Abubuwa Masu Karawa Mace Ni'ima A Jiki:


Abubuwa Masu Karawa Mace Ni'ima A Jiki:



 Yawancin mata rashin kula da kai da rashin sanin irin abubuwan da yakamata su dinga ci domin samun dauwamammiyar ni’ima a jikinsu don samun gamsuwar kawunansu da jin dadin mazajen shi ke haifar mu su da matsalar daukewar ni’ima da kuma daukewar sha’awa.
Abubuwan da ya kamata mu mata mu dinga ci, domin karuwar ni’imar jikinmu da da jin dakin mazajenmu:-


A na son mace ta dinga cin daya ko biyu daga cikin wadannan abubuwan kullum a rana; a cikinsu akwai abubuwa masu saukin kudi wadanda duk rashin hadi ki ko rashin halin maigida, zai iya siya, kuma wadannan abubuwa su na kara lafiya da kuzari a jikkunan al’umma kuma garkuwa ne ga kamuwa da wasu cutukan. Haka kuma ya na karawa mata ni”ima da jin dadi wajen mazajensu.

Wadannan ba wasu abubuwa ba ne illa:

Kankana, Ayaba ,Gwanda, Goba, Lemo, Tumatir, Rake, Aya, Kwakwa, Dafafiyar gyada, Zuma, Nono, Madara, Madarar Shanu, Gurji, Dabino, Chukwi, Zogale, Ruman, Inibi, Tuffa, Zaitun.

Misali yau idan ki ka sami jikakkiyar ayarki ki ka ci, gobe ki sami raken ki ki sha, jibi ki sami nunannun tumatur dinki manya guda biyu ko uku ki shanye, gata ki sha kankana ko nono. Ki dinga cin abu kala biyu a cikinsu, to wallahi Ina tabbatar mi ki banda ni’ima, hatta fatar jikinki sai ta murje ta goge ta yi kyau.


Sannan wasu daga cikin su a na shan ruwansu domin ni’ima ta musamman ko a sarrafa wani abin da ruwan, don samun dauwamamman jin dadin ma’aurata, kamar:

Ga kadan daga cikin yadda a ke sarrafa wasu ruwan daga ciki:

1) Ruwan Kankana, Ayaba Manya Uku, Kankana Kwata da Tuffa: Ki hada ki markada ki zuba madarar ruwa gwangwani daya, zuma yadda ki ke so, ki sa kankara ya yi sanyi, ku sha kamar juice ke da maigida. Ya na karin ni’ima da kaurin maniyyi.


2) Ruwan Tumatir: Ki markada tumatir biyu, ki zuba ruwan a cikin kwai uku, ki sa magi da albasa ki soya ya yi ruwa-ruwa ki ci. Shi ma ya na saukar da ni’ima sosai da saka jin dadin auratayya, sannan hakan ya na saka gogewar fata.

3) Ruwan Kwakwa: Ki fasa kwakwarki ki tsiyaye ruwan cikin kwakwar, sannan ki bare bakin bayan kwakwar ki goga kwakwar da ‘greater’, sannan ki markada a ‘blander’, sai ki zuba ruwa a kan markadaddiyar kwakwar ki tace ruwan ki fidda dusar. Da ma kin bare dabinonki cikin gwangwanin madarar ruwa daya. Ki jika dabinon ya yi laushi sai ki markada ya yi laushi sosai, sai ki zuba a kan ruwan kwakwar, sannan ki zuba ruwan da ki ka fasa kwakwar ya zubo a ciki. Ki zuba zuma da garin madara cokali uku a ciki, ki juya sosai. Ki sa a firij ya yi sanyi ko ki saka kankara. Idan ba ki son sanyi sai ki sha a haka. Ki yini ki na sha; kar ki barshi ya kwana. Hmmm zumdum! Ba zan ce komai ba, sai kin gwada kawai, uwargida za ki ban labari.


4) Ruwan Zogale: Amfanin ruwan zokage ba zai lissafu ba a maganin cututtukan da ya ke yi ma na a jikinmu. Amma zan yi bayanin amfaninsa a bangaren karin ni’ima a jikkunanmu ne kawai.

6) Ruwan Rake: Ki bare rake ki yanka gutsu-gutsu ki daka a turmi ko ki markada a ‘blander’ ki na yi ki na kara ruwa a dusar raken ki na matsewa. Idan kin sami ruwan rake kamar cikin jog daya. Sai ki sami ruwan tafasashshen baure jog daya. Sai ruwan jangari da jangagai da alewar mata da a ka tafasa su guri guda a ka tace su ma jog daya. Sai ki zuba wannan ruwayen naki a wuta ki zuba zuma kofi daya, ki yi ta dafawa har sai ruwan ya kone ya zama kamar cikin jug daya, sai ki sauke. Amma za ki sa kaninfari da kayan kamshi a dahuwar. Idan ya huce sai ki juye a abu mai kyau. Ba zai lalalce ba. Kullum ki sha ludayi daya. Zai ratsa jikinki ki sami dauwamammiyar ni’ima. Mai gida zai dinga jin dadinki ya na gamsuwa da ke sosai. Tsimin rake kenan.

SHARE THIS 

Post a Comment

0 Comments