SHAWARA ZUWA GA ‘YAN UWA MATA KAN INFECTION!!!


SHAWARA ZUWA GA ‘YAN UWA MATA KAN INFECTION!!! ***************************

Ga wasu tambayoyi guda biyu, kowacce kuma tare da amsar ta!

(1) Shin toilet infection kadai yake haddasawa mata Kamar irin wadannan matsalolin ?

—Kaikayin gaba.
—Fitar Farin ruwa daga gaba.
—Kurajen gaba.
—Daukewar shaawa kwata kwata.
—Rashin samun ni’ima. Maana bushewar jiki. etc.

(2)Tambaya ta biyu mai yasa ada can baa cika samun ire iren wadannan matsalolin ba, Kamar irin yanzu?
Matan wancan lokacin, ba irin su bane ba a yanzu!

Amsar tambaya ta:

(1) Alal hakika Kamar yadda wasu maluman muslunci suka fadakar da dadewa shine hada tsarki bayan gida da alaura yana haddasa mutuwar gaba, ko kuma yakan jawo wasu matsalolin makamantan haka.

Haka abin yake don haka dole iyayan mu mata Sai Kun Kara gyara wa sosai, kuma kukara wayar ma yan uwanku mata kai akan haka.

Lallai yana daya daga cikin abinda yake jawo wa mata wadannan matsalolin hada tsarki bayan gida dana fitsari, maana alokacin yin tsarkin bayan gida ruwan da yake gangarowa zuwa alaura Shima yana daya daga cikin abinda abinda ke jawo irin wadannan matsalolin:


—Kaikayin gaba.
—Fitar Farin ruwa daga gaba.
—Kurajen gaba.
—Daukewar shaawa kwata kwata.
—Rashin samun niima. Maana bushewar jiki. etc

Don haka yake ‘yat uwa shawara gareki Matukar kina bukatar dorewar lafiyar ki, to Lallai ki kiyaye a lokacin tsarki ya zama baki bari ruwan tsarkin bayan gida yarika zubowa izuwa ala’urarki ba lokacin da kike tsarki. Allah yakiyaye Ameen.

Tambaya ta (2)Mai yasa mata ada can basucika samun ire iren wadannan matsalolin ba?

Abinda masana suka ce shine yana daga cikin amfanin da suke yi da wasu magunguna da muke kyama a yanzu muce suna kawo cuta, musamman Lallai yana daga ciki.

Domin yana taimakawa wajen magance faruwar ire iren wadannan matsalolin, musamman ma a yanzu zaka ga akwai wasu masu kokari wajen yin sabulun sa,to amfani dashi yana bada kariya koda ansami irin wancan matsalar na hada ruwan tsarkin bayan gida dana fitsari.

Allah taala yabada ikon gyarawa,Allah taala iyaye mana dukkan matsalolin dake damun mu baki daya Allahumma Ameen.


Post a Comment

0 Comments