YADDA AKE YIN RUQIYYAH


YADDA AKE YIN RUQIYYAH

Yadda za ka cirewa mara lafiya Aljani daga jikinsa ko kuma karya sihirin da aka yi masa ta ingantacciyar hanya, da yaddar Allah. 

Insha Allahu a yau za mu yi cikakken bayani akan yadda ake yin Ruqiyyah.

A larabce, idan aka ce *Ruq'yah*
ﺍﻟﺮﻗﻴﺔ
Ana nufin Hanyar yin magani.
Amma a ilimin Magungunan Muslunci, idan aka ce Ruq'yah, ana nufin hanyar yin amfani da ayoyin Alqur'ani da ingantattun addu'o'i da magunguna domin neman waraka ga mara lafiya.
Mafi yawancin Ruqiyyah ana karantawa mara lafiyar addu'o'in ne a jikinsa ko kuma a tofa masa a ruwa ko acikin mai, ya sha, ya shafe jikinsa.
Ruq'yah ta tabbata a sunnar Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
domin ya yi da kansa, kuma sahabbansa sun yi, sannan malaman sunnah magabata an samu wadanda suka aiwatar da Rukiyyah a cikinsu.

Alhadith:-

ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺃﺑﻮ ﺍﻟﻨﻌﻤﺎﻥ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺃﺑﻮ ﻋﻮﺍﻧﺔ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺑﺸﺮ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺍﻟﻤﺘﻮﻛﻞ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺳﻌﻴﺪ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ ﺍﻧﻄﻠﻖ ﻧﻔﺮ ﻣﻦ ﺃﺻﺤﺎﺏ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻲ ﺳﻔﺮﺓ ﺳﺎﻓﺮﻭﻫﺎ ﺣﺘﻰ ﻧﺰﻟﻮﺍ ﻋﻠﻰ ﺣﻲ ﻣﻦ ﺃﺣﻴﺎﺀ ﺍﻟﻌﺮﺏ ﻓﺎﺳﺘﻀﺎﻓﻮﻫﻢ ﻓﺄﺑﻮﺍ ﺃﻥ ﻳﻀﻴﻔﻮﻫﻢ ﻓﻠﺪﻍ ﺳﻴﺪ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﺤﻲ ﻓﺴﻌﻮﺍ ﻟﻪ ﺑﻜﻞ ﺷﻲﺀ ﻻ ﻳﻨﻔﻌﻪ ﺷﻲﺀ ﻓﻘﺎﻝ ﺑﻌﻀﻬﻢ ﻟﻮ ﺃﺗﻴﺘﻢ ﻫﺆﻻﺀ ﺍﻟﺮﻫﻂ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻧﺰﻟﻮﺍ ﻟﻌﻠﻪ ﺃﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻋﻨﺪ ﺑﻌﻀﻬﻢ ﺷﻲﺀ ﻓﺄﺗﻮﻫﻢ ﻓﻘﺎﻟﻮﺍ ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺮﻫﻂ ﺇﻥ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻟﺪﻍ ﻭﺳﻌﻴﻨﺎ ﻟﻪ ﺑﻜﻞ ﺷﻲﺀ ﻻ ﻳﻨﻔﻌﻪ ﻓﻬﻞ ﻋﻨﺪ ﺃﺣﺪ ﻣﻨﻜﻢ ﻣﻦ ﺷﻲﺀ ﻓﻘﺎﻝ ﺑﻌﻀﻬﻢ ﻧﻌﻢ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺇﻧﻲ ﻷﺭﻗﻲ ﻭﻟﻜﻦ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻟﻘﺪ ﺍﺳﺘﻀﻔﻨﺎﻛﻢ ﻓﻠﻢ ﺗﻀﻴﻔﻮﻧﺎ ﻓﻤﺎ ﺃﻧﺎ ﺑﺮﺍﻕ ﻟﻜﻢ ﺣﺘﻰ ﺗﺠﻌﻠﻮﺍ ﻟﻨﺎ ﺟﻌﻼ ﻓﺼﺎﻟﺤﻮﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﻗﻄﻴﻊ ﻣﻦ ﺍﻟﻐﻨﻢ ﻓﺎﻧﻄﻠﻖ ﻳﺘﻔﻞ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﻳﻘﺮﺃ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ﻓﻜﺄﻧﻤﺎ ﻧﺸﻂ ﻣﻦ ﻋﻘﺎﻝ ﻓﺎﻧﻄﻠﻖ ﻳﻤﺸﻲ ﻭﻣﺎ ﺑﻪ ﻗﻠﺒﺔ ﻗﺎﻝ ﻓﺄﻭﻓﻮﻫﻢ ﺟﻌﻠﻬﻢ ﺍﻟﺬﻱ ﺻﺎﻟﺤﻮﻫﻢ ﻋﻠﻴﻪ ﻓﻘﺎﻝ ﺑﻌﻀﻬﻢ ﺍﻗﺴﻤﻮﺍ ﻓﻘﺎﻝ ﺍﻟﺬﻱ ﺭﻗﻰ ﻻ ﺗﻔﻌﻠﻮﺍ ﺣﺘﻰ ﻧﺄﺗﻲ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻨﺬﻛﺮ ﻟﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﻛﺎﻥ ﻓﻨﻨﻈﺮ ﻣﺎ ﻳﺄﻣﺮﻧﺎ ﻓﻘﺪﻣﻮﺍ ﻋﻠﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﺬﻛﺮﻭﺍ ﻟﻪ ﻓﻘﺎﻝ ﻭﻣﺎ ﻳﺪﺭﻳﻚ ﺃﻧﻬﺎ ﺭﻗﻴﺔ ﺛﻢ ﻗﺎﻝ ﻗﺪ ﺃﺻﺒﺘﻢ ﺍﻗﺴﻤﻮﺍ ﻭﺍﺿﺮﺑﻮﺍ ﻟﻲ ﻣﻌﻜﻢ ﺳﻬﻤﺎ ﻓﻀﺤﻚ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ ﺃﺑﻮ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻗﺎﻝ ﺷﻌﺒﺔ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺃﺑﻮ ﺑﺸﺮ ﺳﻤﻌﺖ ﺃﺑﺎ ﺍﻟﻤﺘﻮﻛﻞ ﺑﻬﺬﺍ
