Wasu Dalilai 5 Da Zasu Iya Jawo Ya Fasa Aurenki:



Wasu Dalilai 5 Da Zasu Iya Jawo Ya Fasa Aurenki:

#Tsangayarmalamtonga 
SHARE 🌹

Cikin dalilin da suke koran mazan da suka zo auren mata suna da yawa.
Kamar yadda muka soma kawo wasu a darusan mu na baya. Wannan karon ma ga wasu dalilai guda 5 da zasu iya hana namiji aurenki.
 
1: Yawan Magana Ko Rashin Magana: Kiyi nazarin namijin dake sonki da aure mai yawan son magana ne ko mara so.
Mazan da basu son yawan magana sukan ji tsoron mace mai yawan surutu. Haka nan maza masu yawan magana basu cika son macen da take da yawan surutu ba.
Idan kina da yawan magana a halittance, to ki rika nazarin wanda yake son aurenki, akwai lokacin da baya son yawan magana sai ki takaita masa surutun naki. Idan kin fahimci ranar da yake son hira nan ma sai ki sakar masa hira.

Haka nan ga namiji mai son surutu ke kuma baki yi, dole ki daidata kanki da hakittarsa duk da ba zaki iya zama irinsa ba mai yawan surutu.

2: Son Yin Jima'i Dashi: Mata sukanyi kuskuren tunani na neman su baiwa namiji kansu domin kada ya gudu a cewarsu.
Haka ne, akwai mazan da mace zata iya hanashi guduwa saboda Jima'i, amma mazan da suke guduwa bayan mace ta bada kanta sunfi yawa.
Mutanen sun riga sun cusawa kansu da tunaninsu cewa, muddin mace ta bada kanta ga wanda take so, tana iya baiwa wani dama. Wannan tunanin ke haifar da zargi cikin masoya har a babe.

Wani rashin adalci da mazan ke yiwa mata shine, wasu suke soma yin zina da wacce suke son su aura. Amma kuna sai su dawo suna mata kallon 'yar iska har sai sun rabu a sanadiyar hakan.

Wannan yake jawowa wasu matan suke shiga harkar karuwanci saboda abunda saurayinta na farko ya mata.

3: Yawan Baza Hotuna A Social Media- Maza na gudun matan da suka shahara a kafafen sada zumunta na zamani. Musamman matan dake baza hotunansu a kullum. Ko matan da duk abunda yake cikin zuciyarsu zasu yada shi a social media.
Maza na yiwa irin wadannan matan kallon masu tallata kansu ga maza ko marasa sirri. Don haka sai maza su kasa zuwa neman aurensu ko kuma su gudu idan suna nemansu da aure. 

4: Yin Abun Zargi: Akwai mazan da suke da tsarguwa. Muddin mace zata aikata wani abu na zargi nan take zasu tsaneta suce sun fasa auren.
Akwai matan da suke munafurci idan zasuyi waya ko suke amsa waya suna tare da samarinsu. Akwai matan da suke cusawa masu nemansu zargin Madugo ta hanyar nunawa masu sonsu na aure wata kawarta da ake ganinsu a manne kullum ta fisu daraja.

Akwai matan da yawon tsiyarsu tayi yawa. Wanda har sai masu nemansu da aure sun shiga zarginsu.

Duk ire iren wadannan abubuwan suna jawo zargi ga matan da mazan ke son aurensu. 

5: Wulakanci- Akwai matan da girman kai na sa su rika yiwa mai sonsu wulakanci.
Ba wai basa sonshi bane. Haka nan saboda nuna isa ne ko kokarin jan aji har sai namiji yaga cewa koda ya auri mace haka zata rika masa sai kawai ya kara gaba.
 
Yanada kyau mata masu irin wadannan halayen suyi kokarin gyarawa domin baiwa masu nemansu da aure su sak jiki dasu.
Zamu ci gaba da kawo wasu dalilan a darusa ba gaba.

Post a Comment

0 Comments