Abubuwa ( 12 ) da mace ke siffanta dasu in tana son ka so na haqiqa.


Abubuwa ( 12 ) da mace ke siffanta dasu in tana son ka so na haqiqa.  

1. Tausayi :- In mace na son ka zata na matuqar tausayama da dagama qafa a dukkan al'amuranka musamman abunda ya shafi dawainiyar kudi. 

2. Rufama asiri :- zata kasance mai boye duk wani aibinka ga mutane, da yin wasu dawainiya dan kar a ga gazawarka, da qoqarin nunama mutane qoqarinka boye wasu laifukan kamar shaye-shaye, neman mata, kallon fina-finan banza, chatting din batsa ko exchanging na nudes data gani, ko kana dukanta ko baka sauke wani hakkin ta, rauninka a shimfida, etc. Yakanyi wuya in mace na sonka ta bude wadannan sirrukan in ba abu ya ci tura ba. 

3. Kare martabanka :- duk wani abunda zai sa wani ya renaka ko ya jawoma qaskanci a idon mutane zata kiyaye kuma ta karema shi a idon kowa wani lokaci har tayi fada da 'yan uwanta akan ka. 

5. Burgeka :- duk abunda zatayi ko ta koyo dan ta burgeka zatayi, kama daga kwalliya, rangwada, gyaran gida dana jiki, girke-girke, etc.

6. Son kyautatama da 'yan uwan ka :- zata so yima abubuwa da zai kyautata mu'amalar ta da kai, takan kasance mai son ma 'yan uwanka da kai kyauta. 

7. Samar ma farin ciki :- farin cikinka shine farin cikin ta, zata kasance duk wani abunda zatayi dan taga farin ciki a fuskarka zatayi ko da kuwa wani lokacin zata takura, amma babban burinta shine tagan ka cikin farin ciki wadda wannan ya fiyemata komi. 

8. Hakuri :- zata kasance mai hakuri, kawaici, yafiya da yawan ma uzuri akan kuskuren da kake mata, bata barin matsalar dake tsakanin ku ya bunqasa har ya zama sa6ani

9. Girmama :- tasan girma da darajarka, duk yadda kake tasan kaine jagoranta takan matukar kiyaye duk wani abunda zai sa kaga kamar ta renaka. 

10. Duban kyawawan dabi'un ka :- kullum a cikin maka uzuri take wadda hakan ya bata daman duba zuwaga kyawawan dabi'unda da kawaici akan wadanda basu da kyau, domin son da takema yakan hanata ganin laifin ka ko munin wasu dabi'un ka.

11. Yin biyayya :- takan yi iya qoqarinta wajen kiyaye abunda tasan kake so ayi, da kiyayewa da guje abunda ba ka so domin bata son abunda zai bata ma rai.

12. Son 'yan uwanka :- zata kasance mai son 'yan uwanka da gyara mu'amalar dake tsakanin ka da su, zata dauke su tamkar 'yan uwanta domin tasan su wani sashine na abunda take so. 

✍️ Fatimah Chikaire

Post a Comment

0 Comments