Idan Matarka Tana Waɗannan Ɗabi'un Baka Gamsar Da Itane A Lokutan Jima'i Ne:


Idan Matarka Tana Waɗannan Ɗabi'un Baka Gamsar Da Itane A Lokutan Jima'i Ne:

Da kwai dubannin mata a cikin gidajen aurensu da mazajensu basa iya gamsar dasu kuma sun kasa fitowa fili su faɗawa mazan nasu. 
Wasu daga cikin irin waɗannan mata hakuri kawai suke yi, wasu kuwa sunayiwa mazan hannunka mai sanda da wasu ɗabi'un da idan mijin mai ganewa sai ya gane.
Ga wasu halaye ko ɗabi'un da muddin kaga matarka tana makasu, ka tabbatar da cewa baka iya gamsar da ita ne.
 
1: Idan ka shirya
Idan kaji matarka tana faɗamaka ka tabbatar ka shirya kamin muyi, to ka tabbatar baka gamsar da ita ne.
Anan ta nuna maka ne kada baka shirya ba kuma kace sai kunyi.
Manufar shiri shine koda jiƙo ko shan maganin ƙarin kuzari ne to kayi. 
Don haka magidanta sai a kula da wannan kalmar dake ɗauke da sako cikin sauƙi.

2: Rashin yin kukan daɗi da
 sumbatu.
Da zaran kaji matarka ta zama kurma idan kuna saduwa to ka sani fa babu abunda take ji daga abunda kake mata.
Kukan daɗi da sumbatu suna aika saƙon da zaka iya tabbatarwa matarka tana jin daɗin jima'i da kai.

3: Saurin kwanciyar bacci
Mace idan bata marmarin mijinta bata damu data ga dawowarsa gida ba. Duk lokacin da zaka dawo gida zaka samu tuni tayi baccin da zata fake da kauracewa yin jima'i da kai saboda rashin gamsar da ita.
Mace idan tana samun yadda take so a jima'ince wajen mijinta tun a magariban farko take sheƙa kwalliyar jiran mjinta. Kuma duk jimawar da miji zai yi zai sameta idanuwanta tangaran tana jiransa.

4: Kwakwayon abunda kake yi ko yadda kake yi idan kana saduwa da ita.
Cikin raha da wasa zata riƙa kwaikwayon yadda kake yi idan kuna jima'i. Zata yawaita yi maka irin wannan wasan domin aika maka sakon da zaka gane ka gyara.
Sai dai ana samun wasu matan da ba wai suna maka ba'a da wannan saboda kazawa bane, sai dai bambamcinsu da masu nuna gazawa shine su basa yawaita furta wannan abun. Amma ita wacce ba a gamsar da ita ta rika mitan abun ne amma kuma cikin tsokana domin ka gyara.

5: Rashin nemanka da kanta:
Macen da mijinta baya gamsar da ita a kullum sai dai shi ya buƙaceta ba dai ita ta buƙace shi ba.
Idan za a shekera miji bai nuna yana so ba haka zasu yi ta zama saboda ko sunyi shike gamsuwa ba ita ba.
Amma idan miji yana gamsar da matarsa idan ya bada dama to fa kullum kuma ako yaushe sai anyi.

6: Dain zumuɗin kwanciya da kai:
Kana ganin matarka da kuka saba kwanciya a ɗaki guda a kuma gado ɗaya ta soma kwana a ɗakin yara ko a duguwar kujera, alamace na matarka bata gamsuwa da kai.
Idan mace na jindaɗin mijinta kullum burinta ta yi bacci a jikin mijinta.

7: Bacci da zaran kun kammala saduwa:
Mata ba kamar maza bane. Ita mace idan ta ciyu kwayoyin halittanta suna karamata kuzarine. Hakan yasa duk lokacin da ma'aurata suka yi jima'i mace ke saurin tashi ta bar namji amma fa idan ta gurzu.
Idan kuma jiƙa jiƙa akamata, kasala hakan ke sata tare kuma da baƙin cikin wannan abun cikin sauki sai bacci ya kwasheta.
Sai dai kuma wasu matan akasin hakan suke,idan sun ciyu basa ma iya tashi. Amma dai a likitance mace idan ta samu ci mai kyau a lokacin take ƙara samun kuzari

8: Yawan cewa batada lafiya da zaran yamma tayi
Idan matarka bata jin daɗinka kuma tasan zaka demeta yamma nayi zata fara kukan rashin lafiya domin kaucewa yin jima'i da kai.
Amma idan mace na jin daɗin mijinta, ko batada lafiya bata soma mijin ya sani saboda kada ya tausaya mata.

9: Baka Shawaran Ka samu magani.
Da yake mata sunsan ciwon basir yana ragewa maza kuzari, idan matarka ta raina ƙokarinka zata soma baka shawaran ka nemi maganin basir. Wasu matan ma dakansu suke zuwa su nemo jiƙo su kawowa mijin da suka fahimci yanada ragwanci.

10: Yi da wuri
Idan kaji matarka tana yawan cemaka yi da wuri ka tashi, alamune da baka iya kataɓus a kanta.
Mace idan tana jindaɗin mijinta ko bayan sun samu gamsuwa su take ka kasance a jikinta na wasu lokutan kamin ka tashi.

Da fatan maza masu iyali zasu yi la'akari da wannan kurman sakon da matansu suke aikamusu na rashin gamsar dasu cikin hikima.

Post a Comment

0 Comments