water" a Turance.
Wannan sinadari na da matukar amfani ga lafiyar al'uma. Kadan daga ciki su ne:-
1- Gyaran fata.
Daga cikin manya-manyan amfanin Ma'ul wardi shi ne, yana gyara fata, saboda yana dauke da sinadaran 'anti-inflamatory wadanda ke taimakawa wajen gyara matsalolin fata, na ciki da na waje.
Abin sha'awa shi ne ko da Aljani ne ya 6atawa mutum fatarsa to Ma'ul Wardi yana gyara ta, idan aka hada shi da Ma'ul Khal da kuma sinadarin nan mai sanyi wanda ake hada turare da shi wato Alcohol ana shafawa.
Duk wanda ya ta6a zuwa Rukiyyah wajenmu zai ga muna fesawa Aljanu wani ruwa mai sanyi, wanda yake saka Aljanu ihu da kuka, to Ma'ul Wardi da Ma'ul Khal da Alcohol ne muke hadawa.
Likitoci sun ce, haka kawai ma ana iya shafa Ma'ul Wardi a fata, domin kyautata kyawunta da lafiyarta.
2- Gyara Makogwaro.
Shan Ma'ul Wardi, adadin da ya kamata, yana gyara makogwaro, yana sakin murya.
An kawo min marasa lafiya da yawa wadanda Aljanu su ka rufe musu ba ki, ba sa iya magana kwata-kwata. Amma abinda nake hada musu su ne : Ma'ul Wardi, Ma'ul Khal, Zuma sai kuma Hiltit, sai in yi tofi, in ba su, su sha. Dukkansu kuma atake bakinsu yake budewa, su fara magana. Daya ce ma kawai sai washe-gari bakinta ya bude. Dukkansu kuma ba wacce ta sake samun matsalar.
Saboda haka Ma'ul Wardi yana da kyau wajen sha.
3- Maganin infection/Sanyin Mata.
4- Kyautata lafiyar ido.
amma wadannan biyun ya kamata a nemin shawarar masana akan yadda ake amfani da shi.
5- Hana lalacewar abinci ko magani. Ma'ul Wardi yana dauke da sinadarin antioxidants, wanda yake hana abinci maganin saurin ru6ewa ko lalacewa.
6- Maganin Rauni, Quna ko Yankewa.
Ma'ul Wardi yana dauke da sinadaran Antiseptic da Antibacterial wadanda ke taimakawa ciwo saurin warkewa. Wadannan sinadarai suna kuma taimakawa wajen yakar cututtukan da kan iya shiga yayin da aka samu rauni ko aka qone sannan su taimakawa ciwon ya warke da wuri.
7. Maganin ciwon kai.
Ma'ul Wardi yana taimakawa wajen rage radadin ciwon kai ko ya warkar da shi gaba daya, idan aka shafa. Amma zai fi kyau a jika wani yanki mai kyau acikin Ma'ul Wardi din sannan a dora akan tsawon mintunan kamar 45.
8- Maganin Hana Tsufa.
Ma'ana Ma'ul Wardi na 6oye tsufan mutum, musamman yadda yake gyara fata da kuma kyautata lafiyar jiki da gyara idanu, idan ana amfani da shi yadda ya kamata, bisa shawarar masana.
9- Cushewar Ciki/Rashin cin Abinci.
Ko a shekarar 2008, binciken likitoci ya tabbatar da cewa, Ma'ul Wardi na taimakawa wajen saukaka narkewar abinci acikin mutum tare da warware hanji.
10- Ma'ul Wardi yana da kyau wajen hada Magungunan warware sihiri da lalata sharrin Aljanu. Yawanci dai an fi wanke rubutu da shi ko kuma a yi tofi acikinsa.
YADDA AKE AMFANI DA MA'UL WARDI.
1- Za ka iya shafa Ma'ul Wardi a fatarka zallansa ko ka hada shi da ruwa.
2- Za aka iya zuba Ma'ul wardi a shayi ko lemo ko ruwa ka sha, hakan zai fi kyau, fiye da shansa kai tsaye.
3- Likitoci ba su yi bayanin wata illa wajen shan Ma'ul Wardi ba, haka nan ba su ware wadanda ba za su iya amfani da shi ba amma dai a shawarce, kada ka sha Ma'ul wardi sama da cokali biyu a rana daya.
4- Za ki iya samun auduga mai kyau, sai ki dinga dangwalar Ma'ul Wardi kina goge fuskarki da shi.
5- Za ki iya dura Ma'ul Wardi acikin abin fesawa wato 'sprayer' sai ki dinga fesawa a jikinki, idan kin yi wanka.
Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah.
0 Comments