・ ◇・・NAMIJI DAN GOYO ・・ ◇・
☜⇢www.Sirrinrikemiji@gmail.com
➤・ D3C13938
JOIN US TELEGRAM GROUP:
Zamantakewar aure ga ma'aurata
https://t.me/sirrinrikemij
▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃
A duk inda ake zancen mace, gyara jiki shi ne abin da ake tinkaho da shi. A Yau na shhigo muku ne da wasu karin sirrukan da za su taimaka muku mata yan’uwana.
Bari mu fara da tuna wa juna cewa namiji a kowane hali, abin tattali ne. Don haka, ya kamata a kullum mu rika sanin cewa namiji fa dan goyo ne ga wadda ta iya. Ku girmama mazajenku ko kwa sami Aljannar Ubangijinku cikin sauki.
▽・・ Ni’ima Adon Mata・ ・▽
Dalilai da dama sun kasance manuniya ga zancen da muka faro a sama, wato tun da mun yarda cewa namiji dai abin tattali ne, to kuma yana da kyau mu fahimci irin tattalin da ya kamace shi.
Akwai hidindimun da mace za ta rika yi wa
mijinta domin a gudu tare, a tsira tare.
Addini ya hukunta cewar babu bambaci a tseren imani tsakanin namiji da mace. Ma’ana, don ya kasance mace tana karkashin namiji, bai zama kuma cewa a kullum a baya take ba. A’a, ana nufin ta kasance abokiyar tafiyarsa ne don ya samu saukin rayuwa.
Daya daga cikin ababen da za su amfani tafiyar namiji da mace shi ne tattalin kai, wanda mace ya kamata ta rika yi wa mijinta.
Wannan tattalin da ake magana a nan, ya shafi gyara jiki, nemankarin ni’ima domin saukaka ibadar aure da sauransu. A harkar gyaran jiki, babu macen da ta ba ta san amfanin: Lalle da kayayyakinsa ba.
Bari mu duba yadda ya kamata a yi amfani da wannan sinadarin:
Abubuwan da za a tanada sun hada da:
(1) Lalle.
(2) Kwaiduwar kwai (guda uku).
(3) Manja (Cokali uku).
(4) Cocumber.
(5) Kur-kur.
Idan kin sami wadannan kayan da muka lissafa,ki hada su waje daya, ki kwaba, sai dai Cocumber kadai za ki markada, ki tace ruwan, sannan ki zuba a kai.
Bayan nan, sai ki kwaba sai ya hadi sosai yadda ake bukata. Ki ba shi kamar minti goma ko ashirin, ya tsumu, sannan ki shafa a jikinki, ki ba shi awa guda sannan ki yi wanka da sabulun Ghana ko na Sabulun Salo.
Alal hakika, wannan yana aya daga cikin sinadaran da ke gaggauta gyaran jiki, gami da kara wa mace martaba, ni’ima da jin dadin rayuwarta a dakin miji.
▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃
✿・KAIKAYIN GABA (Emertic)・✿
⇢www.sirrinrikemijinki@yahoo.com
⇢www.Sirrinrikemiji@gmail.com
✆ whatsApp
◇⇢+2348037538596
ya gaggauta neman wadannan kayayyaki kamar haka:
#Tafarnuwa.
#Garin hulba.
#Man shanu.
Bayan kin same su, sai ki tafasa su, har sai ya tafasa daidai misali. Sai ki nemi katon bahon da za ki iya shiga ciki ki zauna, sannan ki zuba ruwan a ciki, ki rika shiga ciki da duminsa, sau uku a rana.
Da sannu za a samu waraka. Amma idan fa an yi wannan, kuma ba a samu waraka ba, ya zama tilas uwargida ta je ta ga likita,
watakila wani abin daban ba wannan ba.
△ ・ ZAFIN・ GABA ・△
Na biyu kuma, akwai wasu masu tambaya kan abin da ya shafi ZAFIN GABA. Shi ma wani nau’i ne na cutar da take yi wa jama’a illa, musamman mata.
Domin masana sun fitar cewa idan kina hawan zafin gaba, cutar zai iya dagula miki sha’anin al’adarki, ta kuma haifar maki da wani abin daban.
Don haka masu fama da wannan cutar sai su tanaji:
"#Ganyen kabewa.
