AMFANIN GANYEN RAI-ƊORE WAJEN KIWON LAFIYA:


AMFANIN GANYEN RAI-ƊORE WAJEN KIWON LAFIYA

Ana amfani da Rai-ɗore wajen abubuwa da dama na kyautata lafiya da kuma maganin cututtuka. Ana iya kiransa Rai-ɗore ko kuma a ce Rairai. 

1- Typhoid: Ana tafasa ganyen Raidore hade da itacensa, a saka jar kanwa kadan. Idan ya huce sai a tace, a sha, kofi daya kullum, zuwa kamar kwana uku. Sannan za a iya hada ganyen Raidore da ganyen Gwanda, a tafasa, a sa zuma, a sha, kofi daya, kullum, har zuwa kwana uku ko biyar. 

2- Malaria: Game da zazza6in maleria, a tafasa Raidore, shi kadai ko kuma a hada da ganyen goba. Idan ya tafasa sai a tace, a sa zuma, a sha, rabin kofi da safe, rabi da yamma. Har kwana uku zuwa sati daya. 

3- Matsalolin mara: kamar fitsari mai zafi, rikicewar jinin haila ga mata, dattin mara da rashin kuzari ga maza, da dai sauran dukkan matsalolin mara. A tafasa ganyen Raidore, hade da itacensa da 'ya'yansa da saiwarsa, a saka jar kanwa kadan aciki. Sai a tace, a sha rabin kofi da safe, rabi da yamma, tsawon kwana biyu zuwa uku. 

4- Hawan jini. A tafasa ganyen Raidore, banda itacen, banda saiwar, banda 'ya'yan. Sai a tace, a sa zuma. Idan ya huce sai a dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma. Ana yi ana zuwa gwaji. Sannan za a iya dafa ganyen, a kwadanta, mai lalurar ya dinga ci. 

5- Tsakuwar ciki: A soya 'ya'yan Raidore, sai a daka. A dinga zubawa a shayi, ana sha. Sannan za a iya hada 'ya'yan Raidore da 'ya'yan Kankana, a daka, a dinga sha da nono ko da ruwa, domin narkar da tsakuwar ciki. 

6- Basir: Musamman mai sa daurewar ciki da rashin cin abinci da basir mai tsatstsagawa mutum dubura ko mai tsiro da sa kumburin ciki. A dafa ganyen Raidore, a yi kwado da shi, a ci. Ko a dafa shi, a sha ruwansa. 

7- Olsa. Mai fama da matsalar gyambon ciki wato Olsa. A busar da ganyen Raidore, a takade. Sai a dinga zuba rabin cokali a ruwa, ana sha, kullum sau daya. Za kuma a iya hada shi da ganyen kuka, a dinga auna rabin cokali, ana sha da ruwa ko madara. 

8- Zazza6i: mai sa mutuwar jiki da ciwon ga6o6i ko irin zazza6in da yake rufe mutum lokaci daya. A tafasa Raidore tare da 'yar jar-kanwa, a tace, a sa zuma, a sha. 

 9- ciwon ciki. A tafasa saiwar Raidore, 'yar kadan, tare da jar-kanwa. Idan ya huce sai a sha, sau biyu a rana amma in ya wuce kwana biyu bai dena ba to a tafi asibiti. 

10- Rashin iya cin abinci. Mai fama da cushewar ciki, ba ya iya cin abinci yadda ya kamata. A tafasa Raidore tare da jar kanwa da zuma, ya sha, insha Allahu cikinsa zai bude. 

     ★AMMA A KULA. 
      Matukar za a yi amfani da Raidore wajen ci ko sha, to a tabbatar an wanke shi da gishiri . Ci ko shan Rai dore da yawa a lokaci daya yana iya sa wa mutum yay gudawa. Saiwar Raidore tana da guba, don haka a dinga cireta a lokacin da ba a bukatarta acikin magani. 

Daga shafin Bashir Halilu.

Post a Comment

0 Comments