Kamin Ki Auri Irin Wadannan Mazan Ki Tabbatar Da Zaki Iya Zaman Aure Dasu:


Kamin Ki Auri Irin Wadannan Mazan Ki Tabbatar Da Zaki Iya Zaman Aure Dasu:


#Tsangayarmalamtonga 
SHARE 🌹

Ba duk namijin dake kike burin aure bane zaki iya zama da Shiba.
Wannan kuwa ba saboda baya sonki ko baya kula dake bane, sai domin yanayin halin da yake ciki idan kina da rashin hakuri, zargi da kishi bazaki iya zama da wadannan mazan guda 4 ba.

 
1: Namiji Dan Siyasa: Duk macen da zata auri dan siyasa ta tabbatar da cewa zata iya mu'amala da mutane. Dole ta zama mai hakuri domin a gabanta za a rika durawa mijin nata ashar musamman 'yan bangan siyasa da kuma sharri na 'yan adawa.
Haka nan zaka zama mara zargi domin yadda wanda zata aura yake cudanya da maza da mata, mahaukata da masu hankali.
Dole mace ta jimrewa zata na wasu kwanaki ba tare da mijinta ba. Domin suna iya barin gari ko ma kasar domin gudanar da taruka na siyasa.
Haka nan akwai lokacinda tana kwance da mijin nata ma zai tashi ya barta saboda ana bukatarsa a wani taro na gaggawa.
Da wannan ne duk wata macen da zata auri 'yan siyasa ta kwana da sanin hakan yana iya faruwa ako wani lokaci.

2: Namiji Likita: Likita ko ma'aikacin jiya, maza ne da duk wata macen da take burin son aurensu ta tabbatar da cewa zata iya zaman auren dasu.
Kamin ki auri namiji Likita ko mai aikin jinya, ka sani aikinsa yasa zai rika mu'amala da mutane daban daban. Haka nan dole ne ya kadaice da duk wani mara lafiya dayazo wajensa namiji ko mace.
Namiji mai aikin jinya ko likita maza ne da basu da lokacin kansu. A kowani lokaci, a kowani hali ana iya nemansu da gaggawa a wajen aikin nasu domin duba mara lafiya.
Wadannan suna jerin manyan abunda duk wata mace mai son auren likita ko mai aikin jinya zata saka a faifai kamin ta amince aurensa.

3: Namiji Dan Kasuwa: Babban matsalar wadannan mazan da ya kamata mace ta sansu shine yawan tafiye tafiye.
Kasuwanci na bukatar zirga zigar na cikin gida har ma na kasashen waje. Dole ne ki zama macen da zata iya hakuri da rashin miji kusa na wasu lokutan.
Hakan nan kowa na iya kiransa mace ko namiji ta waya ko a tura musu sakonnin wahtsapp domin bukatar wasu abubuwan da suke harkar.
Idan mace ta zama mara uzuri da kishi, ta ba zata iya auren namiji Dan Kasuwa ba.


4: Namiji Fitattace-Suna irin wadannan mazan suna shahara ne a wani bangaren da suka yi suna akai.
Akwai celebraty mawaka, marubuta, masu shirin fim, ma'aikatan talabijin da radio, da 'yan kwallo ko masu sana'ar motsa jiki, dukkanin irin wadannan mutanen sukan yi ficen da mutane suke nuna musu so da kauna.
Musamman mata suna son yin mu'amala da mazan da suka shahara suka yi fice. Wasu ma hotunan jaruman nasu suke sakawa a dakunansu ko wayoyinsu amma ko ganinsu basu taba yi ba.

Irin wadannan mazan har runguma da sumbatarsu mata suke yi idan sun hadu dasu baya ga daukan hotuna dasu. Akwai ma matan da suke bada kirjinsu domin mai shaharan ya sa mata hannu akan nonuwanta.
 
Shin kin shirya auren Irin wannan namijin, zaki iya hakuri dashi. Zaki iya daina kishi ko kauda kai akan hakan? Idan amsarki e ne, to kina iya bashi dama ya fito daga yanzu.
 
Ba wai kawai mata ba. Akwai mazan ma da suke son auren Irin wadannan matan. Suma dai irin shirin da zasu yi kenan idan har dagaske suke son su auresu.

Post a Comment

0 Comments