"#Ganyen zogale.
" #Man kadanya.
"#Majigi.
" #Hulba.
Idan kin same su, sai ki hada su waje guda, ki kwaba da man kadanya, ki rika shafawa sau uku a rana.
Duk shafawa sai ta wanke da ruwan dumi.
Cikin kankanen lokaci, za ta sami waraka
da biyan bukata insha Allah.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
❖・NAMIJIN DARE ・❖
Haka kuma na samu wasu tambayoyi daga
kungiyar matan yi tambayar da ta shafi ‘NAMIJIN DARE.’ Abin da ake nufi da namijin dare shi ne, a wasu lokutan a kan sami Aljani da ke aurar ‘ya mace kuma ya
hana ta samun ciki.
Kuma muddin tana tare da shi, ba za ta taba haihuwa ba. Duk da ni ba masani ba ne kan harkar aljanu ba, amma bisa nazarin da na gudanar gami da tuntubar masana,sun tabbatar da cewa alamomin kamuwa da
■・ NAMIJIN DARE ・■
da mata kadai ke yi su ne kamar
haka:
Mafarkin jarirai.
Mafarkin wani na saduwa dake.
Bacin rai da faduwar gaba a koda yaushe.
Mafarkin ruwa.
Yawan ciwon kai.
Jin motsi a ciki.
Lalacewar maganar aure ga budurwa.
Damuwa da rama ko kiba marar misali, da
sauran makamanta hakan.
Don haka, idan uwargida ta samu kanta cikin irin
wannan halin, sai ta gaggauta neman tsarin
jikinta, kana ta yawaita addu’o’i.
▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃
❀・・HIPS ( KUGU ) ・・✿
◇ ◇
☌www.sirrinrikemijinki@yahoo.com
☌www.Sirrinrikemiji@gmail.com
✆ whatsApp
✎+2348037538596
Bari mu fara da masu neman karin ‘Hips. ’ Ina son a fahimci cewa girman kugu halitta ce, wasu matan har kauce hanya suke yi, su je a saka musu kugun roba.
Kun ga akwai alamar kauce hanya a nan ke nan.
Akwai nau’in ababen da mace za ta rika ci, sannu a hankali, kyan diri da halittarta za su kara fitowa, ita ma za ta rika ji ta kara cika, ta yi kyau.
Masana a wannan fannin, sun bayar da
shawarwarin amfani da
☜ Abarba,
☜ Ayaba,
☜ Gwanda,
☜ Kankana
☜ Zuma,
☜ Madarar ruwa.
A kan hada su waje guda, a markada su, har sai sun zama ruwa,sai a dan kara zuma da madara. Bayan wannan,mace za ta rika sha a koda yaushe. Haka kuma kina iya samun Zogale dafaffe, ki hada da ganyen Alayahu, ki zuba Tumatiri da Albasa, ki yi kwadonsu, ki rika ci.
Haka nan za ki rika yin wadannan kayan lambun da ki ka markada, sai ki rika sha misali da asuba ko da sassafe kafin ki
fara cin komai.
Insha Allah za a dace.
━━━━━━━━━━━━━━━━
☜(・⇢NI'IMAR JIKIN MACE ・⇢)☞
✎www.sirrinrikemijinki@yahoo.com
✎www.Sirrinrikemiji@gmail.com
✆ whatsApp
❀⇢+2348037538596
Dangane da bayani kan abubuwan ni’ima.
Kamar kullum mukan bayyana cewa a yawaita samun
✿⇢ ruwan Rake,
✿ ⇢ ruwan Kankana,
✿⇢ ruwan Kwakwa,
sai a matse su, a hade ruwan guda. Ki rika sha so uku-uku a rana.
Uwargida, kina iya yin wani hadi na musamman,wanda shi kansa maigida zai iya amfani da shi,hakan ma yana kara dankon soyayya da fahimtar juna.
Misali, ki samu
♜⇢ Alkama,
♜⇢ Danyar Gyada,
♜⇢ Waken Soya,
♜⇢ Aya,
♜⇢ Madarar ruwa,
sai ki jika ki markada su, ki tace, idan ya zama gasara sai ki rika damawa kamar yadda ake dama Koko, sai ki zuba madara ta ruwa, ki yi kamar sati biyu kuna sha.
