MAI KISHIN MATARSA


MAI KISHIN MATARSA:

"Wanda baya kishin matarsa bazai shiga aljannah ba, kuma baya daga cikin sahun namjin da yafi kowane namiji, domin yana tabbatar da alfasha ne acikin iyalansa, kuma baya nuna kishinsa akansu ballema ya toshe wata kafar barnar a garesu"

"Imam An-Nasa'i (r.h) ya ruwaito cewa Manzon Allah Yace: Mutāne uku hakika Allah yā haramtā musu shiga Aljannah, [1] Mai yin tätil da giyā/me shan giyà, [2] Me cusgunawa iyāyensa, [3] Mara kíshin mātarsa, wanda yake tabbatar da mummunan abu, [Al'fahshä] acikin iyālan sa" (32) : ll

"Wato duk wanda yake shi a rayuwarsa bayā kishin mātansa baya tsoron ya barsu suita yāwo a gari ko yabarsu suna shigar da bata dâce ba, ko kuma bâya killace su a inda zai zamana cewa bāsà yawan bayyanuwa ga mazājen da basu halasta a garesu ba, to shima da ikon Allah Aljannah kwalelen sa matukar shima bai tuba ya gyara ba"

"Kishin da ake nufi anan fa bawai mummunan kishi ba wanda ya fita da cikin koyarwar addinin musulunci ba, domin hakika nasan wasu zafin kishi garesu, ta yadda ko magana yaga tanayi da wani dan-uwanta sai ya nemi ya saketa sabida tsabar jin haushi, wannan ba shine kishin da ake nufi na musulunci ba, saidai shima idan akwai wata barna da ake tsoro ne acikin yin maganar nata da dan-uwan nata"

Post a Comment

0 Comments