.
*Ma'ana* "Wasu daga cikin Sahabban Manzon Allah
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
sun yi tafiya, sai su ka sauka a wani gari, su ka nemi mutanen garin su kar6i bakuncinsu amma su ka ki. Sai suka fita bayan garin suka samu waje su ka zauna.
Sai shugaban mutanen garin nan ya kamu da rashin lafiya sukay masa duk abinda za su iya amma ya gagara warkewa.
Sai wani daga cikinsu ya ce "To ai ya kamata mu je wajen wadancan mutanen na bayan gari, watakila wani daga cikinsu yana da magani.
Sai suka fito bayan gari su ka samu sahabban Manzon Allah
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
su ka gaya musu abinda ke faruwa. Sai wani daga cikinsu ya ce "Ni na iya Rukiyyah amma gaskiya ba zan yi masa ba, saboda mun nemi ku ba mu masauki ku ka `ki, saidai in za ku biya mu ladan aikinmu. Sai su ka ce sun yarda za su biya shi lada. Su kay tsada akan wani adadi na dabbobin da za a ba shi.
Sai su ka je ya karanta masa 'Fatiha' Sai kuwa mutumin ya tsahi kamar bai ta6a yin rashin lafiya ba.
Da suka kar6o dabbobin sai suka taho wajen Manzon Allah
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
su ka gaya masa abinda ya faru. Sai Manzon Allah
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ya ce masa "Ya akay ka gane ana iya yin Ruqiyyah da Fatiha?".
Sannan yay dariya ya ce "Ni ma ku miko min nawa rabon a cikin abinda ku ka kar6a".

*WANDA YA KAMATA YAY RUQIYYAH*
.
i) Lallai wanda zai yi Ruqiyyah ya kasance musulmi ne. Domin idan Arne ne to bokanci zai yi.
.
ii)Yana da kyau ya zama ya fahimci sunnah kuma yana aiki da ita.
.
iii)Ya kasance yana da cikakken ilimin addini musamman abinda ya shafi Tauhidi, Musamman Tauhidir Rububiyyah da Uluhiyyah.
.
iv) Wanda zai yi Rukiyyah lallai ya zama ya iya karanta Alqur'ani da Tajwidi.
.
v) Ana so mai Rukiyyah ya zama ya san wani abu na larabci, ta yadda akalla zai zama yana fahimtar ma'anar Ayoyin da yake karantawa.
.
vi) In da hali an fi so wanda yake yin Ruqiyyah ya zama yana da aure, musamman idan ya mayar da ita sana'a ko kuma aikin yau da gobe.
.
vii) Lallai ka zama jarumi, mara tsoro kuma cikakken mai dogaro da Allah, domin kuwa Aljanu za su dinga yi maka barazana, wani lokaci ma su dinga kawo maka hari.
.
viii) Ana so mai Ruqiyyah ya dinga kula da kansa ta fuskar addu'o'i da neman tsari kamar yadda yake yiwa wadansu ko ma fiye da haka.
ix) Kafin ka fara yin Rukiyyah, yana da kyau ya zama an ta6a yi a gabanka kuma kana da ilimi akanta.
Bashir Halilu 08162600700.

