YANDA ZAKI KARE KANKI DAGA CIWON SANYI (INFECTION):


YANDA ZAKI KARE KANKI DAGA CIWON SANYI (INFECTION):


Ciwon sanyi mata wata babbar matsala ce dake addabar mata. Akasarin mata na fama da wannan cutar, daga kauye zuwa birni, matan aure da en mata. Kafin nayi wannan rubutun sai dana tattauna da mata dayawa akan wace cuta ce tafi damun mata a yanzu? Amsar dana samu kuma ita ce 'ciwon sanyi'. Shin menene ciwon sanyi? Meke kawo wannan cutar? Menene maganinta? Taya zan kare kaina daga kamuwa da ita? Domin samun amsoshin wannan tambayoyin ku cigaba da karatu...

Menene ciwon sanyin mata?

Ciwon sanyi, ko ace toilet infection ko vaginal infection dukka na nuni akan abu dayane. Ciwon sanyi wasu kwayoyin cuta ne dake addabar farjin mace. Wannan kwayoyin cutar na hana mace sukuni ta hanyar janyo kaikayin gaba, warin gaba, fesowar kuraje, fitowar ruwa fari ko yellow ko kore, jin zafi yayin jima'i, jin zafi yayin fitsari da sauransu.

Ire iren ciwon sanyi.

Ciwon sanyin dake damun mata bincike ya nuna kala kala ne. Amma zamu takaita akan guda 3 wanda sune sukafi cutar da mata.

1. Wanda bacteriya take janyowa (Bacterial vaginosis)

Wannan yana daya daga cikin manya manyan dake janyo wannan cutar. Acikin mata 100 dasukeda ciwon sanyi, kashi 50 suna dauke da bacterial vsginosis. Wannan na faruwa ne saboda yanayin canji na bacteriya din dake jikin mace. Asali akwai bacteriya masu bada kariya a farjin mace wanda ake kira da "normal flora". Idan wannan bacteriya suka habaka suka yadu sukan zama kwayoyin cuta kaman 'Gardnerella vaginalis' sai su haifar da ciwon sanyi.

Yaya ake kamuwa da wannan cutar?

Hanyoyin da ake kamuwa da wannan ciwon sanyi na bacterial vaginosis sune kamar haka,
1. Yanayin tsaftace farji
2. Amfani da abubuwan tsara iyali kaman su implanon, intrauterine device (IUD).
3. Ciki
4. Mu'amala da maza dayawa.

Alamomin Bacterial vaginosis
1. Jin zafi lokacin fitsari
2. Fitan farin ruwa mai karnin kifi musamman lokacin jima'i.
3. Fitan ruwa marar kauri sosai kaman kunu.
4. Kaikayin gaba.

Maganin Bactelrial Vaginosis
1. Metronidazole (Flagyl)
Idan kinada ciki daya haura wata 3 kada kiyi amfani da wannan maganin.
2. Clindamycin (cleacin)


2. Wanda fungi ke janyowa (Yeast Infection ko Candidiasis)

Wannan kalan ciwon sanyin na faruwa ne sakamakon girman kwayoyin cutar 'fungus' wato Candida albicans a cikin farjin mace. Asali farjin mace na dauke da wannan kwayoyin halittar amma basa cutarwa har sai sun kara yawa. Suna kara yawa ne idan suka samu damshi, ko waje marar iska.

 Wannan kwayoyin cutar ba farji kadai suke tsayawa ba suna iya yaduwa a cikin jikin mutum. Mata da yawa suna kamuwa da wannan cutar a wani lokaci a rayuwarsu. A cikin kashi 100 kashi 75 sun kamu da shi. Cuta ce mai hatsarin gaske idan ba'a maganceta da wuri ba musamman ga masu ciki, ciwon suga ko kuma masu dauke da cuta mai karya garkuwan jiki wato HIV.

Amma ciwon sanyi na Yeast, ba ciwon da namiji sai iya dauka bane bayan jima'i duk da cewa bincike ya nuna a cikin kashi 15 cikin 100 na maza na samun kaikayin gaba ko fesowar kuraje bayan saduwa da macen dake dauke da wannan cutar.

Alamomin yeast infection
1. Kaikayin gaba
2. Radadi a farji
3. Fitan farin ruwa mai kauri, ko mai yanayi kamar awara.
4. Jin zafi yayin jima'i
5. Labben farji suyi jawur ko su kwaile
6. Fesowar kuraje.

Maganin yeast infection

Akwai magungunan da zaki sha domin magance wannan cutar...
1. Fluconazole (Diflucan) ko
2. Itraconazole (Sporanox)
Likita zai miki bayanin akan yanda zaki sha magungunan.

Sannan idan cutar bata fara karfi ba akwai wasu magungunan da xakiyi amfani dasu. Wannan sakawa a keyi a cikin farji, akwai vaginal tablets ko creams na kwana 7 zuwa 14 d ya danganta da yanda likita yace kiyi amfani dashi. Koda kin fara amfani dashi sai kikaji sauki bayan kwana 2 ko 3 kada ki dena amfani da shi ki cigaba har sai kin gama dose din sabado idan cutar bata mutu ba zata iya dawowa. Daga ciki akwai;
-Nustatin (Mycostatin)
-Miconazole
-Clotrimazole ( wannan yafi karfi a cikinsu).

Yanada keu idan kina magance ciwon sanyi tuh idan da hali ki canza wandunanki, idan babu hali ki wanke su dukka da ruwan dumi ki shanya a rana..

3. Wanda aka kamuwa ta hanyar jima'i.
Wannan kalan ciwon sanyin ana kamuwa dashi ne ta hanyar jima'i wato. Mata zata iya shafawa mijinta idan tana mu'amala da wasu mazan. Haka shima zai iya shafawa matar sa idan yanada mata sama da daya ko kuma idan yana neman mata.

