Illar Rashin Iya gamsar da mace A Jima'ice:

Illar Rashin Iya gamsar da mace A Jima'ice:

Tsangayar Malam Tonga 

Gamsuwar Jima'i ga mace, ya bambamta da yadda namiji yake samun Gamsuwar sa.
Gamsuwa a Jima'ice shine kololuwar jin dadi na Jima'i. Wanda yake zama jigo na kwantar da sha'awar mutum.

Mata suna iya samun gamsuwa a kasa da mintuna biyar, hakan nan mace cikin mintuna 10 tana iya yin zuwan kai fiye da daya.

Sai dai ita mace ba kamar namiji bace. Kamin mace ta soma samun gamsuwa a Jima'i sai ta Jima tana yi, wasu matan ma sai bayan sun samu haihuwar farko. Duk kuwa da ana samun wasu matan da basa yi ko basu taba yin zuwan kai ba kwanta kwata a rayuwar su.

Rashin gamsar da macen da take zuwan kai a Jima'i ba karamin illa yake yiwa mata ba. Duk macen data saba zuwan kai a Jima'i ya kasance bata samun yi idan mijinta ya sadu da ita tana iya shigar matsalar da zai iya shafar kwakwalunta.

Baya ga cutar kwakwaluwa da mace take iya samu saboda rashin samun gamsuwa. Macen da bata samun yin zuwan kai a yayin Jima'i tana rasa walwala, annashuwa da farin ciki a rayuwar ta. A kullum cikin bacin rai da tsanar kanta take.

Cikin sauki mace na iya fadawa harkar madugo saboda rashin samun gamsuwa ga mijinta. Ganin yadda tsarin na madugo yake, babu yadda za a yi mace ta shiga madudo ta kasa samun gamsuwa.
#Tsangayarmalamtonga 

Kaman yadda bincike ya tabbatar, kashi 70 na mata ba suna samun zuwan kai bane ta dalilin shige da ficen azzakari cikin farjin su bane, hanya mafi sauki da mace ke iya samun gamsuwa na Jima'i shine gugan dantsakanta. Sha, ko Tsotson gaban mace tare da yi mata sakace sune mahimman hanyoyin dake gamsar da mace, wanda sune mata masu neman mata suke yiwa matan da suke nema yanayin da idan mace ta saba yana da wuya namiji ya iya gamsar da ita.

Wani illar da rashin iya gamsar da mace yake jawowa shine mace na iya neman maza da aurenta.

Duk macen data gwada yin zina da wani namiji aka yi dacen ya gamsar da ita, wannan matar ta rika bibiyan shi kenan domin samun gamsuwa. Hakan kuma zai bude mata kofa na yi da sauran maza baya ga wannan.

Macen da bata iya samun gamsuwa daga mijinta idan ya sadu da ita, tana iya fuskantar illar amfani da gaban roba, gurji wato cucumber 🥒 ko duk wani abunda tasan zata cusa a gabanta ya kwantar mata da sha'awa. Haka kuma duk macen data saba cushe cushe abu a gabanta tana cin kanta, yana da wuya namiji ya iya gamsar da ita.

Babban illar da mace zata iya fuskanta saboda rashin samun gamsuwa daga mijinta shine rashin girmama shi. Gamsar da mace a Jima'i yana dauke da Kaso mafi tsoka dake sa mace ta kamu da son mijinta, ta hanyar kaunarsa da kuma tausaya masa. Idan mace ta rasa hakan gani take tamkar ba namiji take aure ba hakan kuma na jawo raini da rashin girmamawa na tsakanin miji da mata.

#TsangayarMalam 
Idan mace bata samun gamsuwa na Jima'i bata sha'awar yin Jima'i da mijinta, a duk lokacin da mijinta ya bukaceta zata rika bijiro masa da wasu uzurin da bazata bashi hadin kai ba. Hakan kuma na iya jawo rashin haihuwa da wuri koma taki yin ciki da mijin saboda tunanin tana iya rabuwa dashi.

Mata da dama suna neman rabuwa da mazan da suka aura saboda rashin iya gamsar dasu.

Mace zata gwammace ta kashe aurenta maimakon ci gaba da zama da mijin da baya iya gamsar da ita.

Macen data fita daga gidan auren da rashin gamsuwa ne ya fito da ita, tana iya zama mazinaciya bayan Mutuwar aurenta a kokarin ta na dandana duk wani namij daya zo nemanta da aure. Zata gwammace yin zina ta tabbatar da ingancin wanda zata aura a Jima'ice maimakon tayi auren ta fito a dalilin rashin samun gamsuwa.
Hakan kuwa na jawo illar yawaitan zinace zinace a tsakanin zaurawa da masu neman su da aure a cikin al'uma. 

Wadannan suna daga jerin manyan illolin da rashin gamsar da mace ke iya jawowa.

Yana da kyau ma'aurata musamman maza su yi kokarin fahimtar hanyoyin da zasu iya gamsar da matan da suke aure maimakon jefasu cikin wadannan illolin da muka lissafosu.

Da fatan ma'aurata zasu amfana da wannan nazarin domin amfani dashi wajen inganta zamantakewar auratayyarsu.

#citawanacitaka

Post a Comment

0 Comments