NITDA Blockchain Scholarship:


NITDA Blockchain Scholarship:
________________________________
Abu na farko da suka ce za ayi karatu akai a satin farko na Scholarship din shine Bitcoin Theory, menene Bitcoin Theory? a takaice ba tare da tsawaitawa ba ga kadan daga abinda ake nufi game da Bitcoin Theory, masana da kwararru sunce
  ~ Bitcoin Theory shine tsarin yadda Bitcoin yake tare da manufofin da kirkirar Bitcoin according to "Satoshi Nakamoto", wato a bisa tsarin yadda wanda ya kirkiro shi (Bitcoin) yayi shi, tare da idea, Technology dake tattare da Bitcoin.

  ~ Bitcoin Theory babu inda zaka fara samun foundation na Bitcoin sai ka San abinda Satoshi Nakamoto ya fada game da Bitcoin, ta Ina zamu San abinda Satoshi ya fada?
  ~ Sai ka koma zuwa ga "Bitcoin white paper" da Satoshi Nakamoto ya rubuta wacce take dauke da shafuka goma Sha 'daya, wato 11 pages.
  ~ A Crypto currency zaka ji ana yawan magana akan white paper, white paper itace takardar da zaka rubuta game da Coin ko Token ko Blockchain din daka kirkiro!!!
  
  ~ Bitcoin Theory zaka fara da menene Crypto currency, Menene Cryptography, wanene ya fara kirkiro Bitcoin? Satoshi Nakamoto, me yayi kafin Bitcoin yayi nasarar aka gagara dakatar dashi Kai tsaye?
  ~ Menene tarihin Mining din Bitcoin da farko, tun kafin ayi launching dinsa ya zamo wa duniya abun mamaki, Yaya Mining na Bitcoin yake kafin yau da kuma yau.
Wasu canje canje Bitcoin ko Satoshi ya kawo wa duniya da Bitcoin, sai kaje ka Karanta Bitcoin white paper.

  ~ A cikin white paper ne zaka bayyana wane Coin ka kirkiro? Yaya yake aiki? menene manufar data sa kayi Coin din, wane Technology ne bako a cikin wannan abinda kayi din, wace matsala kake so kayi solving daka kirkiro wannan din?
  ~ A cikin Bitcoin white paper zaka fahimci abubuwa guda uku daga farko:
  1. Na farko, "Peer To Peer Electronic Transaction" Wanda Satoshi ya kira Bitcoin dashi, wannan Peer To Peer din shine zaka ji an takaice shi da P2P, wato tsarin hada hadar kudade Kai tsaye ba tare da wani a Tsakiya ba.
 
  ~ Ba tare da wata hukuma ko gwamnati a Tsakiya ba, No central authority ko middle Man a tsakanin ni da kai, babu ruwan wani damu, idan zan tura maka kudi duk yawan su babu ruwan gwamnati da kai, babu ruwan gwamnati damu.

  ~ 2. Abu na biyu, Financial Freedom:

Zaka iya turawa ko a turo maka babu wani Banki a Tsakiya da zai tace ko ya tantance wannan kudin, su waye zasu tantance sune Computer, Computocin da suke duniya suke kan tsarin Blockchain Validation na wannan Coin din da muke hada hada ta cikin sa.
  ~ Wannan shine suke kira da Decentralization, wato a cire mutane daga cikin wadanda hada hadar kudaden a matsayin su zasu sa ido akan kudaden, a saka "Nodes" Computoci.

  ~ Financial Freedom ta yadda baka tunanin wani ya tuhume ka don anga Miliyan dari biyar, ko Billions a Account dinka, Blockchain Technology da Crypto yazo da fasahar da zaka ajiye kudaden ka duk yawan su babu ruwan wani da kai.
   ~ Hukuma tayi ta wasan kura da kai a Kotu just because of anga kudade a Account dinka, sannan kana da tsaron da ba za'a San hakika waye ya tura kudi kaza ko ya karbi kudi kaza ba, akwai sirri, sai dai in Kuma kayi amfani da CEX Exchange madadin DEX.

  3. Decentralization and Economy:

Decentralization din dai shine abinda muka bayyana a sama, toh amma ta yaya hakan zata kasance a cire Central authority a hada hadar kudaden duniya, sai aka samar da Computer akan tsarin da zasu kula da tacewa da tantance dukkan wata hada hada data biyo kan wannan tsari, tare da rarraba su wa sauran Computoci su ajiye bayanan idan sun inganta.
  ~ Shine maganar distributed ledger da kaji ana yi, toh duk wanda ya saka computer sa a wannan tsarin shi kuma za'a dinga biyan sa Ladan wannan aikin da take yi na tacewa da tantance transactions da aka yi, shine Mining ko Validation and creating the next block of Transaction.

  ~ Wadannan aiyuka da Computoci suke yi akan wannan tsarin shine Blockchain Technology, yana da wasu manyan features guda uku wadanda ake bukata:
  ~ 1. Decentralization, ya zama hada hadar da ake yi Kai tsaye ake yi, ba sai yaje hannun wani mutum yayi approving ba, Kai tsaye computers ne zasu duba idan ba transaction na Bogi bane (Fake) su amince ya wuce.
  ~ Scalability, sauri gaggawa, gudu, ana bukatan sauri wajen aiwatar da wannan aiki, ba wai ka tura kudi ya shafe minti uku bai sauka ba, kamar ka tura kudi daga GT zuwa First Mai Giwa.