Namiji ba kasaifai yake ganewa yanada wanann cutar ba saboda alamominta basu cika bayanna a jikin namiji ba. Yawanci sai idan ciwon ya bayyana ajikin mace, wajen neman maganin sai ya gane shima yana dashi.

Amma idan anyi sa'a ya bayannana cikin namiji akwai alamomi kaman haka;
1. Jin zafi wajen fitsari
2. Jin zafi bayan fitan maniyyi
3. Fitan farin ruwa kadan
4. Kaikayin gaba

Alamomin mata
1. Kaikayin gaba
2. Jin zafi wajen fitsari
3. Warin gaba
4. Fitan ruwa mai launin yellow ko kore ko fari tass.
5. Kwailewar farji

Yadda zaki magance wannan cutar shine amfani da wannan magani me suna Metronidazole.

Mata da maza duka zasu iya amfani da wannan maganain matukar suna dauke da cutar, kuma zasu kauracewa saduwa har sai sun warke.

Wasu alamomin ciwon sanyi;

- Ciwon mara: Ciwon sanyi na janyo ciwon mara sosai koda ba lokacin ala'ada ba.
- Wasa da al'ada: Sai kiga ala'adarki na miki wasa, ko yanayin fitar jini ya karu .

Dabi'unmu na yau da kullum da zasu iya janyo wannan cutar na ciwon sanyi da rigakafinsu.

1. Yanayin tsaftace farji:

Wasu matan na amfani da abubuwa da dama wajen tsaftace farjinsu, a ganinsu hakan shine dai dai. Kaman amfani da ruwan gishiri, ruwan dettol, ruwan lemun tsami, medicated soaps da sauransu. Wanann ba tsaftaceki za suyi ba, hasalima kina kara bata halittar farjinki. Kaman yadda mukayi bayani a baya game da normal flora, yawan amfani da abubuwannan na kashe wannan hallitun na normal flora a cikin farjinki. Kuma asali shi farjin mace na tsaftace kansa da kansa a yanayin hallitarsa, saboda haka er uwa ki dinga amfani da ruwan dumi kawai wajen tsaftace kanki.

2. Yanayin wanke dubura bayan kinyi bayan gida:

Asalin yadda ya dace ki wanke bayan gida shine ki fara daga gaba zuwa baya, ma'ana daga farji zuwa dubura. Amma mata da yawa akasin haka sukeyi. Wannan dabi'ar sam bata dace ba. Idan kika fara daga baya kina debo kwayoyin cutar dake cikin bayan gidanki kina aikawa cikin farjinki. Hakan zai janyo miki da matsala babba. Shi farji baya san bakon abu a tattare dashi.

3. Amfani da bandaki mai datti:

Yawancin mata na daukan ciwon sanyi bayan amfani da bandakunan da mutane dayawa ke amfani wato public toilet. Shiyasa ake cewa ciwon sanyi toilet infection.

Bandakin tsugunno: Idan misali mace mai wannan cutar tayi fitsari a kasa, sai kema kikaje kika tsugunna, fitsarinki ya taba wajen kuma ya dan fallatso a jikinki tuh fah 'yar uwa zaki kamu da cutar. Saboda haka idan zaki tsugunna ki tsugunna waje mai keu inda ba'ayi fitsari ba, kuma kiyi hankali kada ya fallatsa a jikinki.

Bandakin zama (water system):

 kafin ki zauna kisaka tissue a cikin toitle sit din saboda farji a bude yake zai iya dauka kwayoyin cuta cikin sauki daga cikin toilet sit din. Kuma kada ki dade kina zaune akai.

4. Amfani da turare ko sabulu mai kamshi:

Dayawa mata na da wannan dabi'ar fesa abun kamshi ko wanke farji da sabulu mai kamshi. Wannan kusure ne babba, saboda su wannan kwayoyin cutar suna girma ne a inda yakeda damshi ko kamshi.

5. Amfani da jikakken wando:

Amfani da jikakken wando na haifar da cutar ciwon sanyi, saboda kaman yanda mukayi bayani a baya, kwayoyin cutar musaman na yeast na son waje mai damshi. Idan kin gama tsarki yanada mahimmanci daki tsantsane jikinki da tawul mai keu kafin ki maida wandonki.

Kuma ki kasance kina amfani da wando da akayi da auduga (pure cotton) saboda sunfi tsotse damshi akasarin wanda akayi na nylon.
Sannan kindinga shanya wandunanki a rana saboda kashe kwayoyin bacteria akan ki shanya su a inuwa cikin bandaki.

6. Shan magani ba bisa ka'ida ba:

Mutane nada wata dabi'ar sayan magani barkatai ba tareda sanin likita ba. Misali yawan shan antibiotics da kinga kurji a jikinki ko kina ciwon wuya da sauransu, na janyo infection. Bama vaginal infection kawai ba, hadda wasu cuttukan ma na daban. Saboda haka a kiyaye yawan shan antibiotics batare da sanin likita ba.

6. Tsarin iyali.

Idan mace na tsarin iyali domin samun tazarar haihuwa tuh akwai tabbas din da zata iya kamuwa da ciwon sanyi. Saboda yanayin chanji na kwayoyin hallitar ta (hormones) dinta na shafar farjin mace. Koda kina shan pills, ko kinada implant a hannu, ko an daure bakin mahaifarki da dai sauransu.

Dafatn kun karanta kuma kun fahimta. Idan kunada tambaya tuh zaku iya rubutawa a comment a kasa ko ku aiko mana da sako ta hanyar cike contact form a kasa. Allah ya kara mana lfya. Ameen.

SHARE

Post a Comment

0 Comments