Amfanin Dabino Ga Lafiya: CIn Dabino Ga Mata Ma Su Juna Biyu Na Maganin Doguwar Nakuda:- Bincike




Amfanin Dabino Ga Lafiya: CIn Dabino Ga Mata Ma Su Juna Biyu Na Maganin Doguwar Nakuda:- Bincike




Wata kwararriyar likitar a fannin abinci mai gina jiki, Uwar-gida Jane Eleodi, ta shawarci mata masu juna biyu da yawan cin dabino, musamman ma a makwannin karshe-karshe kafin lokacin da za su haihu.

Ta ce, yawan cin dabino na samar wa matan sanadaran gina jiki, sannan kuma ya rage mu su doguwar nakuda.

Eleodi, wacce kwararriyar likita ce a fannin abinci mai gina jiki da ke aiki da wani kamfani mai suna 'JSPRINGS Nutrition and Health, Support LTD, da ke jihar Legas, ta ba da wannan shawara ne yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar wannan Alhamis.

Uwar-gida Jane ta ce, "An gudanar da zuzzurfan bincike kan dabino, kuma an gano ya na taimakawa mata ma su juna biyu wajen magance mu su doguwar nakuda.

"Cin dabino a makwannin ƙarshe kafin haihuwa na samarwa mata ma su ciki sanadaran inganta lafiya, sannan ya hana mu su dadewa a kan gwiwa.

"Cin dabino tun daga farkon ciki zuwa haihuwa na taimakawa mata ma su ciki wajen samarwa jikinsu sanadarai ma su gina jiki kamar, nau'ikan bitamin daban-daban, da kuma 'minerals' wadanda kuma ke taimakawa wajen girman dan tayi. Bugu da kari kuma su na da matukar muhimmanci ga lafiyar mahaifiyar.

Hakanan ta kara da cewa, "Ana samun muhimman sanadarai ma su dinbim yawa cikin dabino, da su ka hada da, Vitamin A, E, K, C, Thiamin, Riboflavin, Folates, Niacin, B6, Pantothenic acid, Zinc, Calcium, Iron, Choline, Magnesium, Phosphorus, Potassium, Manganese da dai sauransu.

"Sauran sanadiran gina jiki da ke kunshe cikin dabino sun haɗa da Omega3 fatty acid, Betaine da 'copper', '' in ji ta.

Eleodi ta kuma ce, 'ya'yan itaciyar sun ƙunshi sanadarin 'Tannins', waɗanda aka tabbatar su na taimakawa mata ma su juna biyu kwarai da gaske.

Ta ce, dabino ya kasance tushen samun sanadaran 'natural suger da kuma clories' waɗanda ke taimakawa mata ma su juna biyu su samu karfi lokacin nakuda.

Kwararriyar likitar ta ce, kodayake, binciken baya-bayan nan ya nuna cin dabino na taimakawa wajen saukin nakuda da kuma hana doguwar nakudar, amma akwai buƙatar karin bincike da nazari da za su marawa wannan sakamako baya, sannan da gano wadansu tasirin na dabino.

Ta ci gaba da cewa, wani bincike da aka gudanar kan wasu mata 69 da suka ci kwayar dabino 6 a kowace rana har tsawon makonni 4 kafin kwanakin da za su haihu, ya nuna cewa sun samu kashi 20 cikin 100 na saukin nakuda, da kuma fara nakudar ba tare da an taimaka mu su ba, sabanin 'yan uwansu da ba su ci dabinon ba.

Sannan nakudarsu, ta kasance gajeriya idan aka kwatanta ta da ta 'yan uwansu da ba su ci dabinon ba, a tsawon wadannan kwanaki.

Ta ce, a wani binciken daban, wanda aka gudanar kan wasu mata 154 masu ciki, sakamakon binciken ya nuna cewa ma su juna biyun da suka ci dabinon, za su iya haihuwa ba tare da an yi kokarin janyo mu su nakuda ba, idan aka kwatanta su da wadanda ba su ci dabinon ba.

"Wani bincike na uku da aka gudanar kan wasu mata ma su juna biyu, da ke cin dabino mai nauyin giram 70-76 a kullum tun daga sati na 37 da samun cikinsu, ya bayar da sakamako kwatankwacin bincike na biyu da ke sama" .

SHARE THIS Facebook    

Post a Comment

0 Comments