AMFANIN SHUWAKA WAJEN KYAUTATA LAFIYA.
Daga Cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq’yah da harhada Magunguna na Musulunci.
Shuwaka, da turanci ana kiranta da ‘vernonia amygdalina’ amma an fi saninta da ‘bitter leaf’.
Shuwaka wata ciyawa ce wadda take da koren ganye, ganyenta da yayanta suna da daci. Galibi yado take yi, ba ta wuce tsayin santi mita biyar a sama.
Ana iya amfani da Shuwaka wajen dafawa a sha ruwanta ko kuma ayi miya a ci abinci da ita. Hakanan akan hada shuwaka acikin nau’in kayan girkin da ake bukata.
Ga wasu daga cikin ayyukan shuwaka wajen kara lafiya.
1- Ciwon mara.
A samu ganyen shuwaka, a wanke, a tafasa, a matse ruwan, sai a sa zuma, shansa na magance matsalar ciwon mara da sauran matsalolinta.
2- Ciwon suga.
Dafa ganyen shuwaka ayi kwado, bayan an rage yawan dacinta ta hanyar wankewa, yana taimakawa wajen magance ciwon suga da rage hadarin kamuwa da shi.
3- Masu karamin ciki ba sa shan shuwaka.
Shuwaka na dauke da sinadaran da ke zubar da cikin mace, idan ta sha acikinta.
4- Hawan jini.
Amfani da ganyen shuwaka wajen ci ko sha, yana magance matsalar hawan jini wanda yay sama, yana kuma rage hadarin kamuwa da shi.
5- Kashe kwayoyin cuta.
Shuwaka na da sinadaran da ke kashe kwayoyin cuta, wadanda idonmu ba ya iya ganinsu.
6- Maganin Zazza6i.
Shuwaka na daga cikin tsirran da ke saurin saukar da zazza6i da kuma magance shi, musamman wanda cizon sauro kan haddasa shi.
7- Maganin wari.
Shuwaka na hana tashin wari a wajen da ake zubda kazanta ko cikin abinci.
8- Maganin gudawa.
Ana iya amfani da Shuwaka a matsayin gudunmawar farko da za a baiwa mai fama da gudawa.
0 Comments