Kanƙancewar Zakari (Penile shrinkage)
Kankancewar zakari na nufin raguwar girman al'aura, wato wani yanayi ne da al'aurar namiji baligi ke zama ƙarama tamkar ta ƙaramin yaro - ta shige ciki ko ta rage tsawo ko kauri a lokacin da take kwance (flaccid state) ko a miƙe (erect state) saɓanin yanda take ada. Wannan yanayi na faruwa ga mutum ne a lokacin da yake manyanta cikin rayuwarsa, a dabi'ance. Hakan na faruwa ne ga mutane da shekarunsu na haifuwa suka kai 30 zuwa 40. Amma duk da haka akan sami matasa da yawa wanda basu kai ga wadannan shekarun haifuwa ba masu fama da wannan matsalar. Saidai wasu da yawa daga cikin masu bada maganin gargajiyar Hausa na ganin cewar matsalar ƙanƙancewar zakari matsala ce kai tsaye dake da alaƙa da ZAFI ko SANYIN MARA, suke iƙrari.
Kankancewar zakari dai matsala ce dake cima mazaje tuwo a ƙwarya musamman irin yanda wasu da yawa ke jin kimarsu da alfaharinsu na kasancewarsu maza na fuskantar ƙalubale. Mutane a al'adun duniya da dama na ganin isasshen al'aurar namiji ita ce abin tunƙaho da fahari ga kowani mutum dake amsa sunansa namiji , kuma itace kimarsa ga 'ya mace. To saidai ƙanƙancewar zakari idan ba yawa tayi ba ba'a tunanin zata iya haddasa rashin gamsuwar jima'i tsakanin ma'aurata. Akwai dalilai na lafiya da dama da zasu iya bada haske gameda ƙanƙancewar gaba. Wasu dalilai na daban da ka iya haddasa kankancewar zakari ga matasa ko manya.
Kabir Yusuf Danwurin Dutsi
0 Comments