*WAJE KO KUMA DAKIN DA YA KAMATA A YI RUQIYYAH A CIKINSA.*
.
i)An fi so a yi Ruqiyyah a cikin daki ba waje ba.
.
ii) Yana da kyau a kulle kofa da taga kuma a ambaci Allah in za a kulle, domin idan ana Rukiyyah wasu Aljanun suna zuwa su taru, suna kokarin sawa Aljanin da aka kama ya gudu.
.
iii) A kawar da duk wani abu da ke kawo Shaidanu daga dakin, kamar hotuna ko mudubi ko kade-kade da dai sauransu. Domin barinsu yana sa wa ay ta karatu amma Aljanin ya maqale a jikinsu akasa kama shi.
.
iv) Ba a so mutane su cika dakin da ake yin Ruqiyyah suna kallo. An fi so ya zama daga masu Ruqiyyah, sai wanda za ay wa Ruqiyyar, sai Waliyyan wanda za ay wa Rukiyyar su kadai a wajen. Saboda idan mutane sukay yawa, to Aljanun za su iya fita su koma jikin wani a cikin `yan kallo.
.
.
*YADDA YA KAMATA AY RUKIYYA*

1) Idan mace ce za ay wa Ruqiyyah, lallai ya zama ta sanya kayan da suka rufe mata jikinta sosai, ta yadda ba za ta yaye tsaraicinta ba koda Aljani ya bigeta.
2) Hakanan ya kasance mijinta ko wani daga cikin muharramanta yana wajen daga farawa har zuwa gamawa.
3)Koda yaro ne ko namiji, to ya kasance Waliyyinsa ne ko wakilinsa zai rike shi ay masa karatun sannan yana da kyau duk wanda zai tsaya yayinda ake gabatar da Ruqiyyah ya kasance ya yi alwala.
4) Ka fara da tambayar mara lafiyar irin abubuwanda suke damunsa. Kamar irin mafarke-mafarken da yake yi, da abubuwan da suke zuwar masa a zahiri, da wadanda yake ji a jikinsa, da lokutan da ciwon ya fi tashi da kuma asalin abinda ya faru da shi a farkon lalura da dai makamantansu.

Yin wadannan tambayoyi zai taimaka wa mai Ruqiyyah wajen gane nau'in Aljanin da yake jikin mutum, da halittar Aljanin, da gurin zaman Aljanin, da inda ya zauna a jikin mutum kuma za ka gane shin ko turo Aljanin akay ko kuma shi ne ya sa kansa. Ta hanyar tambaoyin dai za ka iya gane cewa Aljanin na gado ne ko mazauna gida ne, sannan za ka fahimci ko Aljanin da in an yi Rukiyyah yake magana ne ko kuma wanda ba ya magana yayin Rukiyya.

