Istimna’i: A Ba Ni Addu’ar Dainawa…



Istimna’i: A Ba Ni Addu’ar Dainawa…

Ga hanyar da za a bi don rabuwa da matsalar

Nabeela Ibrahim Khaleel

Tambaya: Assalamu alaikum. Don Allah abokina ne ya ce in tambaya masa wata addu’a da zai rika karantawa saboda kullum sai ya yi istimna’i idan ya je kwanciya. Yana so ya daina amma ya kasa dainawa.

Na ce ya yi aure ya ce min ba ya da halin yin auren. Na ce masa ya rika yin azumi ya ce aikin da yake samun na abinci a tsaye ake aikin babu damar yin azumin. Idan kuma ya yi zai sha bakar wahala ko ya tabka babbar asara. Saboda haka ya sa nake tambayar Duniyar Ma’aurata ko akwai shawara ko addu’ar da za ki ba shi?


Amsa Da farko dai duk wata addu’a da ta tabbata daga Manzon Allah (SAW) a kan neman sauki da samun mafita daga matsalolin yau da kullum ana iya karantawa don samun mafita daga wannan matsala.

Haka yin addu’a a kan matsalar a lokutan amsar addu’a, lokacin saukar ruwan sama, lokacin sujuda, da kuma lokacin bude baki na azumin farilla ko nafila.


Musamman yanzu da aka shiga kwanaki masu albarka na goman watan Zul-Haijj ga yau Ranar Arafa, sai ka yi kokari kada ka mance da sa wannan addu’a a cikin addu’o’inka.

Maganar cewa yana son ya daina amma ya kasa dainawa, mu sani cewa Allah ba Ya dora wa wata rai abin da ba ta iyawa tunda ko har Allah Ya yi umarni: “Kuma wadannan da ba su sami aure ba su kame kansu har Allah Ya wadatar da su daga, falalarsa.” (Suratun Nur, Aya 33).

To lallai kowane dan Adam yana da cikakken karfin halin kame kansa sai dai in raunin zuciya ya hana shi aiwatar da hakan.


Sannan maganar aure kuwa, tunda har yana da sana’ar da yake ci da kansa da ita, to ai kuwa yana da halin yin aure.

Sannan aure hanya ce ta buduwar arziki, domin Allah Madaukakin Sarki Ya fada a cikin Suratun Nur: “Kuma ku aurar da gwagware daga gare ku da salihai daga bayinku da kuyanginku. Idan sun kasance matalauta Allah zai wadatar da su daga falalarSa. Kuma Allah Mawadaci ne, Masani.”

Matsalar matasan wannan zamani shi ne son dora wa kansu abin da ya fi karfinsu, sun dage suna bin zugar Shaidan na lallai sai sun auri mace mai kyau, mai wayewa, wacce ta iya gayu da rangwada, maimakon su nemi mai hankali da tarbiyya kuma mai saukin aure su raya Sunnah su yi maganin matsalarsu.

Su wadancan ’yan matan da kuke kwadayi kudi suke so kuma ko kun kashe masu kudin ba lallai su aure ku ba.

Yarinya ko talla take yi in ka bincika ka ji tana da hankali kuma iyayenta mutanen kirki ne shi ke nan sai ka je ka yi aurenka a saukake ka mance da kyalkyal-banza.

Ka sani cewa aure mai sauki shi ne mai albarka kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya sanar mana.

Maganar cewa ba zai iya yin azumi ba saboda aikinsa na tsayuwa, ka sani cewa, Manzon Allah (SAW) ya yi umarni da yin azumi don dakushe kaifin sha’awa ga matasa, yana sane da cewa wadansu aikinsu na wahala ne wadansu aikinsu na sauki, don haka wannan ba hujja ba ce ta kin yin aiki da umarnin Manzon Allah (SAW).

Wannan hudubar Shaidan ce kawai don ya yaudare shi ya ci gaba da aikata sabon da yake aikatawa.

Dama dole ya ji wahala a farkon yin azumin, amma da ya saba zai zame masa jiki ba zai ji wata wahala ba kuma.

Azumi ana iya yin sa da kowane irin aiki kuma duk wanda ya karfafa niyyarsa ya nemi taimakon Allah, Allah zai taimake shi Ya ba shi damar yin azumin a kowane irin hali yake.

Lallai wannan aboki ya sani yin azumi ya fi masa sauki a kan dabi’ar da ya rika lokacin kwanciya.

Shawarata a nan ita ce ko dai ya yi azama, ya nemi taimakon Allah Ya yi aure ko kuma ya kama azumi ka’in-dana’in.

Sai mako na gaba in sha Allah, da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe Amin

Post a Comment

0 Comments