MASU TINANIN KO SUNA DA KANKANTAR GABA
Binciken ilimi ya nuna cewa yanayin girman jikin mutum, karanta, tsawo ko gajartar jikin mutum bashida alaka da yanayin girma, tsawo ko gajartar al'aurarsa kamar yanda wasu
ke tunani.
.
Sau da yawa akan samu akasin abunda ake tunani. Dayawa daga cikin masu binciken kimiyya da nazari akan al'aurar 'dan adam sun raba mutane (baligai) zuwa kaso uku (3):
.
Kason farko (1) sune mutane
na tsaka-tsakiya (average) wajen yanayin girman al'aurarsu kuma sune mutanen da akafi yawan samu.
.
Kaso na biyu (2) sune mafi girman al'aura (above average), wato sunfi na tsaka-
tsakiya girman mazakuta.
.
Kaso na uku (3) kuma sune na karshe wadanda suke da qasa da abunda kaso na 2 suke dashi (below average), wato masu
karantar al'aura.
.
A lokacinda al'aurar mutum baligi take kwance ba a mike ba (flaccid state) tanada kimanin tsawon inci 3 da `digo 5 zuwa
kusan inci 4 (3.5- 3.9 inches = 9-10 cm) amma bai kai inci 4 ba, wato inci 3 da `digo 9. Wannan shine yanayin tsawo na
mutanen kason farko, wato na tsaka-tsakiya.
.
Kuma shine tsawon da akafi yawan samu a
cikin mutane. Inci 4 zuwa sama kuma shine tsawon mazakutar mutanen kaso na 2, wato wanda su kafi mutanen dake cikin kaso na 2 tsawon mazakuta a lokacinda take kwance (flaccid length of penis). Haka kuma, qasa da inci 3 da rabi shine tsawon mazakutar mutanen kaso na 3.
.
Toh saidai kankantar gaban da namiji a lokacinda yake kwance (flaccid length of penis) bashi bane abunda yake nuni da zahirin tsawonsa ba. Domin kuwa gaba na iya mikewa daga kankantarsa zuwa tsawo mai yawa. Hakan kuwa na yawan faruwa ga wasu mutanen.
.
Mutumin dake cikin kason mutanen farko, a lokacinda gabansa ya mike sosai (erect)
Gaban nada kimanin tsawon inci 5 da `digo 5 (rabi) zuwa inci 6 da digo 3 (5.5 - 6.3 in = 14-16 cm).
.
Ma'ana mutum wanda keda tsawon gaba na inci 5 da rabi ko inci 6 ko kuma zuwa gidan inci 6 da `digo 3 toh ya fada cikin kason mutanen farko (average). Mutumin dake da sama da wannan adadi kuma ya fada cikin kason mutane na 2, wato mutane masu zakari inci 6 da `digo 4 zuwa sama.
.
Haka kuma, mutumin dake da qasa da
inci 5 da rabi wato daga inci 5 da `digo 4 (5.4 in) zuwa qasa ko inci 3 zuwa qasa, toh ya fada cikin kason mutanen karshe
(wato mutane na 3) masu karantar gaba, Kauri, fadi ko gwabin gaba ko kuma (penis
thickness, girth, width, or circumference) na kason mutanen farko nada kimanin inci
4 da `digo 7 zuwa gidan inci 5 da `digo 1 (4.7-5.1 in = 12-13 cm).
.
Mafi yawancin mutane suna cikin kason mutane na 2 (average). Bugu da qari, mutum zai iya zamantowa yana da tsawon
mazakuta da ya fada cikin kason farko ko na biyu amma fadi/ kaurin mazakutar ya fada cikin kaso na biyu ko na farko.
Allah yasa mu dace
Kabir Yusuf Danwurin Dutsi
0 Comments