SHIN KO MUNSAN MENENE CUTAR BASUR???:
A cikin duburar 'dan adam akwai jijiyoyin jini
wadanda wani lokacin suna samun matsatsi
da talala mai takurasu. A lokacinda suka
samu takurawa da yawa, sai su kumbura.
Kumburin wadannan jijiyoyin jini na kara matsi
da takura a garesu cikin dubura. Dalilin
wannan yanayi marar-dadi ga jijiyoyin, sai
kaga wani tsiro ya fito maka a bakin dubura
wanda jijiyar jinince. Zakaji ciwo, ko kai-kayi
koma zubar jini. Wannan lamari shine Malam
Bahaushe ke kira da BASIR-MAI-TSIRO
(Hemorrhoid/ Pile).
Wasu daga dalilanda ke haddasa shi sune
kamar haka:
1. Gaggawa wajen yin yun'kurin kasaye
abunda dake cikin mutum (kashi). Hakan na
takurama jijiyoyin dubura.
2. Yawan zawo(gudawa) ko 'kin fitowar kashi
maisa yawan tsugunni a ban-daki.
3. Yawan kiba, musamman wajen mara ko
duwawu.
4. Juna-biyu da nakuda (musamman wajen
yunkurin fito da jinjiri daga farji). Yana yima
dubura talala da matsi.
5. Jima'i ta dubura (haramun!). Masu jima'i da
iyalansu ta dubura da mafi yawan 'yan luwadi
na fama da basir mai tsiro.
6.Zama mai tsawo kamar na cikin mota ko na
tela, da sauransu.
7. Matsalolin zuciya kona anta na tsawon.
lokaci wanda ka iya jaza talalar jijiyoyin jini.
8. Da sauransu.
Zaka iya maganin rashin fitowar kashi maisa
yawan tsugunni ta hanyar cin 'ya'yan itace da
ganye (fibre foods). Yana da kyau sosai ga
marar-lafiya ya rinka tafasa ruwan zafi ya bari
yayi 'dumi ya gasa basir nashi da auduga ko
kuma ya zauna cikin robar ruwan mai dumi
minti 30 sau 2 a rana, domin samun saukin
ciwo da kumburi. Bayan angama gasawa toh
sai asamu DETTOL a wanke wajen domin
gudun kamuwa da wata bakuwar cuta.
MAGUNGUNA:
1 A hada garin Habba da garin tafarnuwa da garin rumman a hada da zuma a rika shan cokali biyu safe biyu rana biyu dare.
2 A hada man habbatus sauda da man tafarnuwa da man na'ana'a da man jirjir da man albasa da man zaitun da man albabunaj da man hulba a rika shan cokali daya safe daya rana daya dare a ruwan zafi karamin kofi daya tare da garin Habba karamin cokali da da zuma cokali uku.
3 zuma garin Habba da garin rumman da garin hulba da garin zogale cokali daya safe daya rana daya dare.
4 zuma da garin Habba da ma'ul khaal tuffah.
5 A yawaita shan ruwa da yawan mu'aamala da yayan itatuwa da ganyayyaki.
0 Comments