Da yardar Allah za a dace
━━━━━━━━━━━━━━━━
▽・ TOILET INFECTION ( KAIKAYIN GABA ・▽
☜・www.sirrinrikemijinki@yahoo.com
☜・www.Sirrinrikemiji@gmail.com
✆ whatsApp
✎+238037538596
Haka kuma ga wadanda suke neman hanyar samun waraka daga kaikayin gaba, har ma a wasu lokutan suke
△ fitar da ruwa mai wari,
sai su tanadi,
❖⇢ Miski kwalla daya,
❖⇢ Zuma kamar cokali biyu,
❖⇢ Man zaitun cokali biyu,
sai su hada su guri daya, a samu ‘yar Auduga, a goga abubuwan nan da aka hada da zarar an idar da sallar Asuba,
sannan a nemi ruwan dumi, a kama ruwa da shi.
Sai ki dauki Audugar da ki ka goga wancan hadin a jiki, sai ki tura audugar ciki kadan, ki bar shi har tsawon awa hudu, ko fiye da haka, sai ki cire. Sannan ki kama tsarki da ruwan dumi.
Idan kuka yi ta maimatawa, har tsawon sati guda,insha Allah duk wata cuta da warin gaba za su kau. Allah ya sa mu dace.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
✿ ・ SIRRIN GYARAN JIKI ・✿
✆ whatsApp
⇢+2348037538596
Batun sirrin gyaran jiki, ya kamata mu sani cewa jikin mace na bukatar kulawa a kullum..
Ya ke ‘yar’uwa, kina iya samun Lalle, ki jika shi, bayan ya kwana, ki tace ruwan ki zuba Humra da Turare, sai ki yi wanka bayan kin yi wankan, kina iya tafasa Lallen, ki zuba a roba ki zauna a ciki kamar na mai jego, wato ‘Sit bath, ’ ki dan zauna a cikin shi na dan lokaci, wannan sirrinsa shi ne
fatar ki ba za ta taba lalacewa ba, kuma kariya ce ga saurin takurewar fata. Yana maganin cututukan gaban mace kuma yana kara tsuke mace. Bayan haka, yana maganin basir da kuma karin ni’ima ga mace.
Akwai wani nau’in sinadarin karin ni’ima wanda yake da saurin bayar da sakamakon da ake bukata, wato ‘Sharp-sharp, ’ kamar yadda masu hikima ke cewa.
Ki samu danyen Zogale ki hada da Cocumber, ki markada su, sai ki zuba madarar ruwa, ki adana sai ya yi sanyi. Sannan an fi so a rika sha da maraice.
Allah ya taimake mu.
Akwai kuma hadin sabulun tsarki da kan ki za ki hada, kun san yin tsarki da sabulun wanka yana kawo wa mace matsala, saboda irin sinadaran Chemicals din da ake hada sabulun yana da hatsari ne ga dan Adam, musamman mata, amma
wannan hadin sabulun za ki yi tsarki da shi cikin kwanciyar hankali, ba tare da wata damuwa ba,kuma bayan haka yana maganin cututuka na kaikaiyin gaba, da sauransu..
Da farko, zai ki nemi sabulun Zaitun, amma fa wanda aka rubuta Zaplan a jikin kwalin, kada a ba ki mara kyau.
Sai ki nemi Bagaruwa, ki daka ya yi lukwi, ki zuba a roba sai ki yanyanka sabulun zaitun din kanana a kan garin bagaruwan, ki dauko Miskin da kika hada tare ki Kwaba shi da ruwan Hulba, ki kwaba su sosai har sai ya yi kauri.
Sai ki zuba a roba mai kyau ki rufe, ko kuma ki samu turmin ki ‘yar karama,ki daka sabulun a ciki.
Sai rika wanka da abinki,kina tsarki da shi.
Kwararru a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa irin wannan Sabulun ba shi da wani hadari ko ‘Side effect’ ga mace, kuma zai kara tsuke mace, sannan ta rika kamshi da ni’ima ciki da waje.
▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃
⇢www.sirrinrikemijinki@yahoo.com
⇢www.Sirrinrikemiji@gmail.com
✆ whatsApp
❀・⇢+2348037538596
☜⇢D3C13938
▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃
0 Comments