*YADDA AKE AIWATAR DA RUKIYYAH*
1) Da farko mai Rukiyyah zai samu ruwa, ya tofa Ayoyin Rukiyyah aciki. Da kuma man Zaitun, shi ma a tofa Ayoyin Rukiyya a ciki. Sai ka baiwa mara lafiyar ya sha ya shafa afuskarsa bayan ya yi alwala.
.
ii) Sai ka umarci mara lafiyar ya zauna a gabanka, ya fuskantoka ko ya juya bayansa ko kuma ya zauna a gefenka na dama yana kallon bayanka.
.
iii) Sai kay Bismillahi ka riqe goshinsa idan namiji ne, in kuma yaro ne karami sai ka dora hannunka a kirjinsa ko a gadon bayansa, in macece babba sai ka dora tafin hannunka a tsakiyar kanta, ko ka zauna a bayan mutum, amma an fi so ka umarci mijinta ko muharraminta ya dora hannunsa.
Ana iya riqe babban dan yatsan mutum na kafa ko na hannu, wasu ma suna daurewa da zare, don kada Aljanin ya gudu ko kuma ya baka wahala yayin aikin.
Dukkan wannan sanya hannu ana yinsa ne don kada Aljanin da yake jikin mutum ya gudu, har sai an ba shi damar tafiya. Saidai idan ba ka so kay magana da Aljanin to ba sai ka sanya hannunka a jikin mara lafiyar ba.
.
iv) Ka umarci wanda za ay wa Ruqiyyah ya bude kunnensa na dama, ko ya budesu duka, saboda ya zama karatun yana shiga kunnensa sosai.
.
v) Sai ka kusanto da bakinka zuwa kunnensa na dama, ka daga murya, ko kay amfani da _loud speaker_ in kuma yaro ne sai ka sassauta, kay kiran sallah sau uku, sannan ka fara karanta Ayoyin Rukiyyah.
v) A lokacin da kake karatun in kana da turaren kona Aljani sai ka kunna kuma kana yi kana baiwa mutum ruwan Rukiyyar yana sha, ana zuba masa ajikinsa.
.
vii) A lokacin da kake karatun sai ka dinga lura da mara lafiyar ta yadda za ka gane Aljanin ya bayyana a jikinsa.
*YADDA ZA KA GANE ALJANI YA BAYYANA AJIKIN MUTUM.*
.
i) Wani Aljanin a lokacin da kake karatun kawai sai ka ga mutum ya tintsire ya fadi, ya kife a kasa. Jinnul Katfa sun fi bayyana ta wannan salon, su da Jinnul Bakam.
.
ii) Wani kuma zai kankame jikinsa yana karkarwa, mafi yawa Tabriyqul Jinni ne sukey haka. Dama su matsorata ne amma fa 'yan rainin wayo ne kuma sun fi shiga jikin kananan yara su da jinnul Atfal.
.
iii) Wani zai bayyana yana kyalkyala dariya. Jinnut Tayyar sukan yi haka. Amma mafi yawanci Jinnus Sihr sun fi yi, saboda suna da kariya ta sihiri. Karatun da ake yi ba ya ta6a jikinsu balle ya kona su. Saboda haka kana karatu sunay maka dariya. Mun yi bayanin yadda ake yiwa wadannan nau'in Aljanu a kona su a cikin rubutun mu mai taken "JINNUS SIHR" ko kuma KHADIMUS SIHR"
.
iv) Wani Aljanin kuma zai baiyana yana ihu tare da neman afuwa.
.
v) Akwai wanda za ka ga ya dartse idonsa ya ki budewa, idan kasa hannu zaka bude masa idon sai ya sake damtsewa.
.
vi) Akwai wanda yake bayyana da kokawa tare da kokarin tashi ya gudu. Jinnut Tayyar sun fi yin haka.
.
vii) Wani Aljanin kuma saidai kawai ka ji ya ce "Assalamu alaykum" amma mafi yawan Aljanu masu baiyana da Assalamu alaykum mayaudara ne. Indai ka ji Aljani ya baiyanar maka yayin rukiyyah da wannan sigar to kay a hankali, domin a karshe zai maka karya ya yaudareka, domin a karshe zai ce ma ka shi taimakon mara lafiyar yake ba cutar da shi yake ba. Jinnul Filosafiy sun fi yin irin wannan.
.
viii) Wani Aljanin yana bayyana da zagi tare da tsinewa mai yin Ruqiyyar da wanda ya kawo mara lafiyar.
.
ix) Akwai wanda za ka ga idanuwansa sun kakkafe ba ya ko kiftawa.
.
x) Wani kuma ba zai yi komai ba, saidai ka ga fuskarsa ta canja, ta kwakkwa6e ta yi duhu, to alamar Aljanin ya bayyana kenan.
.
xi) Wani idan ana Ruqiyyah saidai kawai aga hawaye yana zubowa a idonsa ko kuma Aljanin ya dinga kuka da hawaye sha6e-sha6e. Wannan Jinnus Sihr ne kawai suke yin haka.
.
xii) Wani kuma idan kana cikin yi masa karatun sai ka ji ya damqi hannunka da karfi ko kuma ya ruqunqume na kusa da shi.
.
xiii) Wani Aljanin kuma idan ya bayyana idon mutum ne yake canjawa ya yi ja.
Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah .

