MUHIMMANCIN AURE A ADDININ MUSULUNCI DA RAWAR DA IYAYE ZA SU TAKA AKAN TARBIYYAR YARAN SU:


MUHIMMANCIN AURE A ADDININ MUSULUNCI DA RAWAR DA IYAYE ZA SU TAKA AKAN TARBIYYAR YARAN SU

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

Aure abu ne mai matuƙar muhimmanci a addinin Musulunci. Manzon Allah S.A.W ya faɗa cewa "A lokacin da ɗan adam ya yi aure, ya cika rabin addininsa". Sannan kuma Manzon Allah S.A.W ya ƙara da cewa: "Aure Sunnah ta ne, duk wanda ba ya tare da Sunnah ta ba ya tare da ni". Manyan dalilan da su ke sa wa a yi aure sun haɗa da:

-Domin ba wa maza da mata damar rayuwa tare cikin farin ciki da ƙaunar juna bisa dokokin addinin Musulunci.

-Domin a samar da ƴaƴa da gina al'umma tagari.

-Domin samar da haɗakar da shari'a ta amince da kuma kare mutunci da rayuwar al'umma daga kowane irin ƙasƙanci.

Daɗi da ƙari aure abu ne a tsakanin maza da mata domin ƙaunar juna da zamantakewa mai ɗorewa da samar da kykkyawan yanayin da za su tarbiyantar da ƴaƴansu su taso su na masu taƙawa da tsoron Allah. A wannan zamani da mu ke ciki mutuwar aure ta zama ruwan dare. Wannan dalili ya sanya ya zama lallai mu gujewa wannan mummunar ɗabi'a ta yawan mutuwar aure, mu zamar da gidajen aurenmu su zamto tamkar Aljannar Duniya. Babbar hanyar da za mu bi wajen kaucewa ruɗun wannan duniya shi ne mu sanya tsoron Allah a cikin zukatanmu.

A matsayin goyon bayan aure, iyaye su na da muhimmiyar rawar takawa wajena taimako da ba da jagoranci da nusarwa ga ma'aurata. Akwai buƙatar su yi amfani da ƙwarewarsu da hikimarsu su nusar da su duk abin da ya dace game da wannan lokaci mai wahala na rayuwar aure. Su kuma ba su dukkan wani haɗin kai da goyon baya da gudunmawar da su ke buƙata ba tare da yin katsalandan kan abin da bai kamata ba.

Farkon aure abu ne mai matuƙar muhimmanci. Akwai buƙatar mu yi duk mai yi yuwa domin samun yardar Allah. Iyaye su tabbatar da Taƙawa a matsayin mahaɗi mai matuƙar muhimmanci game da auren ƴaƴansu. A wannan zamani wasu daga cikin iyaye idonsu ya rufe sun ruɗu da ruɗunin duniya, abin duniya su ke kallo wajen aurar da ƴaƴansu a madadin su maida hankali wajen yi wa ƴaƴa zaɓin abokan aure nagari. Da dama daga cikin iyaye su kan duba matsayin mutum a muƙami ko tarin abin duniya ko wata alfarmar duniya kafin ba da aure wanda hakan ne kuma ya ke haifar da mummunan zaɓi.

Akwai wani labari mai daɗi da ya faru zamanin Khalifancin Hazarat Umar R.A a lokacin da ya ke gudanar da zagayen sirri domin duba halin da talakawansa su ke ciki sai ya ji wata tattaunawa a tsakanin wata uwa da ƴarta. Uwar ta na faɗawa ƴarta cewa ba ta samun riba mai yawa idan ta saida madara ko nono a saboda haka za ta ƙarawa nonon ruwa domin ya na yin yawa tayadda za ta na samun riba mai tsoka. Nan take sai ƴar tata ta ce da ita: "Ba za mu yi ha'inci ba". Duk da cewar a lokacin su ba musulmai ba ne.

Uwar ta yi ƙoƙarin gamsar da ƴarta akan su yi algus na haɗa ruwa da nono tunda babu Khalifa ko wani shugaba da ya ke ganinsu, amma ƴar ta ce sam ba za a yi ba, ya zama wajibi su bi koyarwar addinin musulunci domin in babu wanda ya ke ganinsu to Allah ya na ganinsu kuma ba za su kuɓuta daga girbar abin da su ka shuka ba.

Wannan kykkyawar ɗabi'a da wannan ƴa ta bayyanawa mahaifiyarta ta yi matuƙar burge Khalifa Umar R.A. inda sannu a hankali ya tura mutum ya sayo nono a gun wannan yarinya domin ya ga an yi algus da ruwa ko ba a yi ba, a lokacin da ya gano cewa lallai yarinyar nan ba ta bi umarnin haɗa nonon da ruwa ba sai ya bayyana cewa: "

"Wannan yarinya za ta zama uwa tagari mai girma. Nauyin Nagartarta ba ta tsaya a matsayin kuɗi ba ne, za ta kasance ne a matsayin auna mizanin nauyin ƙasa. Zan karrama ta da lambar yabo mai girma a matsayin kyautata, sannan kuma za ta kasance babban muradin ƙasa.

Khalifa Hazarat Umar ya sa an kawo masa yarinyar da mahaifiyarta fadarsa inda ya gabatar da ita ga ƴaƴansa ya buƙaci ɗaya daga cikinsu ya aure ta, "Wannan za ta kasance uwa tagari. Na sani babu wata amarya tagari sama da wannan mai kykkyawar ɗabi'a. Ba ta da matsayi a duniyance da za a lissafa, amma ta na da nagartar da za ta zama uwa tagari".

Asim ɗansa na uku wanda ba shi da aure shi ne ya auri yarinyar ta zama surukar Khalifan, daga jikokinsu aka samar da Hazrat Umar Bin Abdul'aziz wanda ya zama babban Khalifan Musulunci wanda ya jaddada nagarta da sauƙin kansa. Wannan lamari da ya faru ba zato ba tsammani ya nuna muhimmancin tarbiyyar yara da kykkyawar ɗabi'arsu irin ɗabi'un da ya kamata mu nema a ya yin neman matar aure. Manzon Allah S.A.W ya faɗa cewa "babu wani gata da uba zai ba wa ɗansa sama da ɗora shi kan kykkyawar ɗabi'a".

Post a Comment

0 Comments