YADDA AKE YIN MAN LEMON TSAMI DA KUMA AMFANIN MAN LEMON TSAMI WAJEN KYAUTATA LAFIYA



YADDA AKE YIN MAN LEMON TSAMI DA KUMA AMFANIN MAN LEMON TSAMI WAJEN KYAUTATA LAFIYA

A samu lemon tsami, sai a ɓare fatar, kada a yi
amfani da ruwan lemon tsami wajen hada man
lemon tsamin.
Bayan an ɓare ɓawon, sai a shanya a karkashin
fanka kamar tsawon awa daya. Bayan ya dan
bushe, sai a zuba acikin gora ko kwlaba sannan a zuba man kwakwa ko man Zaiyun a gauraya bawan da man a gorar sannan a
rufe. Sai a samu gurin da babu rana ko daki ko kicin a
ajiye kamar tsawon sati biyu. Amma a kullum a
rika zuwa ana girgizawa. Shi ke nan! Man lemon
tsami ya samu.

Hanya ta biyu ta yin Man lemon tsami kuma ita ce

   A zuba ɓawon a tukunya sannan sai a zuba man
kwa-kwa a dora a wuta amma kada wutar ta yi
yawa. A rika gaurayawa tsawon minti biyar. Bayan
haka, sai a sauke ya huce sannan sai a zuba a
kwalba.

Daga shafin Bashir Halilu.

AMFANIN MAN LEMON TSAMI WAJEN KYAUTATA LAFIYA. 

     Man lemon tsami yana da mahimmanci sosai musamman ma a fata, domin yana dauke da
sinadarin bitamin C. wannan sinadarin kuma yana kara lafiya ne a jiki da kuma fata. Man yana warkar da kurajen fuska, yana maganin kwarkwata, yana taimakawa wajen
kara wa fatar fuska haske ba tare da yin bilicin ba.

Uwa uba kuma yana taimakawa wajen magance mura. Saidai kuma kada a shiga rana da man lemon tsami
a fuska domin zai iya illata fatar. Don haka an fi
son a shafa shi da safe ko da yamma domin
samun sakamako mafi inganci.

YADDA ZA A YI AMFANI DA MAN LEMON TSAMI 

1-GYARA FUSKA:
 ana Amfani da Lemon Tsami wajen kauda Kurajen Fuska, pimples, da ƙyasfi, yana sa fuska ta kara kyau, idan ana shafe fuska da shi. Sannan a kula, kada a bari ya shiga idanu kuma kada a shiga rana sai an wanke shi. 

2- FITAR DA DATTIN HAKORA DA MAGANCE WARIN BAKI
Ayi amfani da Burushin wanke Baki da ruwan
LEMON TSAMI a wanke Hakora Zasu fita kar, Baki
zai bar wari, amma kar arika wankewa akai-akai
sai lokaci-lokaci saboda zai iya raunana karfin
hakora.

3-WARIN QASHI (KO WARIN HAMMATA)
Idan Ana fama da ciwon warin Qashi, ko rashin
tsaftace Hammata yadda ya kamata, Idan an shafa LEMUN TSAMI a Hamata zai kauda wannan warin.

4-RAGE KIBA DA TIMBI (TEBA)
Wanda ke buqatar haka, ya samu LEMON TSAMI daya a ruwan sha da bai wuce kofi daya ba, lokaci-lokaci, kiba da tai6a zasu sa6e.

5-RAUNI (CIWO), Sabon raunin da bai wuce Hankali ba, da zarar an matsa mai LEMON TSAMI zai kame ya warke amma fa akwai zafi. 

6-RAGE SHA'AWA, ana shan LEMUN TSAMI da
Lipton dan rage ƙarfin sha'awa.

7-MAQYAN-QYARO, ana goge maqanqaro da
LEMON TSAMI
akai-akai zai mutu.

8-AMOSANI, Ana goga LEMON TSAMI a kai bayan an aske gashin kan.

9-KAWAR DA ƘARNI, Ana amfani da LEMUN TSAMI wajen kawar da karnin kifi.

AMMA A KULA:

Idan mace ta yawaita amfani da Lemon tsami tana sha to zai rage mata sha'awa. Haka mata
masu ciki kada su yawaita shan Lemon
tsami. Masu Gembon ciki wato Olsa, su ma su
kula wajen shan lemon tsami.
Amma dukkan wadannan zai musu illa ne in sun
sha a ciki ba wai shafawa ba.

    Daga shafin Bashir Halilu.

Post a Comment

0 Comments