NAMIJI BAYA IYA YANKE HUKUNCI KO TABBATAR DA BAYA DA LAFIYAR GABA MATUKAR BA AURE YAYI BA.


NAMIJI BAYA IYA YANKE HUKUNCI KO TABBATAR DA BAYA DA LAFIYAR GABA MATUKAR BA AURE YAYI BA.

Yana Daga Cikin Hukumomi na Ubangiji Tsara Ayyukan Sassan Jikin Dan Adam Daidai da Lokaci.

A bangaren Mazakutar Da Namiji, Sha'awa na zuwa ne tare da aikace aikacen Kwakwalwa ne dan Haka alokacin da Sha'awa ke motsawa idan aikin Zuciya da Kwakwalwa suka Samu Canji zai Shafi bangaren Mazakutar Da Namiji.

Fargaba, Tsoro, Razana da Rashin Kwanciyar Hankali Wadannan Ababen nada alaka da aikin Kwakwalwa da kuma Zuciya alokaci daya, Sannan ababen su iya Canja Yanayin Mazakutar Da Namiji daidai lokacin Sha'awar sa. 

Kallace Kallacen Bidiyon Turawa, Karanta Littafai ba lallai su fassara Wanda bai taba Aure ba a matsayin mai Matsala ko Rashin Nagartar Mazakuta. 

Anfani da Mata ko Zinace Zinace ga Wanda ya jarabtu da Hakan ba zai iya tabbatar da Lallai yana da Matsalar Mazakuta ko Raunin Mazakuta ba. 

Tsawon Gaba, Kauri da Girman Al'aura ba lallai Mutum ya tabbatar ko Baya iya Gamsar da Mace ba Musamman idan ba Aure yai ba Akaran farko. Wadannan Yanayin basa tabbatar da Wani bazai iya Haihuwa ko yima mace Ciki ba. 

Dan Haka Zan iya tabbatar da Bata lokaci ne da Asarar Kudade ga masu Magunguna ko asibiti Akaran farko ga Duk Da Namijin da baiyi Aure ba wajen Neman Magani da Sunan kankantar gaba, Rashin Tsawo ko Saurin Kwanciyar ta bayan Sha'awa ta Motsa. 

Ajira, A Bari Ayi Aure Sannan a tabbatar da lallai Akwai matsala ta Mazakuta akaran farko. 

DANWURI

Post a Comment

0 Comments