  ~ Wannan tsohon yayi ne, bata lokaci ne, in seconds, cikin dakikai Blockchain ko Computer suke aiyuka Miliyoyi a kwaftawar Ido, so Blockchains suna daukan fasahar sauri sosai, shine Scalability.
  ~ 3. Security, dole Blockchains su zama suna da security, tunda ana hada hadar kudi toh lallai ana bukatan tsaro, Kuma ana so da gaggawa, gaggawar da ba za'a samu matsala ba, ana bukatan high level of security.
Wadannan sune ake kira 'yan uku a waje 'daya, wadanda biyu ke da iko wato "Blockchain Trilemma".

  ~ Toh sai dai masana sunce a yanzu an gagara samar da Blockchain din da zai dauki wadannan abubuwan guda uku gaba daya a lokaci daya, Blockchain din da za'a ce yana da:
  ~ Decentralization.
  ~ Scalability.
  ~ Security.
Toh sai dai ana ta samun kwararru suna cewa nan gaba za'a samu, kamar masu Core, wato Core Mining da ake yi akan waya, masu mallakar wannan abun sunce sunzo suyi solving wannan matsalar har ma da Karin abinda duniya bata taba gani ba "Trilemma" sunce a dakunce su, shine suke cewa "Satoshi Plus + Algorithm".

  ~ Blockchain a yanzu suna iya daukan biyu cikin ukun ne, su bar daya a dole, kodai Blockchain dinka ya dauki, Decentralization da Security ya bar scalability.
Ko ya dauki Scalability da Security, ko Decentralization da Scalability.
  ~ Basu iya hada duka ukun, Amma masu Core wato BTCs Mining, sunce sun kirkiro wannan fasahar, suna tafe da ita.
So, Bitcoin mining duk zaka fahimce bayan ka gane wadannan, harkar Crypto ba za'a taba raba ta da Mining ba, musamman a yanzu da ake ta hada Blockchain da Mobile App, shiyasa mu 'yan Pi muke jinjina wa babban Professor Dr. Nicolas Kokkalis da Changdiao Fan.

  ~ To amma dazu kaji nace Computer suna Mining Bitcoin, kada ka dauka a yanzu Computer dinka zalla zata iya maka aikin Bitcoin Validation din da zaka samu kudi ko Ladan aikin, No, a yanzu aikin yafi karfin Laptops da kananan Computer, ana amfani da manyan kayan aiki ne da suke zukan Wutar lantarki me karfin gaske me yawa, shins Mining kenan, Mining din Bitcoin, shi ake kira da "PoW" ko "Proof of Work".
  ~ Sai dai akwai fasahohin da a yanzu ake yi akan wasu Coins din da ba na Bitcoin ba, kamar "PoS" wato "Proof of Stake" irin na kan Ethereum da sauran su.

  ~ Da Kuma DPoS, wato "Delegated Proof of Stake", irin wannan ake yi akan RENEC na Remitano Exchange da sauran su da dama.
Wadannan suna daga cikin abubuwan da ake kira Bitcoin Theory, sannan wasu gyara da matsaloli suka biyo bayan zuwan Bitcoin, menene Bitcoin ya gagara magancewa?
  ~ Yaya za'a yi a magance? gyara za ayi wa Bitcoin ko kuma za'a koma kan sababbin Coins ne da ake kirkirowa a yanzu wadanda suke dauko da fasahohin da ake ganin zasu magance matsalar da Bitcoin bai magance ba, Pi Network ne ko Core, ko wasun su?

  ~ Wasu na daban, kamar yadda masana suke cewa Bitcoin has Three alternatives, sune Ethereum, LiteCoin da Ripple (XRP).
Wadannan kadan ne daga cikin abubuwan da zaka fara fahimta a Bitcoin Theory kafin aje gaba.
  ~ Nasarorn Bitcoin, kamar Decentralization, da Cutting up double spending da sauran su.
  ~ Matsalolin Bitcoin, kamar su Environmental warming da Mining din Bitcoin yake jawowa, low scalability, ko low transaction a lokacin da ake Kara yin yawa akan Network din Bitcoin.
  ~ Anonymity, rashin sanin wanene yake da kudi kaza, waye ya turo wa aka tura wa a wasu lokutan, duk da cewa a bayyana komai yake akan Blockchain, babu rufa rufa.

  ~ A rubutu na biyu zamu cigaba da magana akan menene Bitcoin Theory da JavaScript, Golang da wasun su a takaice me ake nufi dasu, yaya suke aikin, in sha Allah.
  ~ Daga nan zaka fara fahimtar harkar Crypto zallan karatu a cikin ta Malam, babu wasa, sai dai may be Kai kana jin labarin ta kamar wasa toh kana jin ta daga Wanda basu sunta bane.
Allah yasa mu dace.

Sauran bayanai zasu zo a Telegram din mu na "Block Group Technologists", in sha Allah.
✍️:
Abdul-Hadi Isah Ibrahim.
Lahadi, 10 Jumadal Ula, 1444.
Sunday, 04 December, 2022.

Post a Comment

0 Comments