*YADDA ZA KA YI DA ALJANI BAYAN YA BAYYANA AJIKIN MUTUM.*
.
Kana da za6i guda biyu.
Kodai kay ta yi masa karatu har sai ya kone ko kuma ya fita daga jikin mutum ko kuma ka tsaya kay magana da shi.
i) Idan kana so kay magana da Aljanin, to lokacin da ya bayyana sai ka faray masa tambayoyi a nitse yadda ba zai firgita ba.
Ka tambaye shi sunansa, dalilin shigarsa jikin mutumin, adadinsu a jikin mutumin, tsawon lokacin da suka dauka a jikinsa, suy bayanin irin cutarwar da sukay masa, su fadi guraren da sukay masa ajjiya da dai sauran tambayoyi masu muhimmanci wadanda za su taimaka wajen gano bakin zaren.
.
Saidai kada ka saki jiki da Aljani yay ta baka labarai marasa amfani kuma kada ka bari ya ambaci sunan wani mutum acikin bayanin da yakey maka.
.
ii) Idan Kafirin Aljani ne kay masa bayanin musulunci kuma ka nemi ya musulunta. Idan kuma Musulmi ne kay masa nasiha ya dena aikin zalunci da shiga jikin mutane.
.
iii) Idan suna da yawa ajikin mara lafiyar, duk wanda kay magana da shi sai ka ce ya turo maka dan'uwansa, har kay magana da su daya-bayan daya.
.
iv) Ka nemi Aljanin ya fita daga jikin mara lafiyar tare da yin Alakwarin ba zai dawo ba. Yana da kyau ka sa shi yay rantsuwa da Allah sannan ka tsoratar da shi azabar mai karya Alkawari.
.
*IDAN AL-JANI YA ƘI YIN MAGANA KO YA CE BA ZAI FITA BA*

1- Kay mafani da ruwan Rukiyyar daka hada, ka dinga zuba masa a fuska, kana karanta Ayoyin Quna ko na Azaba.
2- Kay amfani da Man rukiyyah, ka dinga shafa masa a goshi da yatsun kafa dana hannu, idan yaro ne ka shafa masa har a qirjinsa da cikinsa da wuyanasa da gadin bayansa.
3-Kay amfani da turarukan da suke Azabtar da Aljani, kay masa hayaki.
4- Ka matse masa babban yatsansa na hannu ko kafa, tare da karanta Alqur'ani. Za ka ji yana ihu, tare da neman ceto.
5- A hade hannayensa waje guda, a rike su da kyau, ta yadda ba zai iya dinga bude su, don indai yana bude hannayensa to zai gudu ya barka da mutumin.
6- In kuma magana ce ya ki yi, sai ka hada da karanta masa Ayatun Nuɗƙi.

Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah 08162600700.

*TA INA YA KAMATA ALJANI YA FITA DAGA JIKIN MUTUM?*
.
Aljanu, musamman wadanda ba sa so su bar jikin mara lafiya. Idan aka tambayesu ta inda za su fita sukanyi kame-kame, suy ta lissafo wasu kofofi a jikin mutum. Saidai gaskiya duk ta kofar da Aljani ya fita daga jikin mutum zai iya cutar da shi. Misali, idan ya fita ta ido mutum zai iya makancewa. In ya fita ta hanci yana iya sawa jini yay ta zuba wanda zai iya kai mutum ga mutuwa. Haka kunne ko dubura ko farji ko cibiya da makamantansu, dukkansu Aljanu suna cewa za su fita tanan amma kada abarsu domin hanyoyi ne masu cutarwa.
.
Hanyar da ake baiwa Aljani umarni ya fita ita ce ya fita ta bakin mutum. Ko kuma ka umarci Aljanin ya rarraba jikinsa ya fita ta ga6o6in jikin mutum. Amma wannan hanyar Aljanu ba sa sonta saboda suna cutuwa, saidai ta fi zaman lafiya ga dan-Adam.

*IDAN ALJANI YACE MAKA BA ZAI IYA FITA BA*
Wani lokacin Aljani zai ce maka gaskiya shi ba zai iya fita daga jikin mutum ba, ko kuma ya ce ya rasa yadda zai yi ya fita.
Suna yin haka ne saboda dayan abubuwa guda hudu:-
1- Na daya wani Aljanin yaro ne, don haka bai san yadda ake fita daga jikin mutum ba.
2- Na biyu wani Aljanin ya wahala sosai a hannunka, yayin yin rukiyyah, don haka jikinsa ya yi rauni, ta yadda ba zai bai iya fita ba.
3- Na uku, wani Aljani bokayene ko `yannuwansa Aljanu suka daureshi a ajikin mutum, don haka shi ma ba zai iya kwancewa ya fita ba.
4- Dalili na hudu kuma wani Aljani tsabar taurin kai ne da yaudara, zai sa ya ce maka shi ba zai iya fita ba.

