Shin ko kasan cewa shan Fiya wato ‘Avocado’ na kara kyan fatar jiki? Ga kadan daga cikin amfaninsa
Fiya na da sinadaran da ake kira da turanci sugar- fructose, glucose, and galactose wanda suke kare mutum daga kamuwa da ga cutar cutar siga.
Shan Fiya na taimakawa mutum wajen samun cin abinci yadda ya kamata.
Fiya na kare mutum daga kamuwa da cutar siga da kuma cutar zuciya.
Fiya na kuma kara wa jariran dake cikin iyayensu lafiya.
Fiya na da wata sunadarin da ake kira ‘Potassium’ wanda ke taimakawa rage ciwon hawan jini a jikin mutum.
Fiya na kara kyan fatar mutum.
Fiya na kare idon dan adam daga cututtuka.
Fiya na da sinadarin vitamin A da B wanda ke kare mutum da ga kamuwa da cutar daji da kuma sa jikin mutum warkewa da sauri idan an kone.
Shan FIYA NA KARE MUTUM DAGA TSUFA DA WURI: Piya na da wata sunadarin da aka kira Xanthophyll wanda yake kare jikin dan adanm daga tsufa da wuri.
0 Comments