RASHIN #SHA'AWAR MAZA DAGA MACE



RASHIN #SHA'AWAR MAZA DAGA MACE:


   akan samu a wasu lokuta mace ta kasance ba, ta sha'awar maza sam-sam, saboda rashin bin ka'idojin jima'i daga maza. Irin wadannan dalili sun hada da:

 miji ya rika kin kulawa da bukatun matarsa wurin jima'i da kuma rashin kulawa da jin dadin ita macen yayin jima'in .da daukarta a matsayin wani bangare mara amfani sosai a wurin ko cikin jima'i cigaba da irin wadannan halaye daga wurin namiji, yana sa mace ta rika guje wa yin jima'i baki daya, domin abin cutar da ita.

 a hankali a hankali, sai kaga yin jima'i ya zama wani abin zabtarwa ne gare ta, saboda bata jin dadinsa, koda kuwa ta yarda a tilas, don yardar da mijinta, a hankali wani lokacin zata bayyana kin da take yiwa jima'i wato ta rika guje masa.

   JIN ZAFIN JIMA'I DAGA MACE:

 a wasu lokuta zaka samu mace tana jin zafi a yayin jima'i ta yiwu mace tana jin zafi a yayin cewa zafin yana faruwa ne saboda rashin sha'awar, maza da macen keyi, ko kuma ya zama cewa wani ciwo ne da take dashi a gabobin jima'in ta yake kawo mata jin zafin. A irn wannan hali ya kamata a shawarci,likita saboda dorewa da jima'i tare da wannan jin zafi yana sa mace ta rinka gudun jima'i.

  RAWAR DA MIJI YAKE TAKAWA:

 ya kamata miji ya san yadda zai jawo hankalin matarsa akan jima'i ta yadda ba zai fuskanci wata jayayya ko nokewa daga wurin taba sam, sai dai ya samu sakankancewa da karbuwa, da kuma kwadayi dama matukar bukatuwa, har zuwa cikakkiyar saduwa, janyo hankali kan jima'i ana yin sane ta hanyar maganganun soyayya, da kuma nunawa matar daraja matan kamarta, da nuna mata cewa ita mai matukar kyau ce, wadda tafi kowacce mace wurin mijin nata, a daidai wannan lokaci sai mijin ya fara shafo sassan jikinta, kamar dai yadda muka bayyana a baya.

  Daga karshe muna yiwa miji nasiha kan cewa har ya rinka matsawa matarsa yin jima'i a lokacin da bata bukata, yafi kyau ya saurara har zuwa lokacin da take a shirye saboda girmama matantakarta musamman idan akayi la'akari, da cewa jima'in hadin guwa ne tsakanin su mata da miji kuma kowannen su yana da hakki akan dan uwansa.

 RAWAR DA MACE TAKE TAKAWA:

 babban aikin jiyar da miji dadi, da kuma kareshi daga yaudarar jan hankali matan banza ya rataya ne wuyan mata, kuma wannan kalubale ne mai hadari da muhimmanci a gareta
 kwararrar mace wato gogaggaya itace, wadda take iya sa wa mijinta ta ya manta da dukkan wata yaudara da jan hankali da yake gani daga wurin wasu mata titi
 mace ta gari itace, wadda tayi kokarin ta san dukkan bukatun mijinta, ta san irin girkin da ya fiso, da irin kayan da yafi so tasa, kai harma da irin launin dayafi so
 yana daga cikin manyan kur-kuran da mata ke tafkawa, rashin caba ado idan suna cikin gida. Sai su rika tarar mazan su da suka dawo daga wurin aiki. Da kaya masu warin hayaki, da gashi hargitsattse, saboda haka kar ayi mamakin ganin miji ya bar matarsa mai dan karen kyau, ya tafi wurin matar banza wadda ma bata kai matarsa kyau ba.

 Ko kuma aga mata wadda bata da wani cikakken kyau amma ta mallake zuciyar mijinta, da tunaninsa, da ma abin hannusa wannan duk daga matar ne
 ya kamata koda yaushe mace ta rika kulawa da jikinta, da yin ado a cikin gida
 kuma kar ta tari mijinta idan ya dawo daga wajen da kawo karar yara ko yan aiki ko kuma, ba kaza, ba kaza ta rika sama masa yana yi wato wurin mai kyau a gida dan ya hita ya shakata, ta kuma rage masa damuwar yara ta hanyar shagaitar dasu wani abu mai amfani, ta kuma fesa turare mai kanshi a jikinta, dama dukkan dakin ta mamaye shi da irin abincin dayafi so gaba daya dai tayi dukkan wani abu da zai taimaka wurin mantar dashi.
 gwagwarmayar daya sha a tsawon yini kuma ya kamata ta rika tsafatace gabobin jima'in ta. Ta rinka wanke farjin ta da magunguna da aka tana da don haka a dakunan saida magunguna domin duk wani wari da zai sa mijin ta ya rika gudun taya fita.

 BAYAN SADUWA; akwai wani mihimmin yanayi da ma'aurata keyi banza dashi saboda rashin sanin muhimmancin sa. Wannan yanayi ko kuma lokaci shine:LOKACIN BAYAN DADI: wannan lokacin shine bayan kawo maniyyi, da kuma gama jima'i bai kamata ma'aurata su juya wa junansu baya ba, bayan gama jima'i musamman ma dai shi miji.

Saboda wannan dan lokaci shine na auna zurfi da karfin soyayyar da ma'aurata suke wa jinansu sannan kuma yin haka musamman dai daga bangaren miji, zai sanya mata ta rika jin cewa ita ba komai bace, sai dai kayan jin dadin namiji. Wato duk amfanin ta bai wuce na abar shakatawa da ita a nan muhimmnacin yin'yan wasanni na kauna bayan gama jima'i yake bayyana ya zama daidai yake da muhimmancin wadannan yan wasannin da ake yi don tsokano sha'awa kafin jima'i.

  MATSALOLI: akwai wasu 'yan matsaloli wadanda suke faruwa a wurin jima'i wadannan matsaloli ba su wuce a shawo kansu ba. Amma saboda rashin sanin yadda za a bullo sai kaga sun kai ga cabewa har su rinka yin barazana ga aure .

DA FATAN ANGO DA AMARYA SUN FAHIMTA


Post a Comment

0 Comments