Matar Barin baku wani sirri akan miji......


Matar Barin baku wani sirri akan miji...... 

Musulunci ya koya mana bin umurni da yima miji biyayya matuqar bai tsallake umurnin Allah da Manzon Sa ba. 

Zaman lafiyarki dashi shine sani da kiyaye wannan maganar. 

Abun lura shine saunawa kika kai qarars mijin ki kika samu yadda kike so ko da kuwa kece da gaskiya ? 

Sau nawa kiqa tubure kika tirje akan abu kikayi nasara akai ? 

Sau nawa kikayi fushi, fada yaji ko zuciya bai yi tasiri ba ?

Sau nawa kikaga aka tilasta shi yayi abunda baiyi niyya ? 

So ki gane, qara, fada, tirjiya, naci, tilastawa, tsaurin ido, taurin kai baya sa namijin da ya isan makansa yayi abun. 

Sirrin shi ne yi masa biyayya da rufe duk wata kofa da zai ga alamun reni ko rashin girmamawa a tattare dake. 

Kiyaye kalaman ki, lallabi da sanin siyasar zaman aure sai yasa ya miki kusan duk abunda ba wadda ya isa yasa ko ya hanashiyi face ke. 

In bakisan yadda zaki biye masa ku zauna lafiya ba zaiyi matuqar wuya ya ja ki ja kuma ke kiyi nasara, in kuwa kikayi nasara a duga 1 kitabbata zakiyi loosing a guda 10 kafun ki sake samun nasara a duga 1. 

Matuqar kina son zaman lafiya dashi kawai bishi a hankali ki zama yar siyasa, qanki qasa tunda ke keda buqatoci daga wajen wadda walwalarsa yana da alaqa da walwalar zuciya da zaman gidan. 

✍️ Fatimah Chikaire


Post a Comment

0 Comments