Amfanin Saiwar Zogale
1⃣ Sanyin kirji:
A tauna saiwar zogale tare da citta kwara daya.
2⃣ Tsutsar ciki:
A tafasa saiwar zogale da jar kanwa a sha.
3⃣ Ciwon sanyi ga mata da maza:
A tafasa saiwar zogale da kwara daya na tafarnuwa a sha sau biyu ga wuni tsawon kwana uku.
4⃣ Yawan ruwan maniyi ga namiji:
A gauraya cokali daya karami da sachet daya na madara.
5⃣ Tarin sanyi ko Mura: A gauraya garin saiwar zogale da zuma a sha cokali daya a kullum da safe tsawon sati daya.
6⃣ Rage nauyi ko qiba:
A tafasa saiwar zogale da lemun tsami daya a tace a sha bayan an karya sau daya a kullum
7⃣ Zafin fitsari :
A tafasa saiwar zogale da kanumfari a aha sau uku safe da rana da yamma.
8⃣ Ciwon sugar:
A rinka cin garin saiwar zogale a cikin abinci.
9⃣ Qazuwa:
A gauraya cokali daya na garin saiwar zogale da man zaitun a sha
10 Ciwon daji a cikin baki:
A tafasa saiwar zogale a marmasa gishiri a kurkure baki dashi a kullum sau uku, safe da rana da yamma
11 Ciwon yatsa na Dankankare :
A gauraya kwata na karamin cokali na garin saiwar zogale da na lalle a dorawa yatsan dake ciwo.
12 Matsanancin ciwon kai na zafi:
A yi hayakin saiwar zogale da garin habba.
13 Ni'ima ga mata:
A tafasa saiwar zogale a tace ruwan misalin kwara daya na karamin cup sai a zuba rabin gwangwanin madara a sha.
SHARE THIS
0 Comments