*To idan haka ta faru, abinda za kay shi ne*
1- Kai masa kiran sallah a kunnensa, sau uku.
2- Ka karanta masa Suratu Yasin.
3- Ka karanta masa Ayatul ikhraji.
4- In ka daure masa yatsa to ka kwance kuma ka dauke hannunka daga kansa.
5-Kay masa turare da hayaki mai budewa Aljani kofa.

*YADDA ZA KA GANE ALJANI YA FITA DAGA JIKIN MUTUM.*
.
Wani lokacin Aljanu suna yin karya, su ce ma ka sun fita daga jikin mutum, alhali suna nan ba su tafi ba. Wani ma suna fita daga dakin da akay rukiyyar ko gidan sai su sake tashi. Wani kuma sai mutum ya je gida tukuna sai su sake tashi.

Daga cikin hanyoyin da za ka gane Aljani ya tafi daga jikin mutum:-

i) Za ka ga Mutum ya yi hamma ko atishawa.
.
ii) Wani kuma za ka ga ya daga dunduniyar kafarsa sama kadan.
.
iii) Akwai wanda za ka ji ya yi ajjiyar zuciya da karfi.
.
iv) Wani mutumin ana cire masa Aljani a take zai kwanta ya zarce da bacci. Saidai wannan ta fi faruwa idan ya kasance ba ya samun bacci lokacin da yake lalurar.
.
v) Idan ka ga mutum yana dube-dube tare da tambayar abinda yake faruwa da shi, to alama ce ta cewa Aljanin ya tafi.
.
vi) Za ka ga mutum ya bude idonsa yana kallon mutane, idan lokacin da Aljanin ya bayyana idonsa a rufe yake.
.
vii) Wani kuma za ka ga ya yi mika tare da Ambaton Allah.
.
viii) Idan ba ka fuskanci wadannan alamomi ba, sai ka umarci mutumin ya karanta maka Ayatal kursiyyu ko wata aya daga Alqur'ani. Idan ya ki karantawa ko ya ce bai iya ba ko yana karantawa ba daidai ba ko yana tsallake, alhali kuma ya iya karatun, to alama ce ta Aljanin bai tafi ba.
.
ix) Ka umarci wanda akaywa Rukiyyar ya dauki ruwan Rukiyyar da hannunsa ya sha sannan ya dauki sauran maganin ya shafa ajikinsa da kansa. Idan ya ki shan ruwan ko kuma yay watsi da shi to Aljanin bai fita ba.
.
x) Bayan an gama Rukiyyah, idan ka ga mutum yanay maka Allah Ya isa, yana cewa ba zai kuma dawowa wajenka ba ko yana zaginka, to Alajanin ne a jikinsa.
.
xi) Za ka ga fuskar mutum ta saki, ya kara kyau, ya dawo hayyacinsa, wani ma yana raha da mutane. Shi ma alama ce ta cewa Aljanin ya fita.
.
xii) Idan ba ka gane wadannan alamomi ba, sai ka tambayi mara lafiyar:
Shin yana jin abu nay masa yawo ajikinsa kamar kiyashi?!, ko yana ganin wadansu halittu a kusa da shi?!, ko kuma yana ji kansa yanay masa ciwo?!. Idan yana fuskantara wadannan matsaloli a lokacin to Aljanin bai bar jikinsa ba., don haka sai a sake maimaita masa Rukiyyah.

*BAYAN AN GAMA RUQIYYAH*.
.
i) Kay wa mara lafiyar da wadanda ke tare da shi bayani cewa: ita Rukiyyah addu'a ce kuma tana yin tasiri ne da iznin Allah. Kay masa bayani akan ya cire tsoro daga ransa sannan ya samu cikakken tawakkali ga Allah. Ka karafafa masa guiwa akan kula da addu'o'i da karatun Alqur'an da kuma amfani magunguna idan an ba shi.
.
ii) Ka hada masa Ruwan Rukiyyah, da Man Rukiyyah, ka umarce ya tafi da shi ya dinga sha yana shafe jikinsa. Haka nan yana da kyau ka hada masa magunguna wadanda zai dinga amfani da su.
.
iii) Ana so ya zama an yi wa mutum Rukiyyah kamar sau uku. Don haka sai ka umarce shi ya dawo bayan kwana uku-uku ko bakwai-bakwai ana maimaita masa Rukiyyar.

Daga Cibiyar masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci.

Post a Comment

0 Comments